Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-05 17:15:11    
Kasar Sin tana shawo kan ciwon fuka cikin himma da kwazo

cri

Ciwon fuka wani ciwo ne mai yaduwa saboda kwayoyin ciwon fuka suna lalata huhun mutum, wanda ya taba yaduwa a kasar Sin, ya kawo wa lafiyar al'ummar kasar Sin illa sosai. Tun daga shakaru 1950 zuwa shekaru 1960, gwamnatin kasar Sin ta kara karfin shawo kan irin wannan ciwo, ta dauki matakai da yawa, saboda haka, halin da kasar Sin take ciki a fannin yaduwar wannan ciwo ya sassauto.

Amma a 'yan shekarun nan da suka gabata, saboda dalilai daban daban, ciwon fuka ya sake yaduwa a kasar Sin. Mataimakin ministan kiwon lafiya na kasar Sin Mr. Wang Longde ya bayyana cewa, 'yanzu kasarmu tana fama da yaduwar ciwon fuka sosai, sa'an nan kuma, kasarmu tana daya daga cikin kasashe 22 na duk duniya, wadanda suke fi daukan babban nauyi bisa wuyansu a sakamakon ciwon fuka, yawan 'yan kasarmu masu fama da wannan ciwo ya zama na 2 a duniya, kasar Indiya ta zama ta farko.'

Tun daga shekaru 1950, kasar Sin ta tanadi yin allurar rigakafi na BCG wato Bacillus Calmette-Guerin a Turance don shawo kan ciwon fuka a cikin tsarin yin rigakafi na kasar, a galibi dai, da zarar an haifi wani jariri, za a yi masa allurar rigakafi na BCG. Amma don me aka kara samun masu fama da wannan ciwo mai yawan haka a kasar Sin? Masana sun yi bayani kan wannan cewa, yin allurar rigakafi na BCG ya iya yin rigakafi da kuma rage yawan yaran da suke kamuwa da ciwon fuka kawai, bai iya kiyaye mutanen da suka riga suka balaga ba. Saboda haka, babban mataki na yin rigakafin ciwon fuka shi ne gano da warkar da masu fama da ciwon fuka na huhu mai yaduwa cikin himma da kwazo, ta yadda za a rage mafarin yaduwar ciwon.

A sakamakon haka, mataki na farko da aka dauka wajen shawo kan ciwon fuka shi ne kara gano masu fama da ciwon fuka. Tun daga watan Janairu na shekarar 2004, kasar Sin ta aiwatar da tsarin ba da rahoto kan masu fama da ciwace-ciwace masu yaduwa a duk fadin kasar, wadanda suka hada da ciwon fuka. A sa'i daya kuma, gwamnatin kasar ta ba likitoci na kauyuka da suka gano masu fama da ciwon fuka kudin yabo, don sa kaimi gare su wajen ba da rahoto kan wadanda ake tuhumarsu da kamuwa da ciwon fuka. Domin wannan mataki, likitoci na kauyuka sun kara ba da rahotanni kan masu fama da ciwon cikin himma da kwazo. Mr. Jin Hongjian, wani jami'in kiwon lafiya na birnin Xinmi na lardin Henan da ke tsakiyar kasar Sin, ya bayyana cewa, 'likitoci na kauyuka sun ba da rahoto kan masu fama da ciwon cikin himma da kwazo. Mun yi bincike a kauyuka a ko wace shekara, idan mun gano cewa, sun rage wadanda ke kamuwa da ciwon, to, za mu yanke musu hukunci.'

Bayan da ta dauki wadannan matakai, yawan masu fama da ciwon da kasar Sin ta gano ya kara karuwa cikin sauri. Sa'an nan kuma, wani muhimmin mataki daban da aka dauka wajen shawo kan ciwon fuka shi ne yin wa masu fama da ciwon fuka jinya. Kasar Sin ta kuma bi hanyar da Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya wato WHO ta gabatar da ita, wato masu sa ido su sa ido kan masu fama da ciwon fuka wajen shan magani. Madam Qiu Cuili, wata likita ta Beijing, haka kuma mai sa ido kan shawo kan ciwon fuka. Ta ce, 'na sa ido kan masu fama da ciwon fuka wajen shan magani a ofishin shawo kan ciwon fuka a kowace rana. Idan sun daina shan magani, ciwon fuka zai saba da magani, ta haka, magani ba zai yi amfani ba yadda ya kamata, ciwon zai kara tsananta, haka kuma sauran magungunan da suke sha ba za su yi aiki sosai ba.'

A galibi dai, saboda gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci kan shawo kan ciwon fuka sannu a hankali, halin da take ciki a wannan fanni ya samu kyautatuwa a bayyane. Har zuwa karshen shekarar 2005, kasar Sin ta warkar da masu fama da ciwon fuka da aka kara samu da yawansu ya kai kashi 91 cikin dari, sakamakon da ta samu ya sami amincewa daga kungiyar WHO.