Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-05 10:50:22    
An yi yawon shakatawa a kasar Afirka ta kudu

cri

Duk fadin kasar Afirka ta kudu ya zarce muraba'in kilomita 120, wanda ya yi kama da fadin Tibeti na kasar Sin, amma yawan mutane da take da shi miliyan 31 ne kawai. Wani shahararren wurin yawon shakatawa shi ne lambun shan iska mai suna Grut na kasar Afirka ta kudu. Fadin wannan lambun Grut ya kai rabin fadin lardin Hainan na kasar Sin. An kashe wannan lambu cikin yankuna da yawansu ya kai 12. A hakika dai, Grut wani lambun ajiye namun daji. Lambun Grut yana da namun daji da yawa, amma ana bukatar 'yan yawon shakatawa da su yi zagaya a lambun cikin mota, haka kuma bai kamata a bude kofar mota ba. Sabo da haka ne, idan kana yawon shakatawa a lambun Grut, sai ka mai da hankali sosai, idan ka bude kofar mota, to, mai yiyuwa ne akwai hadari daga namun daji.

Kudin da za ka biya a lambun Grut a kan abinci da wurin kwana ba shi da yawa. Sabo da haka, idan kana da lokaci, kana iya zagaya a can cikin kwanaki biyu ko uku. Idan ka yi yawon shakatawa daga wani yanki zuwa wani daban, to, za ka iya ganin dabbobi daban daban na musamman. Lokacin safe da dare sun zama lokaci mafi kyau da aka kallon namun daji, domin zakoki da damisa da giwaye su kan nemi abinci a wadannan lokaci.

Birnin Capetown da ke bakin teku wani wuri ne da kasar Afirka ta kudu ta fi raya shi, sabo da haka jama'ar wurin su kan kira shi birnin mahafiya. Daga wannan wuri ne, 'yan mulkin mallaka na kasar Holland sun fara kafa mulki kasar Afirka da kudu. Da farko dai, 'yan mulkin mallaka sun mai da birnin Capetown kamar wurin da aka dasa kayayyakin lambu, amma a halin yanzu, gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta riga ta gina shi kamar wani kyakkyawan lambun da aka dasa furanni.

Zirin Capetown yana da gabar teku mai kyau gani, abin mamaki gare shi shi ne akwai penguin a ko ina a kan gabar tekunsa. An riga an mayar da wannan wuri a matsayin wani yanki da aka kare namun daji, sabo da haka, penguin ba su tsoron mutane ko kadan. Idan ka yi yawon shakatawa a wurin, to, za ka iya ganin penguin da yawansu ya kai 10 ko 20 suna zagaya a kewayen ba su jin tsoro 'yan yawon shakatawa. Idan ka tabo kansu, to, sai su yi kamar wasu yara, kana son ka tafi da su a gida.

Zirin Capetown ya fi samar da manyan kifin teku, wato shark a Turance, sabo da haka fikafikan kifi na Capetown sun yi suna sosai a duk duniya. An ce, da farko ana jigilar fikafikan kifi na Capetown zuwa kasar Thailand, ana sayar da su a ko ina a Asiya, da yawa daga cikin ana sayar da su a babban yankin kasar Sin. Sabo da haka, idan ka yi yawon shakatawa a Capetown, kada ka manta da cin fikafikan kifi na Capetown. Ban da wannan kuma, akwai kanti da ke sayar da naman musamman na kasar Afirka ta kudu, wadanda da kyar a ci su a sauran wurare. To, domin haka, watakila ba za ka manta da kasar Afirka ta kudu ba har abada.(Danladi)