Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-02 19:40:05    
Wu Renbao wanda ke shugabantar aikin bunkasa sabon kauye a nan kasar Sin

cri

Gwamnatin kasar Sin tana kokarin sa kaimi ga yunkurin gina sabbin kauyuka da kyautata ayyukan yau da kullum a kauyuka har da kyautata aikin gona a kasar Sin domin sassautar bambancin da ke kasancewa a tsakanin birni da kauye da kuma karuwar kudin shiga ta manoma. Yanzu a wasu kauyukan kasar Sin, ya kasance da wasu mutane wadanda suke shugabantar manoma domin neman arziki. A cikin shirinmu na yau, za mu bayyana muku wani karamin jami'in na kauyen Hauxi da ke lardin Jiangsu. Wannan karamin jami'i shi ne Mr. Wu Renbao, shugaban kauyen Huaxi.

Tsoho Wu Renbao ya taba hawa kan mukamin sakataren sashen kauyen Huaxi na lardin Jiangsu na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Canja fuskar kauyen Huaxi da kawo wa jama'ar kauye arziki buri ne da yake yunkurin cimma a cikin dogon lokacin da ya gabata. A cikin shekaru 48 da suka wuce, lokacin da yake kan wannan mukami, kauyen Huaxi, wani kauye ne da ba wanda ya san shi kuma ya yi fama da talauci a da ya zama wani kauye mai arziki, kuma ya yi suna kwarai a nan kasar Sin domin kauyen yana da arziki sosai. Yanzu kudin shiga da wannan kauye ya samu a kowace shekara sun kai kudin Renminbi yuan biliyan 30. Dukkan manoman wannan kauye suna da manyan gidaje, wato house. Fadin gida mafi karami na manoma ya kai muraba'in mita dari 4. Bugu da kari kuma, kowane gida yana da mota daya ko biyu har guda 3. Manoman kauyen Huaxi sun gaya wa wakilinmu cewa, mutanen da ke da kudin Renminbi yuan fiye da miliyan 1 suna da yawa. Wasu gidaje suna da kudin Renminbi yuan fiye da miliyan 10. A gaban babban gidan da ke da benaye 3 da wurin iyo da dakin motoci, madam Wu Guiqing, uwargida a wannan gida ta yi farin ciki kuma ta gaya wa wakilinmu cewa, "Gidana yana da iyalai 4, wato ni da mijina da yara 2. Mun riga mun biya dukkan kudaden sayen wannan gida, kuma muna da wasu 'yan miliyoyin kudade a ajiye. Sannan kuma, gidana muna da motoci 3."

Lokacin da wakilinmu yake yin tadi da Mr. Wu Renbao, bai iya amince da cewa, yanzu Wu wani tsoho ne da ke da shekaru kusan 80 ba. Idonsa yana da haske, tunaninsa ya yi daidai kwarai. Har yanzu Mr. Wu yana cike da jikuwa ga tarihin samun bunkasuwar kauyen Huaxi, kuma yana cike da imani ga makomar kauyen. Lokacin da wakilinmu ya tambaye shi me ya sa manomar kauyen Huaxi sun iya samun arziki a karkashin shugabancinsa, Mr. Wu ya ce, "Dole ne jama'a sun fi jami'a jin dadin alheri da arziki, amma idan ya kasance da wahala, dole ne jami'ai su kasance kan gaba wajen fama da wannan wahala. Sakamakon haka, jama'a za su bi sawunka."

Mr. Wu Renbao bai mai da hankali kan ingancin zaman rayuwarsa sosai ba, amma ya mai da hankali kan aikinsa kwarai. Lokacin da yake kan mukamin shugabancin kauyen Huaxi har na tsawon shekaru 48, bai yi kuskure ko sau 1 ba kan muhimman kuduran da ya tsaida. Ya kan yin nazari da fahimtar manufofi iri iri daidai da gwamnatin kasar Sin ta tsara. Sabo da haka ya kan tsai da wasu kudurai daidai har a kan ji mamaki. Dalilin da ya sa ya kan tsai da kudurai daidai shi ne yana mai da hankali sosai kan labaru iri iri, musamman labarun siyasa a cikin dogon lokacin da ya gabata.

Kauyen Huaxi ya zama kauye mai arziki kwarai a kai a kai a cikin shekaru 48 da suka wuce a karkashin shugabancin Wu Renbao. Amma sauran kauyukan da ke kewayan kauyen Huaxi ba su da arziki. Bayan da ya yi nazari sosai, tun daga shekara ta 2001 zuwa shekara ta 2004, an shigar da sauran kauyuka 16 masu talauta cikin kauyen Huaxi. Sabo da haka, dukkan tsofaffin wadannan kauyuka 16 suna da damar samun kudin rayuwa a kowane wata daga hannun kauyen Huaxi, mutanen wadannan kauyuka ma sun samu guraban aikin yi a cikin masana'antun kauyen Huaxi. Ya zuwa yanzu, manoman wadannan kauyuka da suka kai kashi 95 cikin kashi dari sun riga sun gina da sayi sabbin gidajen da suke nema.

Ko da yake kauyen Huaxi da sauran kauyukan da ke kewayan kauyen Huaxi yanzu suna da arziki, amma Wu Renbao ya fara sa ido kan sauran kauyuka masu fama da talauci a duk fadin kasar Sin. Bisa shirin da ya tsara, nan da shekaru 5 masu zuwa, a kowace shekara, zai gayyaci jami'ai dubu 10 na kauyukan sauran wuraren kasar Sin da su je kauyen Huaxi domin yin musayar ra'ayoyin neman arziki, kuma zai iya yada fasahohin neman arziki da mutanen kauyen Huaxi suka samu a duk fadin kasar Sin. Mr. Wu ya ce, "A da mu kan fadi cewa, idan mutane masu arziki 10 sun taimaki mutum mai talauci daya tare, to, wannan mutum mai talauci shi ma zai zama mai arziki sannu a hankali. Amma idan an sa wani mutum mai arziki a cikin mutane masu talauci 10, shi ke nan, wannan mutum mai arziki ma zai zama mai talauci. Sabo da haka, ina ganin cewa, wani kauye kawai ya zama kauye mai arziki, wannan ba hakikanin arziki ba ne. Sai idan dukkan kauyukan kasar Sin sun zama kauyuka masu arziki be jawau za mu iya fadin cewa ai yanzu mun zama masu arziki."(Sanusi Chen)