Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-02 19:38:10    
Kasar Sin ta taimaka wa kasashen Larabawa wajen horar da jami'an kula da harkokin kiyaye muhalli

cri
Daga ran 15 ga wannan wata, za a yi kwanaki 15 ana horar da manyan jami'an kiyaye muhalli 15 da suka zo daga kasashe goma da suka hada da kasar Jordan da Yeman da Syria da Masar a kasar Sin don koyon ilmin kula da harkokin albarkatan ruwa da magance kazamtattun ruwa. Wani jami'in kasar Sin wajen kiyaye muhalli ya bayyana cewa, wannan ne kos na farko da kasar Sin ta shirya domin ba da taimako ga kasashen Larabara wajen horar da jami'ansu, makasudin nan shi ne don ba da taimako ga kasashen Larabawa wajen magance karancin ruwa da kazamtattun ruwa wadanda suke kara tsanantawa a kowace rana.

A gun bikin bude kos din nan a ran 2 ga wannan wata, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin kasa da kasa ta babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin Yue Rui ya bayyana cewa, bisa tsarin yin hadin guiwar kiyaye muhalli a tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa. Kos din zai aiwatar da shirin horar da kwararru a tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa. Kuma kos din da kasar Sin ta shirya a karo na farko zai ba da taimako ga kasashen Larabawa wajen kiyaye muhalli, Ya yi imani cewa, kos din zai iya bude sabon hali na yin hadin guiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa, kuma yana da ma'ana mai muhimmanci ga yin ma'amala da hadin guiwa a tsakaninsu wajen kiyaye muhalli.

Mr Yue Rui ya ci gaba da cewa, batun ruwa batu ne na duk duniya. Yadda za a yi rigakafi da shawo kan kazamtar da ruwa da cim ma buri na yin amfani da albarkatan ruwa cikin dorewa da nuna goyon baya ga tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki ya zama dawainiyar gaggawa da kasashe daban daban na duk duniya suke fuskanta. Kasashen larabawa su ma suna fuskantar matsalar ruwa.

Mun sami labari cewa, bisa halin da kasashen Larabawa suke ciki wajen kula da harkokin albarkatan ruwa, kasar Sin ta shirya darusa iri iri dangane da halin da kasar Sin take ciki wajen kula da harkokin magance kazamtattun ruwa da albarkatan ruwa da tsarin shari'a na kasar Sin wajen yin rigakafi da shawo kan kazamtar da ruwa da tsarin kimanta tasirin da aka yi wa muhalli da fasahohin gyara ruwa da dai sauransu. A karshen lokacin ba da horon, jami'an kiyaye muhalli na kasashen Larabawa za su yi rangadin aiki a wasu wuraren kasar Sin. Wani dalibi na kasar Lebanon Mark Saddeh ya bayyana cewa, na yi fata sosai ga kos din. Ina fatan zan iya fahimci fasahohin da kasar Sin ta samu wajen yin rigakafi da shawo kan kazamtar da ruwa ta hanyar horon nan, a sa'I daya kuma, ina fatan zan sami taimako da goyon baya daga wajen kasar Sin a fannin ilmin da kasar Sin ta samu wajen magance batun kazamtar da ruwa a kasar ta yadda za mu iya ci gaba da kiyaye muhallin da ke bakin kogin Litani da kuma hana kazamtar da aka yi wa noma da sauransu.

A cikin jawabin fatan alheri da mataimakin magatakarda na kawancen kasashen Larabawa Ahmed Ben Helli wanda ke halartar bikin budewar kos din ya yi, ya bayyana cewa, yin hadin guiwa wajen kiyaye muhalli shi ne babban batun da ake yi wajen yin hadin guiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa, ya kuma bayyana cewa, shirya kos din babban sakamako ne da aka samu wajen hadin guiwar muhalli da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa .Ya bayyana cewa, ina fatan jami'an da suke shiga kos din za su iya amfani da fashohin da suka koyo daga kasar Sin a cikin hakikanan ayyukan da za su yi a kasashensu da kuma su zama wadanda ke da karfin sa kaimi ga kiyaye muhalli.(Halima)