Kasar Zambia da ke kudancin Afirka tana da kasa da yawa kuma mai daraja sosai. Wasu kamfannoni da mutunen kasar Sin suna yin aikin gona a kasar, kuma sun ci nasarori da yawa. Akwai dama da yawa a fannin "yin aikin gona" a kasar Zambia.
A cikin kayayyakin sassaka masu yawa na kasar Zambia , katakan sassaka sun fi daraja . Saboda a cikin katakai , bakakke sun fi kyau . Sa'an nan kuma katakan Rose sun fi daraja . Idan ka ajiye su kan ruwa , sai su nutse cikin ruwan . Wadannan kayayyakin sassaka suna da haske sosai , shi ya sa a kan ce suna da halin musamman mai martaba.
Kayayyakin sassaka suna da iri daban daban . A cikinsu akwai giwa da zaki da rhinoceros da sauran dabobi . Ban da wadannan kuma , kayan mutum-mutumi na halin musamman na Afrika da wuka da kuyafa da kwano da sauransu sun sami maraba daga mutane masu yawon shakatawa . Turawa su kan bayyana cewa , sun fi son kai ziyara a kasar Zambia . Ina dalilin da ya sa a yi yawon shakatawa a kasar ? Shi ne ya zo daga sababin siniman na kasar Ingila . Wane ne ya dauki wadannan siniman kabila ? Shi ne Mr. Daniel wanda ya taba zaman yau da kullu ciki9n shekaru 20 , kuma ya hakakke cewa , wannan gaskiya ne .
A kasar Zambia , kai bako ne har abada . Ba sau daya sau biyu ba mutanen kasar Zambia sun gaya mini haka . Bakunci halin musamman ne na mutanen kasar Zambia . Wata rana wani bature ya yi yawo a kasuwa , wani musulmi na kasar Zambia ya cire kundi wanda yake sa al'kura'ani a ciki daga wuyansa , shi da kansa ya rataye a wuyana don nuna fatan alheri gare ni .
A tashar Motoci wani ya shawarce ni zuwa mahaifinsa don ziyara . A gidansa ka ci abinci da zama ba tare da biya kudi ba . Mahaifinsa yana kudancin kasar Zambia . A cikin motocin zirga-zirga wadanda suka ba ni 'ya'yan itatuwa ban sa adadinsu sosai ba . A tituna ko yaushe ko ina sun yi gaisuwa da ni , saboda wannan ya riga ya zama wani kashi na zaman yawon shakatawa .
Idan kana son sanin Zambiawa , to , muddin ka tsaya kan mararraba kuma ka bude wata taswira kamar ka yi batan kai , sai nan da nan wasu mutanen Zambia su zo wurinka kuma su tambaye ka cewa kana son na ba da hannu gare ka ? Idan ba shi da aiki , tabbas ne zai kai ka zuwa birnin da kake son ziyara. A mako na farko da na zo kasar Zambia , kowace rana wasu mutane su da kansu sun raka ni yawon shakatawa.
Mr. Dong Fafu wanda ya jagorar filin gona na amincewar kasashen biyu tun daga shekarar 1997 ya ce, yanzu akwai manyan 'yan kasuwa da yawa sun zo daga kasashen Turai, suna da jari da yawa. Idan 'yan kasuwa na kasar Sin ba su yi kokari, za su fadi a nan gaba.
|