Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-31 17:28:06    
Hukumar makamashin nukiliya ta duniya

cri

Masu sauraro, yanzu lokaci ya yi da za mu amsa tambayoyin masu sauraronmu. Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Salisu Rahman, mazauni jihar Taraba ta tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya aiko mana, ya ce, shin yaushe ne aka kafa hukumar makamashin nukiliya ta duniya, ita wace irin hukuma ce? Mene ne amfaninta a wajen hana habaka makaman nukiliya? Watakila ma sauran masu sauraronmu su ma suna da irin wannan tambayoyi, to, a cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani filla filla a kan hukumar makamashin nukiliya ta duniya.

Hukumar makamashin nukiliya ta duniya, wato IAEA a takaice, wadda ke da hedkwatarta a birnin Vienna na kasar Austria ta kafu ne a shekara ta 1957. Ita hukuma ce da ta kulla hulda da majalisar dinkin duniya, haka kuma hukuma ce da gwamnatocin kasashe daban daban ke aiwatar da hadin gwiwar kimiyya da fasaha a bangaren makamashin nukiliya. Babban daraktan hukumar a yanzu shi ne Malam Mohammed al-Baradei, wanda ya fara rike wannan mukami a ran 1 ga watan Disamba na shekara ta 1997, sa'an nan a watan Satumba na shekara ta 2005, a karo na uku ne ya sake ci zaben zama babban daraktan hukumar.

Buri ne mai sauki lokacin da aka kafa hukumar makamashin nukiliya ta duniya, wato 'don sa makamashin nukiliya ya kasance domin zaman lafiya'. Wannan kuma yana nufin cewa, kamata ya yi a yi amfani da fasahohin nukiliya a fuskokin makamashi da kiwon lafiya da aikin gona da kiyaye albarkatun ruwa da dai sauransu wadanda ke da burin lumana na bauta wa dan Adam. Sabo da haka, manufar hukumar ita ce kara saurin habaka taimakon da makamashin nukiliya ke bayarwa ga zaman lafiya da albarka na duk duniya, da kuma tabbatar da gudummowar da aka bayar ba za a yi amfani da ita a fannin soja ba.

Hukumar makamashin nukiliya ta duniya ta kuma tanadi cewa, ko wace kasa na iya zama mambar hukumar, idan kwamitin daraktocin hukumar ya gabatar da sunanta, sa'an nan an zartas da ita a gun babban taron hukumar, kuma kasar ta mika takardar amince da dokokin hukumar. Ya zuwa watan Faburairu na shekara ta 2006, yawan mambobin hukumar ya riga ya kai 139.

Sassan da hukumar ke da su sun hada da majalisa da kwamitin daraktoci da ofishin sakatare. Majalisar hukumar tana kunshe da duk wakilan kasashe mambobin hukumar, wadda ta kan kira taron hukumar a shekara shekara, sa'an nan ofishin sakatare kuma sashe ne na zartaswa, wanda ke karkashin jagorancin babban darekta, a karkashin ofishin nan kuma, akwai ofishin tsara manufofi da sashen ba da taimakon fasahohi da hadin gwiwa da sashen kula da makamashin nukiliya da tsaron nukiliya da dai sauransu. A matsayinsa na sashen da ke tsai da kudurori, kwamitin daraktoci yana kula da kasafin kudi na hukumar da kuma kasashe masu neman zama mambobin hukumar da kuma gabatar da su ga babban taro, bayan haka, kwamitin yana kuma daukar nauyin zartas da yarjejeniyoyin da abin ya shafa da nada babban darakta da dai sauransu.

Tun bayan kafuwarta, hukumar makamashin nukiliya ta duniya ta yi dimbin ayyuka tukuru a wajen sa ido a kan makamashin nukiliya da kuma tabbatar da mallakar makamashin nukiliya cikin lumana, ciki har da shiga tsara yarjejeniyar hana habaka makaman nukiliya da dai sauransu. sabo da babban taimakon da ta bayar a fuskar hana yin amfani da makamashin nukiliya a fannin soja da kuma tabbatar da mallakar nukiliya cikin lumana, shi ya sa hukumar nan tare da babban darektanta al-Baradei suka sami lambar yabo ta Nobel a kan zaman lafiya a shekara ta 2005.

A shekara ta 1984, gwamnatin kasar Sin ita ma ta mika takardar amince da dokokin hukumar ga hukumar makamashin nukiliya ta duniya, sabo da haka, ta zama wakiliyar hukumar a hukunce. A cikin shekaru gomai daga baya, kasar Sin ta sa hannu cikin ayyukan tsara wasu yarjejeniyoyin duniya na hukumar, haka kuma ta rattaba hannu a kan wasu jerin yarjejeniyoyi tare da ita.

To, masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau, da haka, ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, sai mako mai zuwa, ku huta lafiya.(Lubabatu Lei)