Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-31 08:46:48    
wasu labaru game da wasannin motsa jiki (25/05-31/05)

cri
A gun gasar guje-guje da tsalle-tsalle da aka yi ran 28 ga watan nan, agogon wurin, a birnin Eugene na kasar Amurka, shahararren dan wasa mai suna Liu Xiang na kasar Sin ya yi fintinkau wajen samun lambar zinariya a gun wasan tsallake shinge na gudun tsawon mita 110 na maza da dakika 13 da digo 21, wato ke nan ya kago matsayi mafi kyau a duniya a shekarar da muke ciki. Wannan ne karo na biyu a jere da dan wasa mai suna Liu Xiang ya zama zakara a gun wannan wasa. Dan wasa mai suna Ladji Doucoure daga kasar Faransa ya samu lambar azurfa ; kuma dan wasa mai suna Allen Johnson daga kasar Amurka ya samu lambar tagulla.

An yi karawar karshe ta gagarumar gasar tsakanin kasa da kasa ta wasan kwallon raga wato volleyball na mata na kasar Sin da aka yi ran 28 ga watan da muke ciki a unguwar Beilun ta birnin Ningbo dake bakin teku a gabashin kasar Sin, kungiyar kasar Sin wadda take ita ce zakara a gun taron wasannin motsa jiki na Olympics na Aden da kuma gasar cin kofin duniya ta wannan wasa ta lashe ta kasar Cuba da ci 3 da ba ko daya. Kuma wannan ne karo na farko da kungiyar wasan kwallon boli ta mata ta kasar Sin ta zama zakara a gun gasar tsakanin kasa da kasa da aka yi a wannan shekara. Kasashen Cuba, da Holland da kuma Rasha suna biye da ita.

A gun gasar cin kofin duniya ta wasan daga nauyi ta samari matasa da aka yi a ra 28 ga watan nan a birnin Hangzhou na kasar Sin, dan wasa mai suna Li Zheng ya zama lambawan har ya karya matsayin bajinta na duniya a gun wasan daga nauyi kai tsaye na maza wadanda ajin nauyinsu ya kai kilo 56.

Kwanakin baya ba da dadewa ba, kwamitin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing ya shelanta, cewa ba zai yi hadin gwiwa tsakaninsa da duk ko wane kamfani ba, wanda kerarrun kayayyakinsa yake kunshe da Alcohol da ganyen taba da kuma sauran makamantansu da su kan gurbata muhalli.

An sanar da sakamakon zaben wadanda suka samu lambobin yabo na wasannin motsa jiki na Laureus na shekarar 2006 da aka yi a birnin Barcelona na kasar Spain. Sannannen dan wasan kwallon tenis mai suna Roger Federer daga kasar Swiss ya samu lambar yabo na dan wasa namiji mafi kyau a karo na biyu a jere; Miss. Janica Kostelic, wadda take ita ce zakara a gun wasan skiing tsakanin duwatsu na taron wasannin motsa jiki na Oympics na yanayin sanyi ta zama ' yar wasa mafi kyau a wannan shekara.( Sani Wang )