Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-30 21:46:54    
Taron koli na kungiyar hadin kai ta birnin Shanghai da za a kira na da ma'ana mai muhimmanci, in ji Mr Hu Jintao

cri
Kafin kira taron koli na kungiyar hadin kai ta birnin sxhangchai a birnin Shanghai na kasar sin, shguaban kasar Sin Hu Jintao ya karbi ziyarar da manecma labaru na kasashen da cke cikin kungiyar suka yi masa cikin hadin guiwa a ran 30 ga wannan wata a birnin Beijing. Ya bayyana cew, taron nan na da ma'ana mai muhimmanci sosai, zai ba da taimako wajen sa kaimi ga shiyyar da ke tsakanin nahiyar Asiya da nahiyar Turai don ta zama wata shiyya mai jituwa da ke shimfida zaman lafiya mai dorewa da samun wadatuwa gaba daya.

Kungiyar hadin kai ta birnin Shanghai ita ce kungiyar kasa da kasa da ke tsakanin gwamnatoci kuma ta kasance cikin dogon lokaci wadda kasashen Sin da Rasha da Kazakhstan da Kirghiziastan da Tajikistan da Uzbekstan suka kafa a ran 15 ga watan Yuni na shekarar 2001 a birnin Shanghai na kasar Sin, a cikinsu, sun aiwatar da ka'idar amincewar juna da samun moriyar juna da yin zaman daidai wa daida da yin shawarwari a tsakaninsu da girmama wayin kai iri daban daban da neman samun bunkasuwa gaba dayansu, a waje da su, suna aiwatar da ka'idar rashin kulla kawance da kuma ba domin yin adawa da sauran kasashe da jihohi ba da bude kofarsu. Shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru biyar da kafa kungiyar , za a kira taron koli na shekarar da muke ciki a birnin Shanghai a ran 15 ga watan Yuni. Lokacin da Mr Hu Jintao ya karbi ziyarar da manema labaru na kasashen da ke cikin kungiyar suka yi masa cikin hadin guiwa, ya amsa tambayoyin da manema labaru suka yi masa cikin hadin guiwa a kan tarihi da makoma na kungiyar wajen samun bunkasuwa da kalubalen da shiyyar da ke tsakanin nahiyar Asiya da nahiyar Turai suke fuskanta wajen tsaron kai da matakan da kungiyar za ta dauka da batutuwan da taron nan zai yi tattaunawa da taimakon da kasar sin ta bayar ga raya kungiyar da huldar da ke tsakanin kasar Sin da sauran kasashen da ke cikin kungiyar. Ya bayyana cewa, wannan taron koli da za a kira na da ma'ana mai muhimmanci sosai. Ya ce, a duk tsawon lokacin taron, shugabannin kasashen daban daban za su yi shawarwari kan babban shirin raya kungiyar, da kuma yi musayar ra'ayoyinsu a kan batun samun moriyar juna wajen siyasa da tsaron kai da tattalin arziki da al'adun dan adam da sauransu, kuma za su rattaba hannunsu a kan manyan takardu da bayar da su. A gun taron nan, za a takaita fasahohin da aka samu a cikin shekaru 5 da kafa kungiyar, kuma zai bincike halin da kasashen duniya da kuma shiyyar nan suke ciki da yin nazari kan makomar kungiyar wajen samun bunkasuwa da tsara hakikanin fasali da matakai na yin hadin guiwa. Na yi imani sosai cewa, wannan zai ba da amfani wajen sa kaimi ga kafa wata shiyya mai jituwa da ke shimfida zaman lafiya mai dorewa da samun wadatuwa gaba daya.

Kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da zaman karko a shiyyar shi ne burin farko da aka yi wajen kafa kungiyar , kuma babbar dawainiya ce ta kungiyar a wannan lokaci. Lokacin da ya tabo magana kan kalubalen da shiyyar tsakanin nahiyar Asiya da Turai take fuskanta a halin yanzu, Mr Hu Jintao ya bayyana cewa, a ranar da aka kafa kungiyar, shugabannin kasashen da ke cikin kungiyar sun riga sun rattaba hannunsu a kan yarjejeniyar Shanghai na yaki da karfin da ke cikin rukunoni uku cikin hadin guiwa a tsakanin mambobin kungiyar, sa'anan kuma an kafa cibiyar yin adawa da ta'addanci ta shiyyar. Game da fuskantar kalubalen da aka kawo bisa sakamakon batun tsaron kai a cikin kasar Afghannistan da yaki da miyagun kwayoyi, Mr Hu ya bayyana cewa, fataucin miyagun kwayoyi a kasashen ketare da kuma yin laifufuka a jere bisa sakamakon nan batu ne mai muhimmanci da kungiyar take fuskanta sosai da sosai, mambobin kungiyar sun rattaba hannunsu a kan yarjejeniyar yaki da shan miyagun kwayoyi cikin hadin guiwa, kuma sun ba da taimako ga gwamnatin Afghannistan wajen yaki da shan miyagun kwayoyi.

Lokacin da ya tabo magana a kan amfanin da kasar Sin ta bayar a cikin kungiyar a shekaru 5 da suka wuce, Mr Hu Ya bayyana cewa, a cikin shekaru da yawa da suka wuce, kasar Sin ta bayar da amfaninta da ya kamata ta ba da tare da sauran mambobin kungiyar.(Halima)