Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-29 19:55:10    
Tauraron dan Adam na sa ido kan albarkatun kasa da kasashen Sin da Brazil suka samar da shi tare

cri

Yanzu ana yin amfani da tauraron dan Adam na sa ido kan albarkatun kasa da kasashen Sin da Brazil suka samar da shi a fannoni daban daban, wanda ya ba da hidima ga kasar Sin da kasashen da abin ya shafa a fannonin yin nazari da bincike kan albarkatun kasa da yin amfani da su da kuma kula da su. A cikin shirin na yau, za mu gabatar muku halin da ake ciki a wannan fanni.

An yi amfani da tauraron dan Adam na sa ido kan albarkatun kasa wajen yin bincike da nazari kan albarkatun kasa. Ya iya gano tsare-tsaren kasa da kuma dukiyoyin da ke boye a kasa, haka kuma, ya sa ido kan gandun daji da tekuna da kuma iska da dai sauransu, da kuma ba da gargadi kafin aukuwar bala'i daga indallahi iri daban daban. Tun daga shekaru 1990, kasar Sin ta gama kanta da kasar Brazil wajen yin nazari da samar da tauraron dan Adam. A sheakrar 1999, an harbi tauraron dan Adam mai lambar 1 na sa ido kan albarkatun kasa da kasashen Sin da Brazil suka samar da shi zuwa sararin samaniya; a shekarar 2003, tauraron dan Adam mai lambar 2 ya maye gurbinsa, yanzu wannan tauraron dan Adam yana yin aiki a cikin sararin samaniya. Karamini minista na ofishin jakadanci na kasar Brazil da ke kasar Sin Mr. Edson Mrinho Duarte Moteiro ya bayyana game da wannan cewa,

'saboda hadin gwiwar da suka yi, kasashen Brazil da Sin sun iya mallakar fasaha na zamani da kuma kara wa kansu karfin sa ido kan muhalli da bala'i, tauraron dan Adam nan yana da amfani sosai a fannoni da yawa, yana da muhimmanci sosai wajen biyan bukatun kasashen nan 2 a fannin bunkasuwa.'

Darektan cibiyar harkokin yin amfani da tauraron dan Adam ta kasar Sin Mr. Guo Jianning ya gabatar da cewa, an kyautata amfanin tauraron dan Adam mai lambar 2 kwarai, in an kwatanta shi da mai lambar 1, ya iya ba da bayanai na gaskiya a jere yadda ya kamata ga masu yin amfani da su iri daban daban, ya ce,

'an kyautata ingancin tauraron dan Adam mai lambar 2, ya kara karfinsa na daidaita hotuna. An kara yin amfani da bayanan tauraron dan Adam ya ruwaito mana. Ana yin amfani da bayanai daga tauraron dan Adam na sa ido kan albarkatun kasa da kasashen Sin da Brazil suka samar da shi tare a dukan larduna da birane na kasar Sin.'

An ce, yanzu kasr Sin tana yin amfani da bayanan da tauraron dan Adam na sa ido kan albarkatun kasa na kasashen Sin da Brazil ya ruwaito mana a fannonin ayyukan noma da gandin daji da yin amfani da ruwa da dai sauransu, ta ci riba a fannonin zaman al'ummar kasar da kuma tattalin arziki a bayyane.

Ban da wannan kuma, kasar Sin ta yi amfani da bayanan daga tauraron dan Adam na sa ido kan albarkatun kasa na kasashen Sin da Brazil wajen sa hannu cikin aikin yin bincike kan albarkatun yankuna na duniya cikin himma da kwazo.

Ba ma ba da bayanai na gaskiya ga hukumomin noma da gandun daji da su tsara manufofi kawai ba, har ma tauraron dan Adam na sa ido kan albarkatun kasa na kasashen Sin da Brazil ya kara taka rawa wajen sa ido kan bala'i da fasalin birane.

Darekta Guo Jianning ya ba da karin haske cewa, don mutane za su iya kara yin amfani da bayanan da tauraron dan Adam nan ya ruwaito mana, tun daga watan Afril na shekarar da muke ciki, kasar Sin ta raba bayanai ga kasashen duniya ba tare da biyan kudi ba. A sa'i daya kuma, kasar Sin ta ba da bayanan da abin ya shafa ga kasashen Malaysia da Vietnam da Iran. Mr. Guo ya bayyana cewa, saboda ingancin tauraron dan Adam na sa ido kan albarkatun kasa na kasashen Sin da Brazil yana da kyau, kasashen duniya sun kara mai da hankulansu kan wanann tauraron dan Adam. Ya ce,

'kasashen duniya suna sha'awar bayanan da tauraron dan Adam na sa ido kan albarkatun kasa na kasashen Sin da Brazil ya ruwaito mana, yanzu kasar Sin ta yi shirin yin jarrabawa kan bayanan da wannan tauraron dan Adam ya ruwaito mana a kasashen Australia da Canada da Norway a cikin wannan shekara.'

An ce, kasashen Sin da Brazil suna hada kansu su yi nazarin tauraron dan Adam na sa ido kan albarkatun kasa mai lambar 3 da mai lambar 4, wadanda za su sami babban ci gaba a fannonin fasaha da ingancin bayanai, za a kara yin amfani da su a fannoni daban daban.(Tasallah)