Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-26 21:21:50    
Kasar Sin tana kokarin kyautata sharadin bunkasa harkokin kudi a kauyuka

cri

To, jama'a masu karatu, yanzu sai mu ci gaba da shirinmu mai farin jini na "Bunkasuwar kasar Sin". A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta kara zuba kudade a kauyuka a kai a kai domin neman karuwar kudin shiga na manoma. Amma a wasu wurare, manoma wadanda suke samun arziki a kai a kai sun gamu da sabuwar matsala, wato suna da wuyar samun rancen kudi daga bankuna. A cikin shirinmu na yau za mu tattauna kan yadda gwamnatin kasar Sin ke yin kokari wajen kyautata sharadin bunkasa harkokin kudi a kauyuka domin samar wa manoma taimako wajen samun kudaden da suke bukata.

A lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin, yawan manoma ya kai kashi 60 cikin kashi dari na duk yawan mutanen lardin. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, domin sana'ar su a teku mai zurfi ta samu bunkasuwa sosai, masunta na lardin Hainan suna fatan za su iya sayen babban jirgin ruwa da ke da karfin fama da kuma jure igiyar ruwa da iska mai karfi sosai. Amma idan ana son sayen wani jirgin ruwa na kamun kifi da ya kai ton dari 1, dole ne a kashe kudin Renminbi yuan miliyan 2. Wadannan kudade ne masu yawa ga masunta. Lin Mingfang, wani masunci ne da ke birnin Sanya na lardin Hainan ya nuna damuwar masunta ya ce, "Kowa yana son sayen babban jirgin ruwa. Amma muna da wuyar samun kudi."

Tsarin kudi ya ja da baya sosai a kauyuka wata matsala ce da ke jawo hankulan gwamnatin kasar Sin sosai. A cikin tsarin raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasar Sin na shekarar bana, firayin minista Wen Jiabao ya ce, za a kara yin gyare-gyare da kyautata tsarin kudi a kauyuka. Wannan ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta riga ta gane cewa, lokacin da ake ci gaba da kara zuba karin kudi a kauyuka, dole ne a kara wa manoma hanyoyin neman rancen kudi domin raya aikin gona da kara karfin fama da bala'i daga indallahi da kuma kyautata zaman rayuwar manoma. Mr. Cheng Siwei, mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Sin yana ganin cewa, samar wa manoma taimakon rancen kudi yana da muhimmanci kwarai wajen neman bunkasuwar kauyukan kasar Sin. Mr. Cheng ya ce, "Yunkurin neman bunkasuwar aikin gona yana bukatar sharuda 3, wato kudade da 'yan kwadago da kuma sauran sharuda. Yanzu a kauyukan kasar Sin, ana da isassun 'yan kwadago, amma suna karancin kudade. Idan babu jari, za a samu wuyar neman bunkasuwar aikin gona. Sabo da haka, ta yadda za a bunkasa sha'anin kudi a kauyuka wata matsala ce mai tsanani da ke kasancewa a gabanmu."

Wasu kwararru suna ganin cewa, a halin da ake ciki yanzu bankunan da ke aiwatar da manufofin gwamnati sun samar wa manoma rancen kudi, wannan hanya ce mafi dacewa ga yunkurin kara wa manoma hanyoyin samun rancen kudi. Domin bankunan da ke aiwatar da manufofin gwamnati suna samun kudi ne daga kasafin kudin kasar. Ba su da nauyin neman riba. Sabo da haka, sun fi sauran bankunan kasuwanci dacewa wajen kyautata sharadin sha'anin kudi a kauyuka. Yanzu, bankin raya kasar Sin da yake daya daga cikin bankuna 3 da suke aiwatar da manufofin gwamnati yana yin gwajin samar wa manoma rancen kudi. Mr. Chen Yuan, shugaban bankin raya kasar Sin ya gaya wa wakilinmu cewa, "Mun yi hadin guiwa da gwamnatocin wurare daban-dabam wajen kafa tsarin tabbatar da aminci. Bisa wannan tsarin tabbatar da aminci ne za mu iya samar wa manoma rancen kudin da suke bukata. Sannan kuma za mu iya komowar da wadannan kudaden da manoma suka ara."

Ba ma kawai ana kokarin samar da taimakon sha'anin kudi bisa manufofi ba, har ma gwamnatin kasar Sin tana yin gyare-gyare kan asusun samar da rance a kauyuka. Bisa shirin da aka tsara, gwamnatin kasar Sin za ta yi kwaskwarima kan asusun ba da rance a kauyuka da ya zama bankin kasuwanci a kauyuka. Ya zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta amince da kafuwar irin wadannan bankuna 72. Wasu bankunan kasuwanci na kauyuka sun riga sun fara bayar da gudummawa ga yunkurin neman bunkasuwar aikin gona da kauyuka. Amma kwararru suna ganin cewa, har yanzu kasar Sin tana fuskantar kalubale da yawa kan yadda za a kara kyautata tsarin samar da rance a kauyuka. (Sanusi Chen)