Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-26 19:16:43    
Gwamnatin kasar Sin za ta kara samar da makudan kudade wajen tallafa wa ayyukan nazarin kimiyya a muhimman fannoni

cri

Makasudin nazarin ayyukan kimiyya a muhimman fannoni, shi ne gane yanayin halitta, da binciken gudanarwar ayyukan halitta, da samun sabon ilimi da kuma sabon hasashe da kuma sabbin dabaru. Domin daga matsayin kasar Sin na nazarin kimiyya a muhimman fannoni, gwamnatin kasar Sin ta kafa kwamitin asusun kasa mai kula da harkokin nazarin kimiyya a fannin halitta a shekarar 1986 domin samar da kudin taimako ga ' yan kimiyya na kasar don su gudanar da ayyukan nazarin kimiyya a muhimman fannoni. Yanzu kwamitin nan yana shirya jerin bukukuwa a nan Beijing domin murnar ranar cika shekaru 20 da kafa shi.

Mr. Chen Yiyu, daraktan kwamitin asusun kasar Sin mai kula da harkokin nazarin kimiyya a fannin halitta ya furta, cewa tun shekaru 20 da suka shige bayan da aka kafa wannan kwamirti, an samar da kudin kasar Sin wato Renminbi Yuan biliyan 18 domin tallafa wa ayyuka fiye da 100,000 na nazarin kimiyya a muhimman fannoni. Amma duk haka, ya kasance da babban gibi tsakanin kasar Sin da kasashen duniya wajen nazarin kimiyya a fannoni da dama. Saboda haka, za a kara samar da makudan kudade nan da shekaru biyar masu zuwa don gudanar da wannan aiki. Mr. Chen ya kuma fadi, cewa:" Nan da shekaru biyar masu zuwa, kwamitin asususn zai ci gaba da samar da kyakkyawar dama ga ' yan kimiyya na kasar wajen binciken kimiyya cikin 'yanci. Ya zuwa shekarar 2010, za a yi kokarin samun babban ci gaba wajen nazarin muhimman ayyuka 1,800 a muhimman fannoni ta hanyar kimiyya".

Wannan dai yana nufin, cewa kwamitin asusun zai samar da kudin taimako da yawansu ya kai Yuan fiye da biliyan ashirin, wato ke nan zai zarce jimlar kudaden da aka samar da su cikin shekaru 20 da suka shige.

Yayin da gwamnatin kasar Sin take kara zuba makudan kudade ga ayyukan nazarin kimiyya a muhimman fannoni, ita kuma za ta yi kwaskwarimar tsarin kula da kwamitin asusun kasar mai kula da ayyukan nazarin kimiyya a fannin halitta don kara ingiza bunkasuwar harkokin kimiyya a muhimman fannonin kimiyya. Madam Chen Zhili,wakiliyar majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta bayyana, cewa:' Ya kamata asusun kimiyya a fannin halitta na kasar Sin ya raya da kuma kyautata tsarin dogara kan kwararru da masana don su kula da harkokin nazari ta hanyar kimiyya, kuma kamata ya yi ya girmama matsayin ginshiki na kwararru da masana a cikin harkokin kirkiro da sabbin abubuwa ta hanyar kimiyya da fasaha don kago wani irin kyakkyawan muhalli na himmantar da su wajen binciken kimiyya'.

Ban da wannan kuma, kwamitin asusun ya shelanta, cewa zai ci gaba da bude hanyoyin hadin gwiwa tsakaninsa da kasashen duniya domin yin musanye-musanyen fasahohin da suka samu wajen nazarin kimiyya a fannin halitta.

An bayyana, cewa kwamitin asusun nan ya kulla dangantakar hadin gwiwa da musanye-musanye tare da kungiyoyin asusu da hukumomin nazari da yawansu ya kai 64 na kasashe da jihohi 35. Asusun kimiyya na kasar Amurka yana daya daga cikinsu. Daraktan wannan asusu Mr.Arden L. Bement ya furta, cewa:"Lallai ya kasance da ra'ayi iri daya tsakanin kasashen Sin da Amurka wajen goyon bayan harkokin nazarin kimiyya a muhumman fannoni. Ina begen za a kara yin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu. Buri iri daya dake gabanmu, shi ne goyon bayan harkokin nazari a muhimman fannoni na zamani da kuma yin hadin kai kamar yadda ya kamata".

A gun cikakken babban taron hadaddiyar kungiyar kimiyya da fasaha ta kasar Sin, wanda aka rufe ba da jimawa ba, firaminista Wen Jiabao na kasar ya gaya wa ' yan kimiyya mahalartan taron, cewa ana bukatar dogara bisa yalwatuwar kimiyya da fasaha don warware dimbin maganganun da suka wakana lokacin da ake gudanar da yunkurin bunkasa tattalin arzikin kasar Sin. Saboda haka, wajibi ne kasar Sin ta kara karfin da take da shi na kirkiro sabbin abubuwa cikin 'yanci da rashin tsangwama da kuma tallafa wa wasu ' yan kimiyya da kungiyoyin nazarin kimiyya, wadanda za su kama matsayin gaba a duniya.

Manazarta sun bayyana, cewa wannan dai ya shaida cewa gwamnatin kasar Sin za ta kara zuba makudan kudade wajen nazarin ayyuka iri daban daban ta hanyar kimiyya. Ko shakka babu za a kara mai da hankali kan ayyuka nazarin kimiyya a muhimman fannoni. ( Sani Wang )