Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-26 18:07:37    
Sinawa sukan yi wasan zaman nishadi a bikin ma'aikata

cri

Aminai masu sauraro, ko kun san cewa tun daga ran daya zuwa ran bakwai na kowace shekara, bikin duk kasa baki daya ne a kasar Sin. A duk tsawon lokacin bikin sallar, mutanen kasar Sin sukan fita daga gidaje domin yin yawon shakatawa da cefane ko gaida dangogi da aminai. A takaice dai, mutane sukan yi amfani da wannan dogon hutu domin more zaman alheri. A kasar Sin, ana kiran wannan mako a kan cewa ' Makon zinariya na ran daya ga watan Mayu'. Amma, yanzu mutanen kasar Sin suna ta kishin yin wasannin motsa jiki da zaman nishadi. Saboda haka, a duk tsawon lokacin bikin ma'aikata na wannan shekara, mutane masu yawan gaske sun yi fatsa, da hawan dawaki, da kuma yin wasan kwallon bowling da na tenis da dai sauran wasanni na zaman nishadi maimakon yin cefane da cin abinci.

A gundumar Shun Yi dake da nisa daga birnin Beijing, akwai Tafkin Jin Hai da Tafkin Yan Xi da kuma sauran madatsan ruwa. A zaman yau da kullum, mutane kadan ne sukan je can domin yin yawon shakatawa. Amma, a ' Makon Zinariya na ran 1 ga Mayu' na wannan shekara, mazauna birnin Beijing masu yawan gaske sun je can domin yin fatsa. Bangaren da abun ya shafa ya bayyana, cewa wasan yin fatsa dake iya kara lafiyar jikin mutane, wani kyakkyawan zabi ne da dimbin iyalai na birnin Beijing da birnin Shanghai da dai na sauran wurare suka yi a lokacin bikin ma'aikata na wannan shekara.

Mr. Qin Baohua, manajan club din fatsa na Tian Bao na Beijing ya furta, cewa' A lokacin dogon hutu na bikin ma'aikata na wannan shekara, mun shirya wakilan club dinmu da yawa domin yin fatsa a Tafkin Jin Hai da Tafkin Yan Xi da kuma sauran madatsan ruwa dake kewayen gundumar Shun Yi, inda suka ji dadi ainun'.

Yin fatsa, wani irin kyakkyawan wasa ne ga mutane. Amma wassu samari sun fi nuna sha'awarsu ga wasan kwallon tenis. Mr. Zhang Jianguo, wani babban jami'in club din wasan kwallon tenis na duniya na Jiangxinzhilun dake gundumar Chao Yang ta Beijing ya yi farin ciki matuka da gaya wa wakilinmu, cewa' Club dinmu yana da kananan filaye guda 7 dake cikin manyan dakuna da kuma guda 6 dake waje da dakuna. Mutane mambobin club din na iya yin wasan kwallon tenis a wadannan wurare tun daga karfe 8 na safe har zuwa karfe 11 na dare a kowace rana.'

Bisa labaran da muka samu, an ce wassu wasannin motsa jiki na gargajiya kamar wasan kwallon tenis da kuma wasan kwallon tebur da dai sauran makamantansu, lallai sun kasa biyan bukatun dimbin mazauna biranen kasar Sin. Yanzu, mutane da yawa sun fi son wasan darts, da wasan ninkaya a karkashin ruwa da kuma wasan hawan dawaki da dai sauran wasanni. Wasan hawan dawaki kuma ya fi burge mazauna biranen kasar.

Madam Wang Ping, manajar club din sukuwar dawaki na Tianxingtiaoliang na gundumar Chao Yang ta shirya wassu tsoffin ' yan club din domin yin wasan hawan dawaki a karkarar birnin Beijing, inda ta kuma samu sabbin aminai da yawa. Ta yi farin ciki da fadin cewa:' A duk tsawon lokacin bikin ma'aikata na ran daya ga watan Mayu na wannan shekara, club dinmu ya kara samun sabbin mambobi da yawa, wadanda kuma wassu daga cikinsu suka gwanance a wasan hawan dawaki.'

Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an ce miliyoyin mutanen kasar Sin sun yi wasan hawan duwatsu, da hawan dawaki, da wasan yin fatsa, da wasan kwallon badminton da dai sauran makamantansu a " Makon zinariya na bikin ma'aikata na ran 1 ga Mayu" na wannan shekara.

Shehun malami Chen Liuqin, mashahurin masanin ilmin zamantakewar al'umma na kasar Sin ya bayyana, cewa sabon tashen yin wasannin motsa jiki na zaman nishadi da ya bullo a albarkacin bikin salla ya shaida, cewa jama'ar kasar Sin sun soma bin hanyoyi da yawa wajen morewa a lokacin dogon hutu ba kamar yadda suka yi ba a da. A sa'I daya kuma ya shaida, cewa mutanen kasar Sin sun fi mai da hankali kan lafiyar jiki da kuma wasannin motsa jiki. Wannan dai sakamako ne da aka samu wajen bunkasa tattalin arziki da kuma zamantakewar al'ummar kasar Sin. ( Sani Wang )