Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-25 19:48:34    
Kara karfin tsaron kasa da raya rundunar soja da al'adun zaman gurguzu

cri

"Tsarin ka'idoji na shiri na 11 na shekaru 5-5 na raya tattalin arzikin kasa da zaman al'umma" na kasar Sin ya gabatar da cewa, bisa bukatun kiyaye zaman lafiya da dinkuwar kasa daya da samun moriyar raya kasa, ya kamata a kara karfin tsaron kasa da raya rundunar soja daidai da zamani, ta yadda za a shimfida kyayyawan halin kyautata tsaron kasa da bunkasa tattalin arziki bisa daidaici.

"Tsarin ka'idojin" ya nemi a yi kome domin aiwatar da hakkin tarihi na rundunar soja cikin sabon karni, da kara raya rundunar soja a fannin juyin-juya hali kuma bisa manufar zamanintarwa, da sa kaimi ga yin gyare-gyaren sha'anin soja mai sigar musamman ta kasar Sin, da yin kokarin kara kwarewar yaki don tsaron kai bisa sharadin sadarwa.

Ya kamata a sa ayyukan kyautata tunani da siyasa a matsayi na farko har kullum, a aiwatar da muhimman tsare-tsaren raya rundunar soja ta hanyar kimiyya da fasaha, da kirkirar hasashen sha'anin soja, da kyautata halaye nagari na hafsoshi da mayaka. Ya kamata a tsaya kan manufar hadin kai tsakanin sojoji da jama'a, da kara karfin harsashi da yin kirkire-kirkire cikin 'yanci, da kara saurin yin sauye-sauye da hawa matakin masana'antun kimiyya da fasaha na tsaron kasa, da kara kwarewa wajen yin kirkire-kirkire, da yin binciken fasaha da kayayyaki wadanda ke da amfani ga sojoji da jama'a dukka. Ya kamata a kara yin gyare-gyaren tsarin sa kaimi ga jama'a wajen tsaron kasa, da tsayawa kan tafiyar da harkokin tsaron kasa cikin ayyukan raya tattalin arzikin kasar, kuma a kafa tsari mai mulkin tsakiya da adalci da amfani irin na zamani wajen ta da jama'a da sauri don tsaron kasa.

"Tsarin ka'idoji na shiri na 11 na shekaru 5-5 na raya tattalin arzikin kasa da zaman al'umma" na kasar Sin ya gabatar da cewa, ya kamata a dosawa gaba bisa hanyar al'adu mai ci gaba sosai, a tsaya kan manufar bautawa jama'a da zaman gurguzu da ka'idar "furanni 100 sun toho, kuma mutane 100 sun yi takara", a wadatar da al'adun gurguzu, ta yadda za a biya bukatun jama'a wadanda sai kara karuwa suke a kowace rana wajen tunani da al'adu.

"Tsarin ka'idojin" ya jaddada cewa, ya kamata a aiwatar da hasashen Den Xiaoping da muhimmin tunanin "wakilai a fannoni 3" daga duk fannoni, da yin nazari da kuma aiwatar ra'ayin samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya, da kara yin bincike da kyautata hasashen Markisanci, da tsayawa kan matsayin jagoranci na Markisanci a fannin akida, da kara inganta harsashin tunanin tarayya na yin gwagwarmaya cikin hadin kai tsakanin jama'ar kabilu daban- daban na duk kasa baki daya.

"Tsarin ka'idojin" ya gabatar da cewa, ya kamata a yi kokarin bunkasa sha'anin al'adu da sana'arsa, a kirkiro nagartattun kayayyakin al'adu masu yawa kuma masu kyau domin biyan bukatun jama'a. Gwamnatin kasa za ta kara ware kudade da yawa domin sha'anin al'adu, ta yadda za a kafa cikakken tsarin yin hidima ga al'adun jama'a na duk zaman al'umma. Ya kamata a rika kyautata gyare-gyaren tsarin al'adu, da kafa tsarin tafiyar da harkokin al'adu wanda kwamitin J.K.S. ke shugabantarsa, wanda kuma gwamnatin kasar ke tafiyar da harkokinsa, da tsarin fitar da kayayyakin al'adu masu inganci. Ya kamata a kara aiwatar da dokoki kan kasuwannin al'adu da ayyukan kula da giza-gizan sadarwa, a tsaya kan ayyukan yaki da rashin da'a, da samar da muhallin zaman al'umma domin ba da gudummawa ga al'adu mai kyau da yin gyare-gyare ga al'adu maras ci gaba da kuma kawar da rubabben al'adu. (Umaru)