Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-25 10:22:37    
An yi yawon shakatawa a kasar Morocco

cri

Kasar Morocco tana arewa mao yammacin Afirka, a yammacinta shi ne tekun Atlantic, a arewacinta shi ne zirin Gibraltar ne. Kasar Morocco tana da kyakkyawan yanayi, sabo da haka akwai furanni da itatuwa da yawa, wandanda suka zama kamar zane-zane.

Kasar Morocco tana da dogon tarihi da dadaddun al'adu. A karni na 7, Larabawa sun shiga cikin kasar Morocco, kuma sun kafa kasar Larabawa a karni na 8. Tun daga karni na 15, kasashen yamma ne suka kai hari a kasar Morocco. A watan Maris na shekarar 1912, 'Yan mulkin mallaka na kasar Faransa sun yi mulki a kasar Morocco. A watan Maris na shekarar 1956, kasar ta sami 'yancin kai. Kasar Morocco kasa ce ta addinin musulunci, dukkan fadinta ya kai muraba'in kilomita dubu 459, yawan mutanenta ya kai miliyan 29 da dubu 810, wadanda yawancinsu Larabawa ne. Harshen gwamnati na kasar Morocco shi ne Larabci, amma ana iya yin amfani da harshen Faransanci a duk kasar Morocco.

Aikin gona ya zama babban sashen tattalin arziki da ya fi muhimmanci a kasar Morocco, yawan kudin da aka samu daga wajensa ya kai kashi 20 daga cikin dari na jimlar kudin kayayyakin da ake samarwa a gida na kasar Morocco, yawan mutanen da ke aikin gona ya kai kashi 44 daga cikin dari na mutanen kasar. Tsawon gabar tekun kasar Morocco ya kai kilomita fiye da dubu 1 da dari 7, sabo da haka kasar ta zama babbar kasa ta farko a Afirka wajen samar da kifaye daga cikin teku. Ban da wannan kuma kasar Morocco tana da ma'adinai masu yawan gaske. Aikin samar da ma'adinai shi ma ya zama wani muhimmin sashe na tattalin arzikin kasar Morocco, har yawan ma'adinai da ya fitar da su ya kai kashi 30 daga cikin dari na dukkan kayayyakin fici na kasar.

Kasar Morocco ta shaharra sosai a kan yawon shakatawa, wuraren masu ban sha'awa a cikin kasar Morocco su kan jawo hankulan 'yan yawon shakatawa masu yawon gaske a ko wace shekara. Birnin Rabat, babban birnin kasar Morocco yana da tsofaffin birane da masallata na zamanin da fadar Rabat, wadanda suke shaharra sosai a duk duniya. Ban da birnin Rabat kuma, kasar Morocco tana da birane da ke gabar teku da dai sauran kyawawan wuraren yawon shakatawa. Aikin yawon shakatawa ya riga ya zama wani muhimmiyar hanya da kasar Morocco ta sami kudin shiga. A shekarar 2004, yawan 'yan yawon shakatawa da suka ziyarci kasar Morocco ya kai miliyan 5 da dubu 516 da dari 5, yawan kudin da kasar ta samu ya kai dala biliyan 3 da miliyan 630.

Ko da yake kasar Sin da Morocco suna da nisa sosai, amma kasashen biyu suna da dogon tarihin cudanyar juna irin na abokantaka. A karni 8, wani 'dan daular Tang ta kasar Sin Du Huan ya taba zuwa kasar Morocco. A karni na 14, 'yan yawon shakatawa na kasashen biyu sun taba ziyarar juna. Fasahohin yin takardu da na samar da albarushi na zamanin da na kasar Sin sun je kasashen Turai ne ta hanyar kasar Morocco. Daga shekarar 1958 da kasashen biyu suka kafa dangantakar diplomasiyya, dangantakar gama kai da abokantaka da ke tsakaninsu tana kar samun bunkasuwa, shugabannin kasashen biyu sun kara kai ziyara ga juna, haka kuma suna kara karfafa cudanyarsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya da al'adu da dai sauransu. A shekarar 2005, yawan kudin da kasashen Sin da Morocco suka samu daga wajen cinikayyar da suka yi ya kai dala biliya 1 da miliyan 484.(Danladi)