Yanzu, ana nan ana kiran taron koli kan tattalin arzikin kasar Sin na shekarar 2006 a nan birnin Beijing. Manyan shugabannin gwamnatin kasar Sin da yawa sun halarci taron, kuma bi da bi ne suka bayar da laccoci kan halin da kasar Sin take ciki wajen tattalin arziki da makomar raya tattalin arziki a shekaru 5 masu zuwa. Sun bayyana cewa, kasar Sin za ta yi kokarin sauya hanyar gargajiya da take bi wajen kara karuwar tattalin arziki da kuma bin sabuwar hanyar yin masana'antu da kara muhimmanci ga aikin ba da hidima a cikin tattalin arzikin kasa, har da rage ratar da ke tsakanin kauyuka da birane don samun karuwar tattalin arziki cikin zaman jituwa.
Taron koli kan tattalin arzikin kasar Sin shi ne muhimmin aikin da ake yi a kowace shekara a gun taron nune-nunen kayayyakin kimiyya da fasaha na kasa da kasa da aka shirya a birnin Beijing, a shekarar da muke ciki, manyan shugabanni da mashahuran masana da masu masana'natu na gida da na waje da yawansu ya kai kusan 100 sun halarci taron. Dayake kasar Sin ta tsara shirin raya tattalin arziki na shekaru 5 masu zuwa a watan Maris na shekarar da muke ciki, sai mahalartan taron sun mai da muhimmanci ga makomar samun bunkasuwar kasar Sin a shekaru 5 masu zuwa a lokacin da suke tattaunawa kan halin da kasar Sin take ciki wajen tattalin arziki. A lokacin da suka bayar da laccocinsu, manyan shugabannin kasar Sin su ma sun bayyana shiri na hakika da gwamnatin kasar Sin ta tsara wajen raya masana'antu da yadda za ta zuba jari.
Mataimakiyar direktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin Ou Xinqin ta mai da hankali ga bayyana wasu manufofin kasar Sin na kara saurin raya sha'anin ba da hidima. Ya bayyana cewa, manufar raya sha'anin ba da hidima na kasar Sin ita ce, ya zuwa shekarar 2010, za a kara karuwar yawan kudin da aka samu daga wajen sha'anin ba da hidima da kashi 30 cikin dari bisa yawan kudin da aka samu daga wajen ayyukan sarrafe-sarrafe na duk kasa na shekaru 2005 .Yawan wadanda za su sami aikin yi zai kara karuwa da kashi 40 cikin dari, kuma tsarin sha'anin ba da hidima ya kara samun kyautatuwa a bayyane, shi ya sa yanzu an riga an samu wasu masana'antun ba da hidima da ke da ikon mallakar ilmi da shahararrun lambobin kayayyakinsu da kuma da ke da karfin takara a kasashen duniya.
Mataimakin direktan cibiyar yin nazari kan raya kasa ta Majalisar gudanarwa ta kasar Sin Liu Shijin shi ma ya bayyana wa mahalartan taron ra'ayinsa game da batun sauyawar hanyar da kasar Sin take bi wajen kara karuwar tattalin arziki. Ya bayyana cewa, kodayake kasar Sin tana da fiffiko wajen yin takara ta hanyar yin amfani da danyun kayayyaki marasa tsada , amma bisa albarkacin kara karuwar kudaden shiga ga mutanen kasar Sin da abubuwan da aka kashe wajen aikin kawo albarka ne, irin wannan fiffiko ya yi ta raguwa a kai a kai, yanzu, kasar Sin tana bukatar ci gaba da samun sabon fiffikon yin takara bisa ci gaban da ta samu wajen fasahohi .
Mataimakin babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya Kim Hak Su ya bayyana cewa, mun mai da hankali ga sauyawar da kasar Sin ta samu wajen raya tattalin arziki ta hanyar gargajiya da take bi zuwa hanyar ilmi da take bi, musamman ma ta kara nauyin tattalin arziki na mutane masu zaman kansu da ke cikin bunkasuwar tattalin arzikin birane. Irin wannan nauyin na da muhimmanci sosai ga kasar Sin da kasashen da ke waje da ita, har ma ga duk shiyyar Asiya da tekun Pasific .
Mr Kim Hak Su ya kara bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta zama muhimmin karfin ingiza ga raya tattalin arzikin duk duniya, kuma bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin na da ma'ana mai muhimmaci ga shiyyar Asiya da tekun Pasific.(Halima)
|