Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-24 20:01:56    
Kyautar girmamawa ta Nobel

cri

A wannan mako za mu amsa tambayar da mai sauraronmu daga birnin Abuja na kasar Nijeriya, alhaji Shekarau Abba Adamu ya yi mana, wato shin yaushe ne aka fara ba da lambar yabo ta Nobel, kuma yaya ake zaben wadanda za su sami kyautar?

An haifi Alfred Nobel a ran 21 ga watan Oktoba na shekara ta 1833 a birnin Stockholm, hedkwatar kasar Sweden. Mr.Nobel ne ya kirkiro nakiya, haka kuma ya cimma nasarori dubu dubai a bangaren nazarin ilmin kimiyya. Bayan haka kuma, Mr.Nobel ya kafa masana'antu da dama, ta yadda ya tattara dukiyoyi masu dimbin yawa. Kafin ya rasu, sai Nobel ya rubuta wasiyyar cewa, 'ku mayar da dukiyoyina da su zama asusu, don a bayar da ruwan da aka samu daga asusun a ko wace shekara a matsayin kudin kyauta ga wadanda suka ba da babban taimako ga 'yan Adam a shekarar da ta gabata.' Bisa wannan wasiyyar, tun daga shekara ta 1901, an fara ba da wannan kyautar girmamawa ta Nobel a duk fadin duniya. Ban da wannan, Mr.Nobel ya kuma rubuta a cikin wasiyyarsa cewa, 'ya kamata a karkasa wannan kyauta cikin kashi biyar, wato ga wadanda suka fi samun babban ci gaba a bangaren physics da bangaren chemistry da bangaren ilmin halittar jikin dan Adam da ilmin aikin likita da bangaren ayyukan adabi da kuma ga wadanda suka ba da babban taimako a wajen sada zumunta a tsakanin kasa da kasa da kuma yi watsi da nuna karfin tuwo.' Sabo da haka, an karkasa lambar yabo ta Nobel cikin kyaututtuka 5. Daga baya kuma, a shekara ta 1969, an kara kirkiro wata kyauta, wato ta shida, kyautar Nobel ta ilmin tattalin arziki.

Hanyar da ake bi wajen zaben wadanda suka ci kyautar nan ta Nobel ita ce, cibiyar nazarin ilmin kimiyya ta gidan sarautar Sweden za ta kula da zaben wadanda za su sami kyautar Nobel a bangaren Physics da chemistry da kuma ilmin tattalin arziki, sa'an nan kuma, cibiyar nazarin adabi ta kasar Sweden ita kuma za ta dauki nauyin zaben wanda zai ci kyautar Nobel kan ayyukan adabi. Bayan haka kuma, wani kwamitin da ke da mutane 5 da majalisar kasar Norway ta zaba zai dauki nauyin fitar da wanda ko wadanda za su sami kyautar nan ta Nobel a bangaren kiyaye zaman lafiya. Ban da wannan, Mr.Nobel ya kuma jaddada a cikin wasiyyarsa cewa, 'tilas ne a bayar da kyautar ga wadanda suka fi cancanta, ba tare da ka'akari da kasashen da suka fito da launin fatansu da kuma addinan da suke bi ba.' Bayan haka kuma, kwamitocin kula da kyaututtukan Nobel iri daban daban da muhimman jami'o'in duniya da kuma shahararrun masana da masu ilmin kimiyya su ne za su mika sunayen 'yan takarar neman wannan kyautar Nobel, kuma wadanda suka ci kyautar za su fito ne daga wadannan 'yan takara.

A kan sanar da sunayen wadanda suka sami kyautar Nobel a tsakiyar watan Oktoba na ko wace shekara, kuma a kan yi bikin ba da kyautar a dakin sauraron kide-kide na birnin Stockholm, kuma a ranar 10 ga watan Disamba na ko wace shekara, wato ranar da Mr.Nobel ya riga mu gidan gaskiya. Sarkin kasar Sweden shi kansa ne zai halarci bikin, inda zai mika kyautar ga wadanda suka ci ta. Wadanda suka sami kyautar kuwa su kan karbi takardar shaida kyautar da lambar yabo ta zinari da kuma kudin kyautar a gun bikin, sa'an nan kuma za su bayar da jawabi na minti 3 a gun liyafar da aka kira. Ko wace kyautar Nobel ana iya bayar da ita ga mutane daga bangarorin nazari biyu tare, ko uku a iyaka. Muna iya cewa, kyautar Nobel buri ne ga mutane da dama ke neman cimmawa. Sakamakon kokarin da kasashen Sweden da Norway suka yi ba tare da kasala ba, kyautar Nobel ta rigaya ta zama babbar kyauta ta duk duniya wadda ta jawo hankulan kasashen duniya baki daya.

(Lubabatu Lei)