Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-24 19:51:28    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(18/05-24/05)

cri
An yi babban wasannin motsa jiki na kasar Sin a birnin Suzhou da ke gabashin kasar tun daga ran 20 zuwa ran 30 ga watan Mayu. A kan yi wannan kasaitaccen wasanni ne sau daya a ko wadanne shekaru 2. Yawancin gasannin da aka tanada cikin wannan wasanni gasanni ne na shakatawa ne da ba a yi a cikin wasannin Olympic ba, kamarsu kwallon billiards da yin darar chess da dai sauransu.

An rufe cikakken taro na karo na 6 da kwamitin kula da harkokin wasannin Olympic na karo na 29 na Kwamitin wasannin Olympic na duniya ya shirya a nan Beijing a makon da ya gabata, inda shugaban wannan kwamiti Mr. Hein Verbruggen ya nuna gamsu sosai kan ci gaban ayyukan shirya wasanin Olympic na Beijing, yana ganin cewa, ana shirya wasannin Olympic na Beijing lami lafiya.

Ban da wannan kuma, mun sami labari game da wasannin Olympic na nakasassu na Beijing daga kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing a kwanan baya cewa, a lokacin wasannin Olympic na nakasassu na Beijing na shekarar 2008, za a ba da kudin tafiye-tafiye ga dukan 'yan wasa da jami'ai masu shiga wannan wasanni da kuma kudin abinci da masauki da za su yi amfani da su a Beijing, wanda karo ne na farko a tarihin wasannin Olympic na nakasassu.

A 'yan kwanakin da suka wuce, Hadaddiyar kungiyar wasan kokawa ta duniya ta sanar da cewa, a cikin wasannin Olympic da za a yi a Beijing a shekarar 2008, za a ci gaba da yin gasanni guda 4 tsakanin mata, kuma lambobin zinare da za a yi takarar neman samunsu za su yi daidai da na yanzu, amma za a kara wata lambar tagulla a cikin ko wace gasa.

A cikin karon karshe na gasar wasan kwallon tennis tsakanin mata biyu biyu da aka yi a kasar Morocco a ran 20 ga wata, 'yan wasan kasar Sin Zheng Jie da Yan Zi sun lashe 'yan wasan kasar Amurka, sun zama zakaru. Sun taba zaman zakaru a cikin budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Australia a bana, za su shiga budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta kasar Faransa a karshen wannan wata.

A cikin karon karshe na gasar cin kofin zakara ta wasan kwallon kafa ta kungiyar UEFA ta shekarar 2005 zuwa ta 2006 da aka yi a Paris a ran 17 ga wata, kungiyar Barcelona ta kasar Spain ta lashe kungiyar Arsenal ta kasar Birtaniya da cin 2 da 1, ta haka ta ci wannan kofi a karo na 2 a tarihinta.(Tasallah)