Assalamu alaikum ! Jama'a masu karantun shafinmu na Internet, ga shirinmu na musamman na "Duniya ina labari" na yau mai lakabin haka : Kasar Sin tana kafa cikakken tsarin tabbatar da aikin zirga-zirgar jiragen ruwa .
Yanzu Kasar Sin tana kafa cikakken tsarin tabbatar da aikin zirga-zirgar jiragen ruwa , ta yadda za a samar da aikin hidima sosai ga jiragen ruwan da suke zirga-zirga a tekun dake gabobin tekun kasar Sin . Pang Ying , wakiliyar Rediyon kasar Sin ta aiko mana labari daga birnin Shanghai cewa ,
Kungiyar alamun zirga-zirgar jiragen ruwa ta duniya wata kungiya ce wadda hukumomin kula da alamun zirga-zirgar jiragen ruwa na kasashe daban daban suka kafa don samar da aikin hidima . A shekarar 1957 an kafa wannan kungiyar . Yanzu ana yin taro na 16 na wannan kungiyar a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin . Wakilai fiye da 400 wadanda suka zo daga
Kasar Amurka da Ingila da Jamus da Canada da Japan da sauran kasashe da shiyyoyi kusan 45 sun halarci taron . A gun taron sun yi musanye-musanyen fasahohi , kuma sun tattauna yadda za a hada gwiwa a wajen samar da aikin hidima ta alamun zirga-zirgar jiragen ruwa .
A gun taron , Liu Gongcheng , mataimakin shugaban Hukumar harkokin teku ta kasar Sin ya bayyana cewa , kasar Sin za ta kafa cikakken tsarin tabbatar da aikin zirga-zirgar jiragen ruwa a kan tushen alamun zirga-zirgar na yanzu .
Mr. Liu ya ce , wannan cikakken tsarin zai ba da taimako sosai ga jiragen ruwa ciki har da samar da labarun tsaron jiragen ruwa da aikin hidimar fitilun alamu . Kuma za mu tabbatar da cewa , a kowane lokaci da kowane wuri masu daukar jiragen ruwa za su iya samun aikin hidima mai kyau.
Liu Gongcheng ya ce , tun daga karshen shekarar 2004 zuwa yanzu , kasar Sin ta gina tashoshin ruwa guda 50 wadanda jiragen ruwa za su iya ganin alamun zirga-zirga kuma aka hade su da hanyoyin sadarwar Internet , shi ya sa duk muhimman tashoshin ruwa na duk kasar suna iya ganin inda jiragen ruwa ke tafiye-tafiye ko wace tashar suke hutu .
Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labarin
cewa , Torsten Kruse . babban sakataren Kungiyar alamun zirga-zirgar jiragen ruwa ta duniya ya bayyana cewa , Kasar Sin tana kafa cikakken tsarin tabbatar da aikin zirga-zirgar jiragen ruwa . Wannan zai kawo moriya ga kasashe daban daban na duniya . Wannan tsarin kasar Sin zai samar da cikakkun labaru cikin lokaci ga jiragen ruwa da tashoshin ruwa . A ganina wannan tunani yana da hangen nesa . Muna bukatar wannan hadin gwiwar tsakanin kasashen duniya . Kowane aikin da kasar Sin ta yi , kasashe daban daban na duniya za su sami moriya daga wannan aikin .
To, jama'a masu karatun shafinmu , shirin "Duniya ina labari " da za mu iya kawo muku ke nan a yau . Ado ne ya fasara wannan bayanin . Da haka muke muku sallama tare da fatan alheri .(Ado )
|