Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-23 21:21:30    
Kasashen Sin da Nijeriya sun kafa yankin cinikayya cikin 'yanci na Lekki cikin hadin gwiwarsu

cri

Assalamu alaikun, jama'a masu sauraro, yanzu lokaci ya yi da za mu gabatar muku da shirinmu na Sin da Afirka wanda mu kan kawo muku a ko wane mako. A cikin shirinmu na yau, za mu karanta muku wani bayani da wakilan gidan redion kasar Sin suka taho da shi, bayan da suka kai ziyara a yankin cinikayya cikin 'yanci na Lekki, wanda kasashen Sin da Nijeriya suka kafa shi cikin hadin gwiwarsu. To, bismilla:

Domin kara sa kaimi ga manyan kamfanonin kasar Sin masu inganci da su gudanar da ayyukansu a kasashen waje da kara gama kai da ke tsakanin Sin da Nijeriya a kan tattalin arziki, da cimma burin taimakon juna da ke tsakanin bangarorin biyu a kan tattalin arziki, a ran 11 ga wata Mayu, cikin hadin gwiwa, kasashen Sin da Nijeriya sun kafa yankin cinikayya cikin 'yanci na Lekki da ke gabar tekun Atlantic wato a wani wurin da ke da nisan kilomita 60 da ke kudu maso gabashin birnin Lagos, babban birnin kasar Nijeriya a fannin tattalin arziki. a gun bikin kafa wannan yankin cinikayya na Lekki, jama'ar wurin sun yi raye-raye, domin maraba da manyan baki daga kasar Sin.

Wannan yankin cinikayya na Lekki yana birnin Lagos. Birnin Lagos yana da mutane miliyan 13, kuma shi ne cibiyar tattalin arziki ta kasar Nijeriya, bayan an gama aikin kafa yankin cinikayya na Lekki, za a iya daga matsayin masana'antu da kasuwanci na birnin Lagos sosai, za a iya samar wa mutane masu yawan gaske ayyukan yi, ta haka za a sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki na duk kasar Nijeriya. Sabo da haka, jama'ar birnin Lagos suna maraba da kamfanonin kasar Sin da su kafa masana'antu ko zuba jari a birnin. Wani mazaunen wurin mai suna Prince Philips ya zanta da wakilanmu inda ya ce,

'Haka ne, wannan yankin cinikayya na Lekki zai bayar da guraban ayyuka da yawa gare mu, idan muna da ayyukan yi, to, wannan ya bayyana cewa, muna da abinci a kan tebur dinmu. Wannan yanki zai bayar da guraban ayyuka da yawansu ya kai dubu 300, wannan yana da kyau. Ina ganin cewa, mazaunan wurin suna farin ciki da haka.'

Kasar Nijeriya kasa ce da ta daddale yarjejeniya Iome, sabo da haka, Nijeriya tana iya fitar da kayayyaki zuwa kasuwar kungiyar EU ba tare da biyan harajin kwastan da yawa ba, idan aka kafa yankin cinikayya a Nijeriya, cikin sauki ne za a iya sayar da kayayyaki zuwa dukkan kasashen Afirka da Turai da Amurka da kuma shiyyar gabas ta tsakiya. A sa'i daya kuma, kasar Nijeriya ta zama ta 5 a duk duniya wajen fitar da man fetur. Kamfanonin kasar Sin da yawa da ke Nijeriya sun ga wannan damar yin cinikayya.

Mr. Zhang Huanyu shi ne manajan kamfanin sayar da kayayyakin lantarki mai suna Nari na kasar Sin, wannan kamfani ya shahara sosai a kasar Sin, a wannan karo Mr. Zhang shi ma ya halarci wannan bikin kafa yankin cinikayya na Lekki. Ya ce,

'A wannan karo, na sami nasarori da yawa. Na ga halin da ake ciki dangane da tattalin arziki a Nijeriya da yadda jama'ar wurin suke zama. Ni ma na samu wasu labarai game da masana'antun lantarki na kasar Nijeriya. kasar Nijeriya ta fi girma a yammacin Afirka, tana da babban boyayyen karfin zuba jari.'

Bisa shirin da aka yi, duk fadin yankin cinikayya cikin 'yanci na Lekki zai kai muraba'in kilomita 165, yankin yana da tashoshin jiragen ruwa da dakunan ajiye kayayyaki da masana'antun samar da lantarki da dai sauran manyan gine gine, wannan yanki zai shafi masana'antun samar da kayayyakin lantarki na gida na komfuta da na tufafi da man fetur da jigilar kayayyaki da dai sauransu. Kamfanin CCECC wato kamfanin zuba jari da samun bunkasuwa na kasar Sin da gwamnatin birnin Lagos za su zuba jari da yawansu ya kai dala miliyan 267 a kan wannan yanki, bangaren kasar Sin yana da yawan hannun jari da yawansu ya kai kashi 60 daga cikin dari, bangarorin biyu za su kafa wani kamfani daban domin kula da wannan yanki.

Jakadan kasar Sin da ke Nijeriya shi ma ya halarci bikin kafa yankin a ran nan, ya yi wani jawabi cewa,

'Na yi imani cewa, yankin cinikayya cikin 'yanci na Lekki zai zama wani yankin masana'antu na zamani kuma wani shahararren wurin yawon shakatawa a duk duniya. Bari mu yi kokari tare domin mayar da Lekki da ya zama wani yankin masana'antu da zai iya bayar da tasiri ga birnin Lagos da dukkan shiyyar yammacin Afirka.'

A ran nan, wakilin shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo kuma ministan kasuwanci na kasar Nijeriya Idriss Waziri shi ma ya halarci bikin kafa yankin cinikayyar Lekki. Ya yi wani jawabi cewa, ya yi imani cewa, kasar Sin za ta zama wata muhimmiyar kasa a duk duniya a karni na 21, kuma ya yi imani cewa, bunkasuwar kasar Sin za ta kara sa kaimi ga bunkasuwar kasar Nijeriya, yankin cinikayya cikin 'yanci na Lekki zai kara karfafa dangantakar abokantaka da ke tsakanin kasashen biyu(Danladi).