Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-23 18:48:40    
Za a yi wani sabon tashen zuba jari da masana'antu da kamfanoni na kasar Sin suke yi a Nahiyar Afrika

cri

Sanin kowa ne, yanzu kasashen babbar Nahiyar Afrika suna ta kara bude kofa ga kasashen duniya, kuma ana ta samun babban ci gaba wajen musanye-musanyen cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Saboda haka, zuba jari da masana'antu da kamfanoni suke yi, kila zai zama wani muhimmin salo ne da kasar Sin za ta bi wajen zuba wa kasashen Nahiyar Afrika jari. Amma a da ba haka ba ne, wato gwamnatin kasar Sin kawai ta zuba jari kuma wassu kananan ' yan kasuwa masu zaman kansu sukan yin cinikayya tare da kasashen Afrika ba bisa babban mataki ba.

A gun wani dandalin tattaunawa na farko da aka soma gudanar da shi jiya Litinin a nan Beijing kan batun zuba jari a Nahiyar Afrika, wassu kwararru sun kiyasta, cewa nan da shekaru biyar zuwa shekaru takwas masu zuwa, kila wani lokaci ne mafi dacewa da zuba jari da masana'antu da kamfanoni na kasar Sin za su yi a Nahiyar Afrika. Saboda haka, ya kamata masu masana'antu da suke da kyawawan sharuda su yi shiri sosai.

Mr. Chi Changsheng, daraktan ofishin nazarin harkokin tattalin arziki na Cibiyar kula da hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasa da kasa ta kwamitin kula da harkokin gyare-gyare da na raya kasa na kasar Sin ya furta, cewa a 'yan shekarun baya, yanayin siyasa na Nahiyar Afrika ya gamsar da mutane, kuma kasashen Nahiyar suna bunkasa tattalin arziki taka tsantsan, kazalika muhallin zuba jari na kara kyautatuwa, dadin dadawa kasashen Nahiyar Afrika sukan nuna gatanci wajen aiwatar da manufofin zuba jari. Duk wadannan suna nan suna mayar da Nahiyar Afrika a matsayin wani wurin sabon tashen zuba jari a duniya.

Sa'annan Mr. Chi Changsheng ya fadi, cewa lallai ya kasance da kyakkyawar dama ga masana'antu da kamfanoni na kasar Sin wajen samun riba mai tsoka idan sun shiga cikin wannan babbar Nahiya tun da wuri. Yanzu yawan masana'antu da kamfanoni masu hadin gwiwar jari na kasar Sin dake Nahiyar Afrika ya riga ya zarce 600.

A gun dandalin tattaunawar, jagoran kungiyar jakadun kasashen ketare dake kasar Sin kuma jakadan kasar Kamaru dake wakilci a nan ya bayyana, cewa ya kamata masana'antu da kamfanoni na kasar Sin su zabi ayyukan gine-gine da farko da za su yi a wassu muhimman kasashe da jihohi yayin da suke la'akari da zuba jari a Nahiyar Afrika ; haka kuma su iya zuba jari wajen yin safiyo, da hakar ma'adinai, da sufuri da kuma na raya makamashi da dai sauran fannoni.

Ban da wannan kuma, jakadan kasar Kongo Brazaville dake kasar Sin ya shawarci gwamnatin kasar Sin da ta fito da kwararan matakai don himmantar da masana'antu da kamfanoni masu karfi na kasar wajen zuba jari a kasashen Afrka. A sa'i daya kuma, ya jaddada, cewa ya kamata kasashen Afrika su ma su nuna himma da kwazo wajen samar wa masana'antu da kamfanoni na kasar Sin kyakkyawar dama don ci gaba da ingiza yunkurin cinikayya da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.

A gaban gayyata mai faranta rai da kasashe daban daban na Afrika suka yi wa masana'antu da kamfanoni na kasar Sin, wassu manazarta mahalartan dandalin tattaunawar sun bayyana, cewa ko shakka babu ya kasance da kyakkyawar makoma ga masana'antu da kamfanoni musamman ma na jama'a na kasar Sin wajen zuba jari a Nahiyar Afrika ; Amma duk da haka wajibi ne su mai da hankali yayin da suke tsaida kuduran da abun ya shafa, wato ke nan kada su yi kuskuren mayar da Nahiyar Afrika a matsayin wani wuri mai talauci kuma maras daraja wajen zuba masa jari ; haka kuma bai kamata su yi hasashen cewa ya kasance da zinariya ko'ina a Nahiyar Afrika ba. A takaice dai, wajibi ne su duba yanayin kasuwannin kasashen Afrika sosai don gudun samun hadari wajen zuba jari.( Sani Wang )