Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-23 18:06:30    
yawon shakatawa a birnin Luoyang na kasar Sin

cri

Birnin Luoyang tsohon birni ne na lardin Henan da ke tsakiyar kasar Sin, kuma yana daya daga cikin masoman wayin kai a kasar Sin. Abubuwa biyu da suka fi shahara a wannan birni su ne, kogon dutse da aka sassaka mutum-mutumi a kan bangwayensa da kuma wani irin kyakkyawan fure da ake kira "Peony" a Turance.

Kogon dutse mai suna Longmen da aka sassaka mutum-mutumi a kan bangwayensa yana wani wuri da ke da nisan kilomita 13 daga kudancin birnin Luoyang. Yau da shekaru 1500 ke nan da aka fara yinsa. A gun akwai duwatsu biyu da ke fuskantar juna, kuma ruwan kogi da ake kira Yihe yana malalawa a tsakaninsu. An huda koguna da yawansu ya wuce 2300 a kan bangwayen duwatsun nan biyu, wadanda tsawonsu ya kai kimanin kilomita 1 daga yamma zuwa gabashi. Yawan mutum-mutumin addinin Buddah masu kayatarwa da tsofaffin kwararrun masassaka na kasar Sin suka sassaka a kan bangwayen wadannan koguna ya wuce dubu dari.

Dalilin da ya sa aka sassaka wadannan mutum-mutumin addinin Buddah da yawa kamar haka, shi ne domin sarkin daular Beiwei na kasar Sin a karshen karni na 5 ke tsananin bin addinin Buddah. An ce, gunkin addinin Buddah yana saka wa mutane alheri bisa yawan mutum-mutumin addinin Buddah da ake sassaka. Da jin haka, sai wannan tsohon sarkin kasar Sin ya yanke shawara a kan sassaka mutum-mutumin addinin Buddah masu dimbin yawa a kan bangwayen kogunan nan. Malama Yang Ting wadda ke aiki a kogunan duwatsun Longmen ta bayyana cewa, "babban mutum-mutumin addinin Buddah da aka sassaka a kan bangon kogo mai suna Binyang a zamanin daular Beiwei shi ne Sakyamuni wanda ya kirkiro addinin Buddah. Jikin mutum-mutuminsa dogo ne siriri. Amma mutum-mutumin addinin Buddah da aka sassaka a sauran koguna a zamanin daular Tang masu kiba ne. Daga wannan, an gano cewa, ya kasance da ma'auni masu shan banban da ake bi wajen sassaka mutum-mutumin nan a zamanin daular Beiwei da ta Tang. "

A shekarar 2000, bisa matsayinsa na babban dakin nunin fasahar sassakar duwatsu, an shigar da kogon dutse mai suna Longmen cikin "littafin sunayen tsoffafin kayayyakin al'adu na duniya". Malam Ma Shizhang, shehun malami mai binciken tsoffafin kayayyaki na Jami'ar Beijing yana ganin cewa, "kogon dutse mai suna Longmen da aka sassaka mutum-mutumi a kan bangwayensa ya kiyaye abubuwa da yawa. Daga wajensu, za a gano abubuwan addini, da tarihin kogon dutsen nan da tattalin arziki da fasaha da al'adu. Kamata ya yi a ce, shigar da shi cikin "littafin sunayen tsoffafin kayayyakin al'adu na duniya" ya tabbatar da darajarta. "

Idan wani ya sami damar yin yawon shakatawa a kogon dutsen nan na birnin Luoyang, to, zai iya halartar bikin wani irin fure da ake kira "Peony" a Turance. Irin wannan fure ya kan toho sosai a birnin Luoyang tun daga farkon watan Afrilu zuwa farkon watan Mayu, don haka birnin ya kan shirya gaggarumin bikin furen nan ta yadda masu sha'awarsa za su more wa idanunsu. Malam Guo Congbin, mataimakin magajin gari na Luoyang ya bayyana cewa, yau da misalin shekaru 100 da ake noman furen Peony a birnin Luoyang, 'yan birnin nan na takama da irin wannan fure da ke alamanta zaman alheri da arziki. Ya kara da cewa, "ana iya samun duk ire-iren furen Peony na duniya a birnin Luoyang. Ban da cewar yawansu ya wuce kimanin 970, filayen noman furen nan ma yana da fadi kwarai. Yanzu, fadin lambun irin wannan furi ya wuce kadada 2000 a birnin Luoyang, in wani ya sa kafa a cikin lambun nan, to, lambun zai burge shi kwarai."

Furen Peony launukansa iri daban daban ne, daga cikin su akwai launi mai ruwan hoda da rawaya da fari da baki da tsanwa da kuma shudi. In an sami damar zuwa birnin Luoyang a lokacin da furen nan ke toho sosai, to, za a more wa idanu da su, za a ji dadi kwarai. (Halilu)