Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-23 15:07:55    
Tsohon babban darektan kungiyar WHO marigayi Lee Jong-wook

cri

Ran 22 ga wata, a birnin Geneva, shugaban babban taron kiwon lafiya na duniya na karo na 59 kuma ministar kiwon lafiya ta kasar Spain madam Helena Salgado ta sanar da cewa, a ran nan da sassafe, a Geneva, babban darektan Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya wato WHO Mr. Lee Jong-wook mai shekaru 61 da haihuwa ya rasu a sakamakon ciwo , wanda aka kai masa asibiti cikin gaggawa a kwanan baya, amma a karshe dai likitoci ba su kubutad da shi ba.

Madam Salgado ta darajanta gudummowar da marigayi Lee Jong-wook ya bayar a fannin sha'anin kiwon lafiya na duniya bayan da ya zama babban darektan kungiyar WHO a shekaru 3 da suka wuce, ta kuma nuna ta'azziya ga rasuwarsa sosai. Saboda shawarar da ta bayar, dukan wakilai masu halartar taron sun tashi, sun nuna alherinsu har tsawon mintoci 2.

An haifi Mr. Lee a birnin Seoul na kasar Korea ta Kudu a ran 12 ga watan Afril na shekarar 1945, ya yi aure, yana da wani da. A lokacin da yake karatu a kwalejin ilmin aikin likita na Seoul, Mr. Lee ya kula da masu fama da ciwon albaras a kauyuka. Bayan ya gama karatu, ya ci gaba da yin karatu a jami'ar Hawaii ta kasar Amurka, inda ya sami digiri na biyu a fannin ilmin aikin likita na al'umma. Daga baya, ya yi aiki a cibiyar cututtuka na wurare masu zafi ta Samoa. A shekarar 1983, Mr. Lee ya shiga cikin reshen kungiyar WHO da ke tekun Pacific na yamma, daga nan ne ya fara kulla hulda a tsakaninsa da kungiyar WHO.

Tun bayan da ya fara aiki a cikin babban zauren kungiyar WHO da ke Geneva a shekarar 1994, Mr. Lee ya taba kula da wasu muhimman ayyuka.

A cikin shekaru 9 da suka wuce, wato tun daga shekarar 1994 har zuwa ta 2003, Mr. Lee ya ja gorancin manyan ayyuka 2 na kungiyar WHO, wato yaki da ciwon inna da ciwon tibi, ya gwada gwanintarsa sosai a fannin shirya da kuma tafiyar da ayyuka, saboda haka, mutanen rukunin kiwon lafiya na duniya sun yaba masa kwarai. A lokacin da yake hawan karagar babban kwamanda na shirin allurar rigakafin ciwon agana, Mr. Lee ya yi tattaunawa da hadin gwiwa da rukunin masana'antun magunguna daga duk fannoni, haka kuma ya yi kwaskwarima, ya dora muhimmanci kan masu ilmin kimiyya da fasaha na zamani. Sa'an nan kuma, ya yi amfani da akasarin ra'ayoyin jama'a, ya yi cudanya da bangarori daban daban, ta yadda an kara yawan kudin da aka zuba kan shirin allurar rigakafin ciwon agana daga dalar Amurka miliyan 15 zuwa dalar Amurka miliyan 70 a ko wace shekara, haka kuma, an kara yin allurar rigakafin ciwon agana a wasu kasashe masu tasowa, musamman ma tsakanin yara na kasashe mafi fama da talauci. Saboda babbar gudummowar da ya bayar wajen yaki da cututtuka masu yaduwa, an mayar da shi a matsayin 'sarkin allurar rigakafi'. A shekarar 2000, bayan da Mr. Lee ya zama jami'in kula da sashen shawo kan ciwon tibi, wannan sashe ya tattara abokan yin hadin gwiwa fiye da 250 daga kasashe daban daban, wadanda ke kunshe da asusu iri daban daban da uban tafiya da masana'antu da kungiyoyin da ba na gwamnati ba. An tafiya da aikin shawo kan ciwon tibi a duk fadin duniya lami lafiya a karkashin shugabancinsa.

A watan Yuli na shekarar 2003, a lokacin da mai yiwuwa ne ciwon SARS zai sake barkewa a ko wane lokaci, haka kuma, kwayoyin murar tsuntsaye za su haddasa barkewar mura tsakanin mutane a duk duniya, marigayi Lee Jong-wook ya kama mukamin babban darektan kungiyar WHO, ta haka ya zama dan kasar Korea ta Kudu ne na farko da ya zama shugaba na hukumar duniya da ke karkashin shugabancin Majalisar Dinkin Duniya. A karkashin shugabancinsa, kungiyar WHO ta kyautata tsarin yin bincike kan cututtuka masu yaduwa da kuma tsarin ko ta kwana, ya tsara shirin ko ta kwana domin annobar murar tsuntsaye na duniya mai amfani. Ya sha yin gargadi cewa, ba zai yiwu mutane za su yi rigakafi da daidaita barkewar annobar murar tsuntsaye yadda ya kamata ba, illa za su share fage kwarai da gaske. Ban da wannan kuma, a cikin wa'adin aikinsa na tsawon shekaru 3, kungiyar WHO ta sami babban sakamako wajen kawar da ciwon inna da kuma shawo kan ciwon AIDS a duk duniya.

Marigayi Lee Jong-wook ya kan ce, makasudin aikinsa shi ne raya kungiyar WHO da ta zama hukuma ce mai bauta wa matalauta. Ya kuma bayyana haka cewa,' ya kamta a zagulo shi bisa gudommowar da kungiyar WHO ta bayar kai tsaye da kuma sakamakonta, a maimakon albarkatun kasa da kuma kudin da aka yi amfani da su.'(Tasallah)