Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-22 21:03:35    
Shan ruwa ta hanyar kimiyya ya iya kiwon lafiya

cri

Kowa ya sani cewa, ruwa yana da matukar muhimmanci ga dan Adam, idan wani ya rasa ruwan da yawansa ya kai kashi 15 cikin dari a cikin jikinsa, to, zai shiga halin bakin mutuwa. Saboda haka muna bukatar shan ruwa a ko wace rana, amma yadda muka sha ruwa yadda ya kamata? To, yanzu za mu tabo magana kan shan ruwa da kuma kiwon lafiya.

Da farko dai, za mu gabatar muku wani mutum mai kishin shan ruwa kwarai, sunansa Yu Guanxiong. Mr. Yu ya kan sha ruwa kilogram 25 a ko wace rana. Dalilin da ya sa haka shi ne Mr. Yu ya ji rauni mai tsanani a cikin hadarin mata a ran 21 ga watan Disamba na shekarar da ta gabata, ko da an kubutar da shi, amma ya gamu da abu mai ban mamaki. Ya fi son shan ruwa, amma bai ci abin ba. Saboda rashin abinci, Mr. Yu ya yi siriri har kilogram fiye da 10 a cikin tsawon watanni 4 kawai, ba yadda zai yi ba, sai ya je wajen likita.

Shehun malami Li Qifu, wanda ke aiki cikin asibiti na farko na jami'ar ilmin aikin likita ta Chongqing ya yi binciken lafiyar Yu Guanxiong, yana ganin cewa, kwakwalwar Yu ta ji rauni a cikin hadarin mota, ya kamu da ciwon fitsari na musamman. Ya yi bayani kan wannan cewa, 'kodar mutum ta hana rasa ruwa daga jikin mutum kamar wata madatsar ruwa, kwakwalwa ta sarrafa wannan madatsar ruwa. Dalilin da ya sa Mr. Yu ya kamu da ciwon fitsari na musamman shi ne kwakwalwarsa ta jikata, bai iya sarrafa kodarsa yadda ya kamata ba, a sakamakon haka, ruwa mai yawa ya bace daga koda, shi ya sa Yu ya ji kishirwa, ya sha ruwa da yawa.'

Ko da yake Yu Guanxiong ya sha ruwa da yawa, amma jikinsa bai yi amfani da shi ba, yawancin ruwan da ya sha ya zama fitsari, shi ya sa ko da yake ya sha ruwa da yawa, amma ya kan ji kishirwa kwarai.

To, yanzu mun gane dalilin da ya sa Yu Guangxiong ya sha ruwa da yawa, amma ya ji kishirwa sosai. Abin da ya faru kan jikinsa ya nuna mana cewa, shan ruwa ba yadda ya kamata ba ya kawo wa lafiyar mutum illa. Daga baya mun tabo magana kan ruwa nawa ne ya kamata a sha a ko wace rana don biyan bukatar jikinmu. Binciken da aka yi ya nuna cewa, ya kamata ruwan da a sha ya yi daidai da ruwan da a fitar da shi zuwa waje. Wato ba ma cin abinci kawai ba, har ma muna bukatar shan ruwa misalin milliliter dubu 1 zuwa dubu 2, wato kofi 6 zuwa 8. Amma a lokacin zafi ko bayan motsa jiki sosai, ana bukatar kara sha ruwa.

Mutane masu yawa suna ganin cewa, lokacin da a ji kishirwa, to, ana bukatar shan ruwa. Amma shehun malami Li Qifu ya bayyana cewa, wannan ba daidai ba ne, ya ce, 'kada a sha ruwa a lokacin jin kishirwa. A lokacin nan an yi karancin ruwa sosai a jikin mutum. Shi ya sa, a galibi dai, a kan sha ruwa kullun, kada a sha ruwa a lokacin da a ji kishirwa.'

A sakamakon haka ya kamata mu kan sha ruwa kadan amma sau da yawa. To, za mu gabatar muku wani ajandar shan ruwa ta hanyar kimiyya.

A galibi dai, ya fi kyau a sha ruwa kofi daya bayan a tashi daga barci a wanke fuska da safe, amma kafin a ci abinci. Da karfe 10 da safe a sake shan ruwa kofi daya, bayan abincin rana kofi daya, da karfe 3 da yamma kofi daya, kafin abincin dare kofi daya, a karshe dai kafin a yi barci a sha ruwa kofi daya, ta yadda za a taimakawa kiwon lafiyar mutune.

Ban da wannan kuma, kamata ya yi a sha ruwa a lokacin motsa jiki ta hanyar kimiyya. Mataimakin shehun malami na asibiti na farko na jami'ar ilmin aikin likita ta Chongqing Mr. Zhou Bo ya yi bayanin cewa, 'a zahiri shan ruwa a lokacin motsa jiki yana da muhimmanci. Kowa ya sani cewa, mun yi gumi da yawa a lokacin da muke motsa jiki, mun bace ruwan da ke cikin jikinmu, idan mun sha ruwa a lokacin da muke jin kishirwa, an riga an rasa daidaituwa a cikin jikinmu. Shi ya sa, da karko dai, kafin motsa jiki, mun sha ruwa tukuna, mun shara fage tukuna. Na biyu kuma, tilas ne a sha ruwa kadan amma sau da yawa bayan motsa jiki, kada mun sha ruwa da yawa. Shan ruwa da yawa ya kawo wa lafiyar mutane illa sosai. '

Saboda haka hanyar da ya kamata a bi wajen shan ruwa bayan motsa jiki ita ce, a dauraye kadan a cikin baki, a laimaci baki kadan, daga baya, a sha ruwa kadan, jin kadan kuma, a sake sha kadan. Ko shakka babu, bayan an yi gumi mai yawa, idan a sha ruwan da ke cike da gishiri kadan cikin lokaci, to, za a fi amfanawa kiwon lafiya.

A karshe dai, za mu gabatar muku ruwan da kada a sha. Da farko shi ne ruwan da aka dade ana ajiye a cikin kwalba, na biyu kuma shi ne ruwan da aka sha tafasa a cikin injin tafasa ruwa, na uku shi ne ruwan da aka sake tafasa shi.