Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-22 15:50:29    
Wani film ya jawo hankulan jama'a sosai a kan halakar da aka yi wa muhalli

cri

'The promise' shi wani film ne da shahararren jagora na duniya Chen Kaige ya yi a 'yan kwanakin baya, a lokacin an sami kudin tikiti da yawansu ya kai kudin Sin Yuan miliyan 200 daga wajen film din. Amma a cikin kwanaki da yawa, kafofin watsa labaru na kasar Sin sun kai suka sosai a kan bangaren keren film na 'The promise'. Dalilin da aka yi haka shi ne domin bangaren keren film din sun halaka a kan muhallin halittu na wani tabki mai suna Bigu na lardin Yunnan da ke kudancin kasar Sin a yayin da yake yin film din a kai. Yaya wannan abu yake ? Wa zai kawar da halakar da aka yi wa tabkin Bigu ? Mene ne ra'ayin hukumar gwamnatin kasar Sin a kan haka ? Sai mu ga wani cikakken bayani dangane da haka.

Film na 'The promise' yana da kyawawan hotuna masu yawan gaske. Bisa labari da muka samu, an ce, an dauki hotuna da yawa daga cikinsu ne a wani shahararren yankin yawon shakatawa na tabkin Bigu. Yankin tabkin Bigu yana cikin wani dutse da ke da mita dubu 4, tabkin Bigu yana da ruwa mai haske garau, kuma yana da furanni masu launuka daban daban da itatuwa da ke tofo da kansu da ciyayi masu launin kore.

Amma abin bakin ciki shi ne, bayan da kungiyar keren film na 'The promise' ta isa wurin, halaka ta zo masa. Wakilimmu ya ga abinci da kwalaben giya da leda da rigar maganin ruwa a ko ina a yankin tabkin Bigu. Ban da wannan kuma, kungiyar keren film na 'The promise' ya halaka sauran wurare sosai a cikin yankin.

Wannan ya hadasa fushin mazaunan wurin sosai. kafofin watsa labaru na sauran jama'a su ma sun kai suka a kan kungiyar film din. Wata mazauniyar Beijing Malama Li Hao ta ce, 'idan aka canza muhallin halittu na tabkin Bigu, to, ba za a iya mayar da wurin da ya zama yadda yake a da ba. Abin fushi shi ne, kungiyar keren film ta yi amfani da muhallin halittu bisa ra'ayinta kawai ba tare da yin la'akari a kan sauran jama'a ba, wannan abin son kai ne.'

Ban da kungiyar keren film na 'The promise', akwai kungiyoyi da yawa suka halakar wuraren yawon shakatawa da yawa, game da haka, musamman halakar da aka yi wa tabkin Bigu, mataimakin shugaban kafa dokoki na babbar hukumar kare muhalli ta kasar Sin Bie Tao ya bayyana wa wakilimmu cewa, 'wannan abu ya sa na yi tunani sosai. Game da hukumomin kare muhalli, kamata ya yi mu dauki nauyin da ke bisa wuyanmu cikin yakini kuma kafin aukuwar halakar da aka yi wa wuraren yawon shakatawa. Game da kungiyoyin da ke keren film, ya kamata su kara mai da hankali a kan kare muhalli. A matsayin hukumar kare muhalli ta kasar Sin, ya kamata mu kafa wasu dokoki domin hana aukuwar halakar da aka yi wa wuraren yawon shakatawa.'

A halin yanzu dai, jami'u da kwararrun babbar hukumar kare muhalli ta kasar Sin da na hukumar kare muhalli ta lardin Yunnan sun riga sun yi bincike a yankin tabkin Bigu domin yin kimantawa a kan halakar da aka kai wa yankin.

A sa'i daya kuma, mataimakin ministan gine-gine na kasar Sin Qiu Baoxing ya kai suka a kan kungiyar keren film na 'The promise', ya ce, 'idan mu ga wata kungiyar keren film ba ta bi babban tsari na wuraren yawon shakatawa ba, za mu kai suka gare su, za su dauki matakai a kan haka domin kada wuraren yawon shakatawa da suke da ma'anar tarihi da al'adu su lalata a cikin hannumu.'

Bisa labarin da muka samu, an ce, a halin yanzu dai, ana gyare yankin tabkin Bigu domin mayar da shi a matsayin yadda yake a da. Amma wasu kwararru da abin ya shafa sun yi hasashen cewa, idan ana son sake ganin kyawawan wuraren yawon shakatawa a yankin tabkin Bigu kamar a da, to, wannan ya bukaci lokaci na shekaru daga 3 zuwa 5.(Danladi)