Assalamu alaikum, jama'a masu karatu, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Bunkasuwar kasar Sin. Kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da wani babban shirin raya kauyuka. Bisa wannan shiri, gwamnatin kasar Sin za ta dauki matakai iri iri, ciki har da matakin samar wa amfanin gona kudin rangwame da na rage harajin da ake buga wa aikin gona da manoma da kuma matakin kara gina wasu ayyukan yau da kullum a kauyuka wadanda suke fama da talauci domin raya su da su zama sabbin kauyuka masu arziki inda ke cike da dimokuradiyya da wayin kai. A cikin shirinmu na yau, za mu bayyana muku wannan filla filla.
Lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin, lardi ne dake raya aikin gona sosai. Mutane masu dimbin yawa na wannan lardi suna yin aikin gona. A wani kauyen da ake kiransa Qiaodi a lardin Guizhou, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, domin manoma su iya samun kudi kadan, kuma ba su da ingantaccen ayyukan yau da kullum, manoman da ke da zama a kauyen ba su ji dadin zamansu sosai ba. Zhang Deming, wani manomi ne na wannan kauye, ya gaya wa wakilinmu cewa, "A shekara ta 2000, kauyenmu ba shi da kyau. Idan an yi ruwan sama, shi ke nan, sai mu sha wahala sossai. Amma samari da yawa suna nan suna da zama a kauyen. Ba su farin ciki ga muhallin da muke ciki ba. Mu kan son kyautata muhallinmu, amma ba mu da karfin yin haka. Daga baya, a karkashin jagorancin gwamnati, mun tsara shirin neman arziki."
Domin yawancin mutanen kasar Sin manoma ne. Maganar yadda za a raya kauyuka za ta yi tasiri sosai ga halin zaman karkon kasar da ake ciki da bunkasuwar tattalin arzikin kasar. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin kasar Sin tana kokarin daidaita wannan magana a kullum. Bi da bi ne ta bayar da jerin matakan nuna goyon bayan raya kauyuka. Alal misali, ta samar wa manoma kudin rangwame kai tsaye da soke harajin da aka buga wa aikin gona da dai makamatansu. Da gaske ne wadannan matakai sun bayar da gudummawa sosai wajen sa kaimi ga manoma da su yi aikin gona d kara kudin shiga da manoma suke samu. Amma a sa'i daya kuma, biranen kasar Sin sun fi samun saurin neman bunkasuwa. Bambancin da ke kasancewa a tsakanin kauyuka da birane yana karuwa.
Mr. Chen Xiwen, mataimakin direktan ofishin rukunin ba da jagora kan harkokin kasafin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiya na kasar Sin, ya ce, "Yanzu, bambancin da ke kasancewa a tsakanin birane da kauyuka yana ta samun karuwa. A shekarar bara, kudin shiga da kowane manomi ya samu ya kai kudin Sin Renminbi yuan 3255, amma kudin da kowane mazaunan birni zai iya kashewa ya kai kudin Renminbi yuan dubu 1 da 493. Bambancin da ke kasancewa a tsakaninsu ya kai kudin Sin Renminbi yaun 7238. Bugu da kari kuma, yanzu manoma ba su iya jin dadin ayyukan da ake yi domin jama'a, alal misali a fannonin ba da ilmi da kiwon lafiya da al'adu iri iri da gwamnatocin suka gabatar kamar yadda mazaunan birane suke jin dadinsu ba. Wannan bambanci ma yana kasancewa a cikin hali mai tsanani."
Domin ana son kawar da matsalolin da suke kasancewa a kauyuka kwata kwata, bayan da aka yi nazari da gwaje-gwaje sosai a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta bayar da manufar raya sabbin kauyuka. Bisa wannan manufar, a cikin shekaru gomai masu zuwa, kasar Sin za ta zuba jari mai yawan gaske a kauyuka domin gyara fuskokin ayyukan yau da kullum iri iri a kauyuka. Manoma ma za su iya jin dadin sakamakon bunkasuwar tattalin arziki da zaman rayuwar kamar yadda mazaunan birane suke ji.
Yau da wasu shekarun da suka wuce ne, aka riga aka fara gwajin aiwatar da wannan manufa a kauyen Qiaodi da muka ambata a gaba. Gwamnatin wurin ta zuba kudaden Renminbi yuan dubu darurruka a kauyuka a fannonin shimfida hanyoyin moat da gidaje da dakin kiwon lafiya da ayyukan al'adu yayin da ta samar wa manoman kauyen kudin rangwame domin sa musu kaimi kan noman amfanin gona da za a iya samar da su.
Bayan da aka gina da kyautata ayyukan yau da kullum, yanzu, kauyen Qiaodi ya riga ya zama wani sabon kauye mai arziki, inda ke da ingantaccen ayyukan yau da kullum.
Lokacin da take tabo sauye-sauyen da suka faru a kauyen, madam Li Fumei, wata manomar kauyen ta ce, "A da, mu kan kona katako domin dafa abinci. Amma yanzu muna yin amfani da man gas iri iri loakcin da muke dafa abinci."
Ba ma kawai sharudan zamantakewar jama'ar kauyen Qiaodi sun samu kyautatuwa ba, har ma manoman kauyen Qiaodi sun fara bin al'adun wayin kai. A da, ya kasance da barayi da yawa a kauyen, amma yanzu, babu barawo ko daya a cikin kauyen. A cikin shekaru 4 da suka wuce, babu aukuwar matsalolin kanana da manyan laifuffuka a kauyen.
Mr. Chen Xiwen ya bayyana cewa, bayan da kasar Sin ta samu bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri sosai a cikin shekaru fiye da 20 da suka wuce, yanzu kasar Sin tana da kwarya-kwaryan karfin zuba kudade a kauyuka da aikin gona. A sa'i daya kuma, manufar ray sabbin kauyuka a kasar Sin za ta bayar da gudummawa sosai wajen kyautata karfin sayen kayayyaki na manoma miliyan dari 9. A sakamakon haka, za a iya kara raya kasuwanni cikin gida na kasar Sin. Wannan kuma zai bayar da gudummawa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a nan gaba. (Sanusi Chen)
|