Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-19 15:42:24    
Wu Bangguo yana fatan dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kawancen kasashen Turai za ta kara samu bunkasuwa

cri
Jama'a masu karatu, yanzu ga shirinmu na "Mu leka kasar Sin"; A ran l8 ga watan nan da muke, Mr.Wu Bangguo shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin dake yin ziyara a kasar Romaniya ya yi wani jawabi mai lakabi haka "kara karfin zumuncin al'adar dake tsakanin kasashe biyu da neman samu bunkasuwa tare. A cikin nasa jawabi, ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan kasar Romaniya da ta shiga kawancen kasashen Turai, kuma mun yi imani cewa, bayan da kasar Romaniya ta shiga kawancen kasashen Turai sai za ta kara kawo babban karfi ga kawancen kasashen Turai.

Yanzu ga abubuwan da wakilin musamman na rediyon kasar Sin ya rubuto mana filla filla; Kasar Romaniya ta zama tasha ta farko da Mr.Wu Bangguo yake yin ziyara a kasashe hudu na kawancen kasashen Turai, Kuma bayan rabin shekara mai zuwa, wannan tsohuwar aminiyar kasar Sin mai tsawon shekaru fiye da 50 da suka shige za ta zama mamba ta kawancen kasashen Turai, A cikin wannan jawabin da Mr.Wu Bangguo ya yi ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kokarin da gwamnatin kasar Romaniya da jama'arta ke yi don neman shiga kawancen kasashen Turai, Kuma mun yi imani cewa, bayan da kasar Romaniya ta shiga kawancen kasashen Turai, za ta iya kawo babban karfi ga ci gaban kawancen kasashen Turai.Kana kuma za ta iya kawo sabuwar dama ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kawancen kasashen Turai.

Bayan da aka kafa kawancen kasashen Turai, sai sau biyu an yi masa habakawa, yanzu yawan kasashe mambobi na kawancen nan sun kai 25. Kuma a ran daya ga watan Janairu na shekara ta 2007, kawancen kasashen Turai zai kara karba kasashe mambobi guda biyu a cikinsa. A cikin nasa jawabi, bisa madadin gwamnatin kasar Sin ne Mr.Wu Bangguo ya bayyana babban goyon baya da kasar Sin take nunawa har kullum ga aikin neman dayantaccen kawancen kasashen Turai. Ya kuma cekasar Sin tana goyon bayan aikin neman dayantaccen kawancen kasashen Turai, kuma tana son kawancen kasashen Turai zai iya kara ba da babban amfaninsa cikin harkokin shiyya shiyya da na duk duniya.

Kawancen kasashen Turai shi ne rukunin kasashe masu arziki mafi girma a duk duniya, kuma kasar Sin ita ce kasa mai tasowa mafi girma a duniya. Koda yake an kasance da banbancin tarihi da na al'adu da na tsarin siyasa,amma, bayan da aka kafa huldar diplomasiya tsakanin sassa biyu har cikin shekaru fiye da 30 da suka shige, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kawancen kasashen Turai yana ta samu bunkasuwa cikin zama mai dorewa, har an sa sassa biyu sun kara samu babbar moriya iri daya.

Mr.Wu Banggou ya ci gaba da cewahakikanin abubuwa na bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kawancen kasashen Turai sun bayyana cewa, muddin mu tsaya kan ka'idoji 5 na yin zaman tare cikin lumana, da kara habaka sassan neman moriyar juna, daidaita sabanin dake tsakanin sassa biyu cikin lumana, sai kasashe masu bambancin tsarin zaman al'umma su iya kara karfin yin aikatayya tare da kara naman bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashe daban daban.

Ya ci gaba da cewa, har kullun ne kasar Sin ta mai da dangantakar dake tsakaninta da kawancen kasashen Turai a kan muhimmin matsayi na harkokin wajenta. A wannan rana, akwai 'yan majalisa da dalibai wajen 600 na kasar Romaniya sun saurari jawabin da Mr.Wu Bangguo ya yi.(Dije)