Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-18 19:55:43    
Tarihin aikin watsa labaru da harshen Hausa na kasar Sin

cri

Jama'a masu sauraro, yanzu lokaci ya yi da za mu amsa tambayoyin masu sauraro. Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Abubakar Ali daga Galim-Tingnere Adamaoua na kasar Kamaru. A cikin wasikar da ya rubuto mana, ya ce, ina mai tambayarku cewa, shin a wace shekara ce Sin ta fara ba da labaru ta muryar Hausa? Hasali ma dai, bayan malam Ali Abubakar, masu sauraronmu masu yawa ma sun taba yi mana irin wannan tambaya. Sabo da haka, a cikin shirinmu na yau, bari mu kawo muku dan bayani a kan tarihin kasar Sin a wajen watsa labaru da muryar Hausa.

Masu sauraro, an kafa gidan rediyon kasar Sin ne a ran 3 ga watan Disamba na shekara ta 1941, wanda kuma shi ne gidan rediyo kadai da ke gabatar da shirye-shirye zuwa wurare daban daban na duk duniya a nan kasar Sin. A halin yanzu dai, yana watsa shirye-shiryensa cikin harsunan waje 38 da amintaccen Sinanci da kuma karin harshen Sinanci 4, kuma harshen Hausa yana daya daga cikinsu.

An fara shirin kafa sashen Hausa a nan gidan rediyon kasar Sin ne daga karshen shekara ta 1960. A watan Janairu na shekara ta 1961, sashen Hausa ya gayyato wani masanin harshen Hausa daga kasar Nijer don ya koya wa wasu daliban kasar Sin wadanda suke jin Faransanci Hausa ta hanyar Faransanci. Bayan da masanin ya koma gida kuma, an sake gayyato wani masanin harshen Hausa mai suna Amada daga Nijer, wanda kuma shahararren mai watsa labaru ne na gidan rediyon birnin Yamai. Bisa taimakonsa, ma'aikatan kasar Sin sun fara iya Hausa sannu a hankali. A karshen shekara ta 1962, sashen Hausa ya fara watsa labaru. Bisa kokarin da aka shafe watanni da dama ana yi, daga karshe dai, a ran 1 ga watan Yuni na shekara ta 1963, sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin ya fara watsa labarunsa a hukunce.

A halin yanzu dai, akwai ma'aikatan kasar Sin 14 a nan sashen Hausa na rediyon kasar Sin, kuma akasarinsu sun taba zuwa jami'ar ABU ko jami'ar Bayero ta kasar Nijeriya don zurfafa ilminsu na harshen Hausa. Bayan haka kuma, muna da masanan harshen Hausa guda biyu wadanda suka zo daga kasar Nijeriya, wato malam Balarabe Shehu Ilelah da kuma matarsa Lubabatu Shehu Ilelah. Sa'an nan kuma, a shekara ta 1995, an kafa tashar manema labaru ta gidan rediyon kasar Sin a birnin Lagos na kasar Nijeriya, a cikin tashar, akwai kuma wani wakili na sashen Hausa.

A halin yanzu dai, sashen Hausa na rediyon kasar Sin yana watsa shirye-shiryensa har sau 7 a kowace rana zuwa yankunan Hausa na yammacin Afirka. Wato shirinmu na farko wanda ya kan zo muku daga karfe 5 da rabi zuwa karfe 6 da rabi na yamma, agogon wurin, wanda kuma mu kan maimaita shi daga karfe 6 da rabi zuwa karfe 7 da rabi na yamma. Sa'an nan kuma, mu kan watsa muku shirinmu na biyu daga karfe 7 zuwa karfe 7 da rabi, agogon wurin, da kuma shirinmu na uku daga karfe 9 zuwa karfe 10 na safe. Bayan haka kuma, daga watan Mayu na shekara ta 2002, sashen Hausa ta fara watsa shirye-shiryensa har sau biyu a ko wace shekara a kasashen Afirka kai tsaye. A nan kuma, muna farin ciki matuka da gaya muku cewa, tun daga ran 10 ga watan Afril na wannan shekara, daga karfe 1 zuwa karfe biyu na yamma na ko wace rana, sashenmu ya kuma fara watsa shirye shirye ta gidan rediyon R&M na birnin Yamai na kasar Nijer, wato a kan FM104.5MHz. Lalle ne, ya zuwa yanzu, tsawon shirye-shiryenmu da sashen Hausa ke watsa muku a ko wace rana ya riga ya kai mintoci 390. A ko wace rana, sashen Hausa na rediyon kasar Sin yana watsa wa masu sauraronsa muhimman labarun kasar Sin da na sauran kasashen duniya wadanda ke da dumiduminsu, musamman ma na kasashen Afirka. Bayan labaru, ya kan kuma gabatar musu da bayanin musamma dangane da labarin da ya fi muhimmanci a wannan rana, don yin bayani sosai a kan labarin. Ban da wannan kuma, sashen Hausa yana gabatar wa masu sauraronsa da shirye-shirye masu kayatarwa, kamar su 'me ka sani game da kasar Sin' da 'Sin da Afirka' da 'musulmai na kasar Sin' da 'amshoshin wasikunku' da 'zabi sonka' da 'koyon Sinanci' da dai sauransu, wadannan shirye-shirye sun sami karbuwa sosai a tsakanin masu sauraro sabo da halayensu na ilmantarwa da sakin jiki da kuma mu'amala. Bisa bunkasuwar fasahohin internet kuma, sashen Hausa ya kuma yi kokarin yi amfani da wannan fasaha mai ci gaba, kuma ya kafa tasharsa ta internet a shekara ta 2003, wato www.cri.com.cn, inda idan masu sauraro suka kama, to, za su iya karanta labaru masu yawa, haka kuma suna iya sauraron sabbin shirye-shiryen sashen Hausa a tashar a ko da yaushe.

Bunkasuwar sashen Hausa ba ya iya rabuwa da goyon baya da masu sauraronmu suka ba mu, a ko wace shekara, sashen Hausa ya kan samu wasiku masu dimbin yawa daga masu sauraro. A shekarar bara kurum, ya sami wasikun da yawansu ya zarce dubu 13. A sabo da haka kuma, ya kulla zumunta da aminan Afirka masu yawa, a sa'i daya kuma, ra'ayoyi da shawarwari da aminansa na Afirka suka ba shi a cikin wasikunsu ma sun taimaka masa kwarai wajen kara kyautata shirye-shiryensa. Sabo da haka, a nan ma, a madadin dukan ma'aikatan sashen Hausa na rediyon kasar Sin, ina so in yi wa masu sauraronmu godiya. Kuma muna fatan za ku ci gaba da rubuto mana wasiku ko Email, don taimaka mana a wajen kara kyautata shirye-shiryenmu.

To, masu sauraro, wannan shi ya kawo karshen shirinmu na yau, da haka, ni Lubabatu daga nan Beijing ke ce muku, sai mako mai zuwa, ku huta lafiya.(Lubabatu Lei)