"Tsarin ka'idoji na shiri na 11 na shekaru 5 na raya tattalin arzikin kasa da zaman al'umma" na kasar Sin ya gabatar da cewa, bisa sharadin kafa tsarin tattalin arziki na kasuwannin gurguzu, ya kamata a dogara bisa babban gudummawar da aka bayar wajen albarkatun kasuwanni domin tabbatar da makasudi da aikin wannan tsari. Sa'an nan kuma ya kamata gwamnatin kasa ta aiwatar da hakkinta bisa gaskiya, da sa ido kan albarkatun zaman al'umma, da rarraba al'barkatun jama'a yadda ya kamata, ta yadda za a tabbatar da aiwatar da tsari lami lafiya.
"Tsarin ka'idojin" ya nemi da a kafa tsarin aiwatar shi ta hanyar yin jagoranci ta hanyoyi daban-daban, za a tafiyar da harkokin muhimman fannonin samun bunkasuwa ciki har da aikin gona da masana'antu da sana'ar yin hidima, da yin amfani da jarin waje da yin cinikin waje ta hanyar dogara bisa kasuwanni, ya kamata gwamnatoci na matakai daban-daban su kiyaye gasar da ake yi cikin adalci, kada su sa kafa cikin harkokin kasuwanni.
Tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki da sauri kuma cikin zama mai dorewa, da bunkasa sabbin kauyukan gurguzu da sa kaimi ga bunkasa birane lami lafiya da sauran ayyukan da aka tsayar cikin tsarin, za a yi kokarin aiwatar da su ne musamman ta hanyar kyautata tsarin kasuwanni, ya kamata gwamnatin kasar ta tsai da kyawawan tsare-tsare da manufofi ta hanyar kirkirar tsarin da kyautata manufa. Ba da ilmin tilas da kiwon lafiyar jama'a da samun tabbacin zaman al'umma da sa kaimi ga samun aikin yi da yin binciken kimiyya da fasaha da sauran ayyukan yin hidimar jama'a da aka tsayar cikin tsarin dukkansu alkawuran gwamnati ne, ya kamata gwamnatoci na matakai daban-daban su aiwatar da hakkokinsu cikin nitsuwa, kuma su matukar kokari don kammala wadannan ayyuka ta hanyar yin amfani da albarkatun jama'a.
Kiyaye muhallin halittu da ikon mallakar fasaha, da daidaita batun rarraba kudin shiga da kiyaye tsarin tattalin arziki na kasuwanni da tabbatar da ikon halal na jama'a da sauran bukatun jama'a da aka tsayar cikin tsarin za a tabbatar da su ne ta hanyar kyautatawa da yin kokarin tafiyar da dokokin shari'a, kuma ta hanyar tattalin arziki. Aikin yin gyare-gyare da aka tsayar cikin tsarin wani muhimmin aiki ne na gwamnatin kasar, dole ne a mai da shi bisa muhimmin matsayi cikin ayyukan gwamnati, kuma za a tafiyar da wannan aiki ta hanyar hadin gwiwa tsakanin sassan da abin ya shafa, kuma a ciyar da aikin gaba ba tare da bata lokaci ba.
"Tsarin ka'idojin" ya jaddada magana kan daidaita da kuma kyautata manufofin tattalin arziki, da rarraba ayyuka da hakkokin kashe kudi ga gwamnatoci na matakai daban-daban yadda ya kamata. Fannonin da suka samu fiffiko wajen yin kasafin kudin jama'a su ne, ba da ilmin tilas a kauyuka da kiwon lafiyar jama'a, da yin amfani da kimiyya da fasaha wajen aikin gona, da sa kaimi ga samun aikin yi da samun tabbacin zaman al'umma, da yin fama da talauci da tsarin rage yawan haihuwa, da yin rigakafi da kuma kau da bala'u da yin binciken fasaha domin samun moriyar jama'a, da kiyaye muhallin halittu da albarkatun kasa.
"Tsarin ka'idojin" ya nemi da a kyautata tsarin aiwatar da shiri, da kara samun daidaituwa daga duk fannoni. Ya kamata a himmantar da dukkan larduna da jihohi masu tafiyar da harkokin kansu da kuma biranen da ke karkashin gwamnatin tsakiya domin tafiyar da ayyukan da aka tsayar cikin tsari.(Umaru)
|