Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-18 12:07:39    
Yin aiki da kyau wajen riga-kafin aukuwar Tsunami

cri

' An sanar da, cewa an yi girgizar kasa mai tsanani a kasar Chile. Girgizar kasa tana da awo takwas da digo biyu a ma'aunin Ritcher'. Jiya da safe misali karfe l0 da minti 37, Cibiyar kula da tarzoma ta kasar New Zealand ta samu wannan rahoto na gaggawa daga daraktan mai kula da harkokin yin gargadin farko kafin aukuwar Tsunami.

Da misalin karfe l0 da minti 41, Cibiyar kula da tarzoma ta kasar New Zealand ta ba da oda nan da nan ga Cibiyar ceto cikin gaggawa ta gwamnatin kasar, da sassan tsaro na jama'a, da hukumomin jiyya da abun ya shafa da kuma hukumomin gwamnatocin birane daban daban don su yi aiki sosai wajen fuskantar aukuwar Tsunami ba zato ba tsammani.

Wannan dai wani gwaji ne da sassa goma sha shida da abun ya shafa na kasar New Zealand suka yi jiya da safe a Cibiyar kula da tarzoma ta wannan kasa a karkashin babban ginin majalisar dokokin kasar.

Wannan gwaji, wani kashi ne dake cikin gwaje-gwajen yin gargadin farko ga aukuwar bala'in Tsunami da ake yi cikin hadin gwiwa a kewayen tekun Pacific, wandanda aka lakaba musu sunan " Babbar Guguwa ta tekun Pacific a shekarar 2006". Kasashe da jihohi guda ashirin da takwas sun shiga gwaje-gwajen. Lallai ba a manta ba, an samu bala'in Tsunami a tekun India a karshen shekarar 2004, wanda ya girgiza duk duniya. Sakamakon haka, kasashe daban daban sun ba da shawara bi da bi don kafa tsarin yin gargadin farko ga aukuwar bala'in Tsunami. Makasudin gwajin da aka yi a wannan gami a kasar New Zealand, shi ne auna da kuma jarraba tsarin yin gargadin farko ga yanayin Tsunami a karo na farko kuma bisa babban mataki tare da yin hadin gwiwa a kewayen tekun Pacific.

Bisa shirin gwajin, Cibiyar kula da gargadin farko ga aukuwar bala'in Tsunami ta Hawaii ta ba da gargadi da farko; daga baya dai an watsa rahoton gargadi ba tare da bata lokaci ba ga sassan kula da harkokin gaggawa na kasashen da abun ya shafa.To, duk kasashen da suka samu wannan rahoto wajibi ne a wannan rana ko kashegarin su sanar da rahoton yin gargadin gaggawa ga cibiyoyin mayar da martani kan harkokin gaggawa na wurare daban daban.

Mr. John Noton, jami'in zartarwa na farko na Cibiyar kula da tarzoma ta kasar New Zealand ya furta, gwajin da aka yi a wannan gami , wata kyakkyawar dama ce ga kasar New Zealand wajen dudduba tsarin fuskantar aukuwar bala'in Tsunami cikin gaggawa Sassan da abun ya shafa za su iya gyara abubuwan da ba su bace ba; A sa'I daya kuma yana fatan ta wannan dama a ja kunnen jama'ar kasar don tsaya kan baka wajen yaki da bala'in Tsunami.

An kashe awa biyar da ' yan kai ana yin gwajin. Bayan awa biyu da aukuwar bala'in Tsunami, sai aka kira hadadden taro tsakanin manyan jami'an gwamnatin kasar kan yadda za a yi kwaskwarimar shirin gargadin farko ga aukuwar bala'in Tsunami; Ban da wannan kuma, kafofin yada labarai daban daban sun rika watsa labaran da shafi bala'in Tsunami ga jama'ar kasar don su shiga matakin da aka dauka a fadin duk kasa na yaki da bala'in.

Bayan da aka kammala gwajin, sai Mr. Noton ya jaddada, cewa ko ta yaya mutane ba za su saki jiki ba; Wajibi ne su tuna da wurin da za su tsira kafin su shiga barci. ( Sani Wang )