Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na APA ya bayar a ran 16 ga wata, an ce, kasashe uku wato Faransa da Britaniya da Jamus, wadanda suke yin shawarwari da kasar Iran a madadin kungiyar EU, suna shirin bayar wata kunamar sarrafa nukiliya na 'Light-water' ga kasar Iran, domin kasar Iran ta daina ayyukan tace sinadarin Uranium da ake da bambancin ra'ayi a kai. Game da haka, kasar Amurka ba ta ce kome ba a ran nan.
An ce, bisa wani sashe na shirin da kungiyar EU take yi wa kasar Iran a jere, kungiyar tana son sayar da wata kunamar sarrafa nukiliya na zamani, haka kuma ta yi alkawarin cewa, za ta bayar da taimakon da abin ya shafa ga kasar Iran. Kungiyar EU ta yi haka ne domin sa kaimi ga kasar Iran da ta daina ayyukan tace sinadarin Uranium da hana kasar Iran ta kafa kunamar sarrafa nukiliya na 'heavy-water'.(Danladi)
|