Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-17 09:38:00    
Wassu labaru game da wasannin motsa jiki (11/5-17/5)

cri
A ran 13 ga watan nan, an yi bikin bude makon harkar yin magana da harsunan waje ta mazauna birnin Beijing a shekarar 2006 a lambun shan iska na Chao Yang na Beijing. Domin neman samun nasarar shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics a shekarar 2008, har kullum gwamnatin birnin Beijing takan shawo kan dimbin mazauna birnin don su koyi harsunan waje da kuma yin amfani da su musamman ma harshen Turanci. Makasudin shirya wannan harka, shi ne domin himmantar da mazauna birnin Beijing wajen koyon harsunan waje tare da nuna sha'awarsu a kai. Mazauna birnin a kalla 50,000 sun halarci bikin bude wannan makon harkar yin magana da harsunan waje;

A gasa ta rana ta karshe ta wasan tsunduma cikin ruwa ta samun babbar kyauta da hadaddiyar kungiyar iyo ta duniya ta shirya a ran 14 ga watan nan a Fort Lauderdale ta kasar Amurka, ' yan wasa na kasar Sin sun samu lambobin zinariya guda uku a gun wasan daka tsalle cikin ruwa daga kan dakali tsakanin namiji dai dai da na maza biyu-biyu da kuma wasan tsunduma cikin ruwa daga kan katako mai tsayin mita 3 tsakanin mace da mace. Sakamakon haka, ' yan wasan kasar Sin sun zama zakaru a dukkan gasar da aka yi a wannan gami.

An yi gasar cin kofin duniya ta wasan harbe-harbe a shekarar 2006 daga ran 4 zuwa ran 12 ga watan nan a birnin Kerrville na kasar Amurka. 'Yar wasa mai suna Zhu Mai ta kasar Sin ta samu lambar zinariya a wasan jefa faranti wato discus tsakanin mata zalla.

A gun budaddiyar gasa ta wasan kwallon tenis da aka yi a ran 14 ga watan nan a birnin Berlin na jamus, ' Yan wasa mata wato Zhenjie da Yanzi na kasar Sin sun zama lambawan a gun wannan wasa da aka yi tsakanin mata bibbiyu.

Za a yi taron wasannin motsa jiki na 6 na yanayin sanyi na Asiya tun daga ran 28 ga watan Janairu zuwa ran 4 ga watan Fabrairu na shekarar 2007 a birnin Changchun dake arewacin kasar Sin.

An kawo karshen gasar cin kofin duniya ta wasan daga nauyi ta nakasassu a shekarar 2006, wadda aka shafe mako daya ana yinta a birnin Busan dake kudu maso gabashin kasar Korea ta Kudu. ' Yan wasa na kasar Sin sun yi fintinkau wajen samun lambobin yabo a gun gasar.

A gun gasar samun kyaututtuka ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle da aka yi ran 12 ga watan nan a Doha, dan wasa mai suna Justin Gatlin daga kasar Amurka ya karya matsayin bajinta na duniya a wasan gudu na tsawon mita 100 na maza da dakika 9 da digo 76 maimakon dakika 9 da digo 77 da dan wasa mai suna Asafa Powell na kasar Jamaica ya kirkiro a watan Yuni na shekarar bara a kasar Girka.( Sani Wang )