
An shirya taron ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar hadin kai na Shanghai a ran 15 ga wata a birnin Shanghai na kasar Sin. Ministocin harkokin waje na kasashe 6 da suka hada da Sin da Rasha da Kazakhstan da Krkistan da Tajikista da kuma Uzbekistan sun yi tattaunawa a kan aikin share fage domin taron koli na kungiyar hadin kai ta Shanghai da za a shirya a wata mai zuwa a birnin Shanghai. A gun taron manema labaru da aka shirya bayan taron, ministocin kasashen nan 6 gaba daya sun bayyana cewa, an gudanar da taron nan bisa halin da ake ciki, kuma an sami sakamako mai kyau.
Kasashen Sin da Rasha da Kazakhstan da Kirgistan da Tajikista da kuma Uzbekistan sun shelanta kafa kungiyar hadin kai ta Shanghai a ran 15 ga watan Yuni na shekarar 2001 a birnin Shanghai na kasar Sin. Kungiyar nan kuma wata dauwamammiyar kungiyar kasa da kasa ce da aka kafa tsakanin gwamnatoci. Shekarar nan zagayowar shekaru 5 ce da aka kafa ta. Kungiyar kuma za ta shirya taron shugabannin kasashen nan 6 a birnin Shanghai a tsakiyar watan Yuni. An shirya taron ministocin harkokin waje a wannan gami ne duk domin share fage ga taron shugabannin nan da za a yi. Bayan taron, Mr Li Zhaoxing, ministan harkokin waje na kasar Sin ya bayyana wa manema cewa, "taron ya yanke shawara a kan kara yin tattaunawa a tsakaninsu, da karfafa hadin guiwarsu don tabbatar da nasara ga taron kolin da za a yi, musamman ma ga hadin guiwar da ake yi. Mun yi binciken halin da kungiyar hadin kai ta Shanghai take ciki a yanzu, muna ganin cewa, ya kamata, mu ci gaba da inganta hadin guiwa da amince wa da juna da kuma kara karfin hadin guiwa wajen murkushe 'yan a-ware da 'yan ta'adda da masu tsatsauran ra'ayi don kare zaman lafiya, mu hada guiwarmu a fannin tattalin arziki, ta yadda kungiyarmu za ta kara taka muhimmiyar rawa wajen kare zaman lafiya da zaman karko da samun bunkasuwa a yankinmu."
1 2
|