Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-15 16:41:53    
Har wa yau tsirarrun dakaru masu yin adawa da gwamnati na Darfur sun nuna kin yardarsu ga sa hannu kan yarjejeniyar neman zaman lafiya

cri

An ce, a ran l4 ga watan nan da muke ciki, Mr.Al-Nur shugaba na wani rukunin rundunar sojan neman 'yancin Sudan mai yin adawa da gwamnati na Darfur na kasar Sudan ya sake nuna kin yardarsa ga rokon kawancen kasashen Afrika wajen sa hannu kan yarjejeniyar shimfida zaman lafiya. Ta haka ne har wa yau aikin shimfida zaman lafiya na kasar Sudan yana cikin halin wuya.

A farkon watan Mayu na shekarar nan da muke ciki, bisa kokarin da kasashen duniya suka yi, a birnin Abuja, hedkwatar kasar Nigeria, wani babban rukunin dakaru na neman "yancin kasar Sudan tare da gwamnatin kasar Sudan sun kulla wata yarjejeniyar shimfida zaman lafiya kan matsalar Darfur, amma wani karamin rukunin dakaru na neman "yancin kasar Sudan dake karkashin Mr.Al-Nur ya nuna kin yarda ga sa hannu kan wannan yarjejeniyar shimfida zaman lafiya kan matsalar Darfur.

Bayan haka, koda yake kasashen duniya sun yi ayyuka da yawa sau da yawa ne jami'ai na kawancen kasashen Afrika da manzon musamman na majalisar dinkin duniya sun shiga da fita daga wurin Darfur, kuma sun yi ta roki wannan karamin rukunin dakaru da ya bi hanyar adalci, amma a karshe dai ba a sami wani sakamako ba.

Masana suna gani cewa, dalilin da ya sa yarjejeniyar neman zaman lafiya ta Abuja ta gamu da wannan babbar wahala domin an kasance da babban sabanin dake cikin rukunin dakaru masu yin adawa da gwamnatin kasar Sudan. Kuma babban rukunin dakaru masu yin adawa da gwamnati da na wani karamin rukuni sun yi jayayya don neman samu ikon shugabanci, ta haka da wuya ne za a iya kai ga samu ra'ayi daya. A cikin wannan gami, babban rukunin dakaru mau yin adawa da gwamnati dake karkashin shugabancin Mr.Minnawi, amma wani karmin rukunin dake karkashin Mr.Al-Nur ya janye jikinsa daga shawarwari, kuma ya nuna kin yarda ga sa hannu kan yarjejeniyar neman zaman lafiya.

Mr.Al-Nur ya taba bayyana cewa, shi zai iya sa hannu kan wannan yarjejeniyar neman shimfida zaman lafiya amma akwai sharadan da ya kamata gwamnatin Sudan za ta biya masa. Amma, gwamnatin kasar Sudan ba ta yi rangwame ga sharudan da Mr.Al-Nur ya gabatar ba, domin idan gwamnatin kasar Sudan za ta biya bukatun da Mr.Al-Nur ya gabatar sai zai iya jawo adawa daga shugaban babban rukunin dakaru masu yin adawa da gwamnatin kasar Sudan, kuma mai iyuwa ne Mr.Minnawi zai iya janye jikinsa daga wannan yarjejeniyar shimfida zaman lafiya ta kasar Sudan.

A ran l5 ga watan nan da muke ciki, a kasar Habasha, kawancen kasashen Afrika da majalisar ministocin neman zaman lafiya za su yi taro. Kafin wannan, sashen yin sulhuntawa na duniya ya yi kokari mai da wannan lokaci da ya zama jadawali na karshe, domin neman karamin rukunin dakaru masu yin adawa da gwamnatin kasar Sudan da ya sa hannu kan yarjejeniyar shimfida zaman lafiya ta Abuja. Amma, daga halin da ake ciki da wuya ne za a iya tabbatar da wannan buri. Koda yake an yi haka,amma kasashen duniya da kawancen kasashen Afrika da majalisar dinkin duniya suna nan suna ci gaba da yin kokarinsu. (Dije)