Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-12 17:42:05    
Bangarori 2 da ke tsakanin gabobin mashigin tekun Taiwan suna hada kansu wajen fuskantar bunkasuwar tattalin arziki bai daya a duniya

cri

A ran 15 ga watan Afrilu an rufe taron fadin albarkacin bakinka kan tattalin arziki da cinikayya a tsakanin bangarori 2 na mashigin tekun Taiwan da ya shafi kwanaki 2 ana yinsa a nan birnin Beijing. A gun taron, wakilai sun tattauna kan batutuwa iri iri. Alal misali, yadda musanye-musanyen tattalin arziki da cinikayya a tsakanin gabobin 2 za su yi tasiri ga tattalin arzikin gabobin 2 da hadin guiwar aikin gona da yin zirga-zirga a tsakaninsu kai tsaye da harkar yawon shakatawa da sha'anin kudi. Sannan kuma, a gun taron, bangaren babban yankin kasar Sin ya bayar da manufof masu gatanci guda 15 ga 'yan uwanmu na Taiwan. Wakilai wadanda suka halarci taron sun bayyana cewa, lokacin da ake bunkasa tattalin arziki bai daya a duniya, ya kamata gabobi 2 da ke tsakanin mashigin tekun Taiwan su kara yin hadin guiwa irin ta moriyar juna domin neman bunkasuwa tare.

Tun daga shekaru 60 na karnin 20 da ya gabata, tattalin arzikin yankin Taiwan na kasar Sin ya samu bunkasuwa cikin sauri sosai har na tsawon shekaru 40, wato saurin karuwar tattalin arzikinsa ya kai kashi 9 cikin kashi dari a kowace shekara. Amma bayan da jam'iyyar neman cigaban dimokuradiyya ta Taiwan ta hau kan mukamin mulkin yankin Taiwan a shekara ta 2000, tana bin manufar neman 'yancin Taiwan da take adawa da ra'ayoyin jama'ar Taiwan. Kuma bai yi kome ba kan yadda za a raya tattalin arzikin yankin Taiwan. Wannan ya sa tattalin arzikin Taiwan ya shiga cikin mawuyacin hali, saurin karuwar tattalin arziki ya kai kashi 3 cikin kashi dari kawai a kowace shekara, amma mizanin yawan mutanen da suka rasa aikin yi yana ta karuwa. Mr. Ye Wan'an, mai ba da shawara ga cibiyar nazarin tattalin arzikin kasar Sin da ke Taiwan yana ganin cewa, a cikin halin da ake ciki yanzu, idan bangaren Taiwan bai yi hadin guiwa da bangaren babban yanki a fannin tattalin arziki ba, yankin Taiwan zai shiga cikin hali mai hadari. Mr. Ye ya ce, "A cikin shekaru 6 da suka wuce, ingancin zaman rayuwar jama'ar Taiwan bai samu kyautatuwa ba, jama'ar Taiwan suna taka tsantsan wajen kashe kudi. Bugu da kari kuma, domin yanzu ana bunkasa tattalin arziki bai daya a duniya, musamman bangaren babban yankin kasar Sin yana hada kan kasashen Asean da Japan da Koriya ta kudu. Sabo da haka, idan yankin Taiwan yana son neman bunkasuwa a nan gaba, dole ne ya yi hadin guiwa da babban yankin."

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, bayan da babban yankin ya yi kokari, bangarorin biyu da ke tsakanin mashigin tekun Taiwan sun yi ciniki a tsakaninsu cikin sauri. Amma domin hukumar Taiwan ta kan sa hannu kan cudanyar tattalin arziki da ake yi a tsakanin bangarorin 2, har yanzu 'yan kasuwa na gabobin 2 ba su iya yin sufurin kayayyaki da zuba jari a tsakaninsu kai tsaye ba. Masana'antun babban yankin kasar Sin ba su samu izinin zuba jari a tsibirin Taiwan ba. A kan wadannan matsalolin da suke kasancewa a gabansu, wakilai fiye da dari 4 wadanda suka halarci taron dukkansu sun bayyana cewa, za su ci gaba da kokarin neman izinin yin zirga-zirga a tsakanin gabobin 2 kai tsaye. Mr. Zhang Guanhua, shehun malami ne da ke nazarin maganar Taiwan a cibiyar nazarin zaman al'ummar kasar Sin ya bayar da ra'ayinsa cewa, kafin a cimma burin yin zirga-zirga kai tsaye ka'in da na'in a tsakaninsu, ya kamata a yi zirga-zirga kai tsaye a tsakanin wasu birane na gabobin 2. Mr. Zhang ya ce, "Yanzu ya kasance da wasu tasoshin ruwa da wasu filayen jirgin sama masu yin ciniki cikin 'yanci a Taiwan, bangaren babban yankin kasar Sin ma yana iya kafa irin wadannan tasoshin ruwa na yin ciniki cikin 'yanci. Sabo da haka, za a yi zirga-zirga a tsakanin wadannan tasoshin ruwa na gabobin 2 kai tsaye."

Bayan da aka sami bunkasuwa a cikin shekaru 20 da suka wuce a nan babban yankin kasar Sin, masana'antu masu jarin Taiwan da aka kafa a nan babban yankin sun riga sun samu ci gaba sosai kuma sun zama masana'antun da ke suke neman bunkasuwa bisa fasahohin zamani. A sa'i daya kuma, babban yankin kasar Sin ma yana kokarin canja hanyar neman bunkasuwar tattalin arziki. A gun wannan taron fadin albarkacin bakinka, Mr. Jia Qinglin, shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin ya ce, "A nan gaba, ya kamata gabobin biyu su kara yin musanye-musanye da hadin guiwa kan wasu muhimman sana'o'i. Kuma su kafa tsari da dandalin yin amfani da makamashin kimiyya da fasahohin zamani tare." (Sanusi Chen)