Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-12 17:33:06    
Baradei ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su yi rangwame a kan matsalar nukiliya ta kasar Iran

cri

A ran 11 ga wata a birnin Amsterdam, babban birnin kasar Holland, babban daraktan hukumar makamashin nukiliya ta duniya Mohammed Mostafa El-Baradei ya bayyana cewa, ya yi maraba ga MDD da ba ta saka takunkumi a kan Iran ba, haka kuma ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su yi rangwame a kan matsalar nukiliya ta kasar Iran.

Mr. Baradei ya yi wannan bayani ne a gun wani taron manema labaru da aka shirya a ran nan. Ya ce, ya yi farin ciki sosai domin MDD ba ta saka takunkumi a kan Iran kuma kasashen kungiyar EU suna samar da wasu shirye-shirye a jere domin sa kaimi ga kasar Iran da ta gama kai da sauran kasashe.

Mr. Baradei ya ci gaba da cewa, yana fata bangarorin da abin ya shafa ba za su kai suka a kan juna ba, za su kuma yi rangwame a kan matsalar nukiliya ta kasar Iran.(Danladi)