Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-12 16:55:58    
Kasar Sin ta raya wasannin motsa jiki na nakasassu domin shekarar 2008

cri
A gun taron ganawa da kafofin yada labaru da kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasar Sin ya shirya a kwanan baya, Wang Lijing, wata budurwa mai kyakkyawa, tana zauna a kusurwar dakin, wadda ke da shekaru 17 da haihuwa, amma ita makauniya ce, ba ta ga kome ba.

Ko da yake haka ne, makanta ba ta hana Wang Lijing tana kishin zaman rayuwa ba. Tun daga shekarunta ya kai 8, ta fara gwada gwanintarta a cikin wasannin motsa jiki. Bayan hadaddiyar kungiyar nakasassu ta birnin Tianjin ta gano gwanintarta, Wang Lijing ta fara yin wasan judo. Ta yi shekaru 3 tana yin kokarinta sosai, yanzu ta zama daya daga cikin 'yan wasan judo makafi mafi nagarta na kasar Sin, sa'an nan kuma, an mayar da ita a matsayin 'yar wasa da za ta samu lambar zinare ko azurfa a cikin duniya.

Wang Lijing ta ci irin wannan nasara saboda gwanintarta da kokarin da ta yi, ta san matsala mafi girma da makafi za su daidaita a lokacin da suke yin wasannin motsa jiki sosai, ta ce,'ga misali, idan wani mutum ya koyi wasan judo, malami ya horar da shi, zai gane yadda zai yi da idanunsa; amma mu makafi ba mu ga kome ba. Malamanmu sun koyar da muda hannunsu, mun taba su, mun ji yadda za Wang Lijing ta kan yi aikin horo awoyi 5 a ko wace rana, kwanaki 6 a ko wane mako, ba ta yi hutu ba a duk shekara. Horo da gasanni sun kusan zama zaman rayuwar Wang Lijing. Watakila ba a jure wannan ba, amma Wang Lijing ta ji dadin zaman rayuwarta kwarai?

Akwai nakasassun da suka himmantu ga wasannin motsa jiki suka nuna darajarsu, kamar yadda Wang Lijing take yi, masu yawa a kasar Sin, sun samar da babban rukunin wasannin motsa jiki na nakasassu na kasar. Wannan kuma ya shaida dalilin da ya sa nakasassun kasar Sin sun sami manyan nasarori a cikin wasannin Olympic na nakasassu. Mutane da yawa sun yi imanin cewa, 'yan wasan kasar Sin za su ci gaba da nuna fifikonsu a cikin wasannin motsa jiki na nakasassu da za a yi a nan Beijing a shekarar 2008.

Amma, mataimakiyar babbar sakatariya mai gudanarwa ta kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasar Sin madam Zhao Sujing ta bayyana cewa, zama lambawan a cikin jerin kasashe a fannin samun lambobin yabo a cikin wasannin Olympic na nakasassu ba makasudi ne kurum ga kasar Sin da ta raya sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu. Ta ce,'abin da ya fi muhimmanci shi ne nuna ra'ayi, wato nakasassu sun nuna kansu, sun nemi gwada darajarsu a cikin gasannin da suka yi. Suna jin alfahari sosai saboda sun ba da gudummowarsu don kasar Sin. Shi ya sa 'yan wasa nakasassu sun yi korari kawari da gaske.'

Madam Zhao ta kara da cewa, muhimmin abu ne sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu na kasar Sin shi ne kara sa kaimi kan nakasassu da su motsa jiki, su ji dadin rayuwarsu. Amma a gaskiya kuma, an yi karancin gine-ginen motsa jiki da suka dace da nakasassu a duk kasar Sin. Ko da yake akwai gine-ginen motsa jiki a birane daban daban na kasar, amma saboda matsalolin aikatawa da yin cudanya, da kyar nakasassu su ji dadin yin amfani da wadannan gine-gine. A zahiri kuma, daidaita wannan matsala yana da sauki. Game da wannan, madam Zhao ta ganin cewa,'ina tsammani za a warware wannan matsala cikin dukan birane. Alal misali, za a samar da wani bayanin da aka yi da rubutun makafi a kusa da gine-ginen motsa jiki, ta haka, makafi za su gane yadda za su yi amfani da wadannan gine-gine, za su sa hannu a ciki. Ba za a bukaci kudade masu yawa ko kuma yin kwaskwarima sosai kan gine-ginen ba.'

Ban da wannan kuma, madam Zhao ta yi la'akari da cewa, ban da kara samar da gine-ginen motsa jiki ba tare da shige ba, har ma, ya kamata a samar da gine-ginen musammab ga nakasassu.

Kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya kuma gabatar da cewa, ya dora muhimmanci sosai kan shirya wasannin Olympic na nakasassu na shekarar 2008, zai tabbatar da ganin shirya wasannin Olympic na nakasassu na karo na 13 da kuma wasannin Olympic na lokacin zafi na karo na 29 a lokaci daya, wadanda za su ci nasara tare, sa'an nan kuma, za a yi amfani da damar shirya wasannin Olympic na nakasassu wajen karfafa ra'ayin al'ummar kasar a fannonin mai da hankali da ba da taimako ga nakasassu da goyon bayan sha'anin nakasassu. A idon madam Zhao Sujing, manufofin da kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing ya bayar sun yi daidai da wadanda ake bi wajen raya sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu na kasar Sin.