A ran 25 ga watan Afrilu na shekarar nan,wakilin kasar Sin ya kai ziyara a kamfanin L.T.D mai ba da jagora ga hanyar internet wanda ya yi cinikin taswirar na'urori masu aiki da kwakwalwa na duk kasar Sin.Yanzu, a kasar Sin taswirar na'urori masu aiki da kwakwalwa na ba da jagora ta kasar Sin ta iya rufe birane 313 na duk kasar Sin.Yanzu an riga an kafa hanyoyin internet a duk kasar. Har an nuna tabbaci cewa, za a iya ba da jagora ta hanyar internet a duk mafadin kasar Sin.
A ran 25 ga watan Afrilu, a gun babban taro yin safiyo ta hanyar kimiyya na duk kasa da aka shirya ne wakilin kasarmu ya sami labarin nan.
A duk duniya, a wurare da yawa an fara yin amfani da dabarar nan, kana kuma cikin 'yan shekaru da suka shige, sha'anin ba da jagora ta hanyar internet shi ma ya sami saurin bunkasuwa sosai.Misali a kan motoci da tashoshin ba da jagora da tashar kula da zirga zirga dukkansu sun fara yin amfani da irin taswirar na'urori masu aiki da kwakwalwa.
Kasar Sin tana da babban karfin kasuwanci yin cinikin sana'ar na'urori masu aiki da kwakwalwa.Kana kuma wannan sha'anin na'urori masu aiki da kwakwalwa ga ba da jagora ta kasarmu ya sami saurin bunkasuwa sosai. Kuma kwararru sun yi kimanta cewa, yawan kudin da kasar Sin ta kan samu daga kasuwannin yin cinikin taswirar na'urori masu aiki da kwakwalwa na ba da jagora a kowace shekara sun kai biliyan kusan l0, Hatta ma bisa saurin karuwar kashi 200 zuwa 300 cikin dari ne ana yi ta kara samu bunkasuwa sosai.
Kuma masana suna gani cewa, taswirar na'ura mai aiki da kwakwalwa wajen ba da jagora wannan ta kai wani kashi daga cikin ayyukan bunkasuwar tattalin arziki na kasar Sin. Wani babban manaja na babban kamfanin ba da jagora ta hanyar internet na birnin Beijing ya bayyana cewa, an kasance da irin ra'ayi ne a lokacin da kasar Sin ta fara tafiyar da shirin raya kasa na shekaru 5-5 na karo na l0 na kasar, ofishin yin safiyo na gwamnati ta kara karfin kan kulawar sha'anin taswirar na'urori masu aiki da kwakwalwa na ba da jagora, har an kafa tsarin shigar da sha'anin nan, da tsara manufofin da abin ya shafa, Bugu da kari kuma, kwamitin neman bunkasuwar tattalin arziki da yin gyare gyare na gwamnati ya kafa tsarin dokoki kan sha'anin nan, har cikin shekaru 2 zuwa 3 ne da suka shige, an canja surar sha'anin nan da kyau.Duk wannan ya bayyana a kan sassa daban daban:
Misali da farko, matsayin fasahar na'urori masu aiki da kwakwalwa na ba da jagora na kasarmu ya dagu, kuma karfin sana'ar nan ya kara karuwa sosai, a karshe dai an sami babban sakamako, kuma tare da nasara an fara yin fasahar nan a kan sassa daban daban na zaman rayuwar jama'a na kasar Sin. Kuma wannan ya iya biya bukatun bunkasuwar sana'ar neman ba da jagora ta kasar Sin.
Ban da haka kuma, don ingiza bunkasuwar sha'anin neman ba da jagara ta hanyar intenet, sai kwamitin neman bunkasuwar tattalin arziki da yin gyare gyare na gwamnati ya kafa tsarin dokokin musamnan na sana'ar ba da jagora ta hanyar internet.Wani shugaba na sashen nan ya bayyana cewa, bisa tushen labarin kasa ne ofishin yin safiyo na gwamnati ya ba da babban taimakonsa.(Dije)
|