Jama'a masu sauraro, assalamu alaikum, barka da wannan lokaci, kuma barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na 'amsoshin wasikunku'. Ni ce Lubabatu ke gabatar muku da wannan shiri kuma ke yi muku sallama daga nan gidan rediyon kasar Sin da ke nan birnin Beijing. Masu sauraro, a cikin farkon shirinmu na yau, za mu karanto muku wasu ra'ayoyi ko gaishe-gaishe da masu sauraronmu suka rubuto mana a cikin wasiku ko ta hanyar E-mail, daga baya, za mu amsa wasu tambayoyin da masu sauraronmu suka yi mana.
Masu sauraro, kwanan nan, malam Mamane Ada daga birnin Yamai na kasar Nijer ya rubuto mana Email cewa, a gaskiya abun kamar hasken rana, abun da ya sa na ce haka don tun lokacin da rediyo r&m ta fara watsa shirye-shiryen rediyon kasar Sin. Abu na farko ga mazauna birnin Yamai shi ne mamaki na jin Sinawa na Hausa. Abu na biyu shi ne tambayar da suke ina Sinawa suka koyi Hausa. Hakan ya sa abun ya zama yayi ga mazauna Yamai da an ce Sin ta fara shirye shiryen Hausa, to, ka ga kowa ya manne ga rediyonsa. Shiri kamar na labarun gida da na duniya, amsoshin wasikunku, Sin da Afirka, Koyon Sinanci su ne aka fi saurare. Tambayar da suke shi ne yaushe CRI za ta fara ba da labaru da suka shafi kasar Nijer. To, malam Mamane Ada, mun gode maka kwarai da gaske sabo da shawara mai kyau da ka ba mu. Kullum muna watsa muku labarun kasar Sin da na sauran kasashen duniya a kowace rana, musamman ma mun fi mai da hankali a kan labaru na kasashen Afirka, ciki har da na Nijer. A nan gaba ma, za mu kara ba da labarun da suka shafi kasarku. Dangane da tambayar nan ta a ina ne Sinawa suka koyi Hausa, sauran masu sauraronmu masu yawa ma su kan yi mana wannan tambaya, shi ya sa nan kadan, a cikin shirinmu na yau, za mu amsa muku wannan tambaya, sai ku ci gaba da kasancewa tare da rediyon kasar Sin.
Masu sauraro, Muna fatan za ku ci gaba da aiko mana wasiku ko Email, ku fadi albarkacin bakinku, ko ra'ayoyi ko shawarwari a kan shirye-shiryenmu, don mu kyautata su tare. Kada kuma ku manta kuna iya turo wasikunku ta akwatin gidan wayarmu a kasar Nijeriya, wato Lagos Bureau, China Radio International P.O.Box 7210, Victoria Island, Lagos Nijeriya. ko kuma ku aiko mana wasiku zuwa nan kasar Sin, wato, Hausa Service CRI-24, China Radio International, P.O.Box 4216, Beijing, P.R.China,100040. kuna kuma iya aiko mana Email a kan Hausa @cri.com.cn.
To, masu sauraro, yanzu lokaci ya yi da za mu amsa tambayar da malam Mamane Ada da dai sauran masu sauronmu na birnin Yammai suka yi mana, wato shin a ina ne Sinawa suka koyi Hausa. Hasali ma dai, masu sauraronmu da yawa su kan yi mana wannan tambaya, sabo da suna jin mamakin Sinawa na Hausa. To, masu sauraro, bari in amsa muku tambayar. Yawancin Sinawa sun koyi Hausa ne a nan kasar Sin, wato a cikin jami'a. A halin yanzu dai, akwai jami'o'i biyu a nan kasar Sin wadanda ke koyar da Hausa, wato daya ita ce jami'ar Koyon harsunan waje ta Beijing, dayan kuwa ita ce, jami'ar koyon fasahohin watsa labarai ta kasar Sin. Amma hakika, ba kwana daya ko biyu Sinawa suka soma karanta Hausa ba, a'a, tun daga shekarun 1960 ne, Sinawa suka fara koyon Hausa. Amma don ba ku cikakken tarihin Sinawa na koyon Hausa, shi ya sa wakiliyarmu Lubabatu ta ziyarci wani babban malami na koyar da Hausa a nan birnin Beijing, wato malam Yusuf, ta yi hira da shi, don ya ba ku amsa.
Lubabatu: To, malam, assalam alaikum.
Yusuf: Alaikum salam.
Lubabatu:Ko za ka bayyana kanka ga masu sauraronmu?
Yusuf:OK, ni malami ne mai koyar da Hausa a jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing, China, sunana na Hausa Yusuf. A shekara ta 1965, wato bayan na gama karatuna na sakandare, na ci jarrabawar neman shiga jami'ra koyon harsunan waje ta Beijing, na fara koyon Hausa. Na yi shekaru hudu ina koyon Hausa. A shekara ta 1969, na gama karatun Hausa, kuma na kama aiki, na zama malami. Don kara zurfafa ilmina na Hausa, a shekara ta 1994, bisa yarjejeniyar al'adu tsakanin kasar Sin da Nijeriya, gwamnatinmu ta aika da ni zuwa Nijeriya. Na yi shekara daya ina karatu a Ahmadu Bello University, wato ABU, har yanzu, ina aikin koyarwa a nan Beijing.
Lubabatu:Hausawa su kan ji mamaki lokacin da suka samu Sinawa masu iya Hausa, lokacin da suka same ka wanda ke iya Hausa, ko sun ji mamaki?
Yusuf:Gaskiyarki. Sun ji mamaki kwarai da gaske. In mun yi hira, su kan tambaye ni, a ina ne aka haife ni, kuma a ina ne na koyi Hausa. Na gaya musu, an haife ni a China, kuma na fara koyon Hausa ma a China.
Lubabatu:Amma hasali ma dai, an dade da samun Sinawa masu iya Hausa, sabo da an kafa sashen Hausa a jami'ar koyon harsunan waje ta Beijing a shekara ta 1964, to, amma me ya sa a lokacin, aka ga cewa, ya kamata a kafa sashen koyon harshen Hausa a kasar Sin?
Yusuf:Sabo da a lokacin, mutanen duniya, musamman ma mutanen Asiya da Afirka da Latin Amurka, suna gwagwarmayar neman 'yancin kansu, kuma suna gwagwarmaya sosai da mulkin mallaka don samun 'yancin kansu, a wancen lokaci, gwamnatinmu tana ganin cewa, ya kamata a sa wasu dalibai su koyi harshen Asiya da Afirka da na Latin Amurka, domin mu ba da taimakonmu ga gwagwarmayarsu, shi ya sa a nan jami'armu, aka kafa sashen Hausa a 1964.
Lubabatu:Kana daya daga cikin Sinawa da suka fara koyon Hausa a wannan jami'ar, ko za ka yi dan bayani a kan yadda kuka koyi wannan harshe a lokacin can?
Yusuf:Sabo da farkon kafuwar wannan harshe, a lokacin, Sinawa, kamar ba wanda ya iya Hausa, shi ya sa da farko, gwamnatinmu ta aika da wasu dalibai masu koyon Turanci zuwa Ghana, don su fara koyon Hausa. Kuma a lokacin, mun gayyaci wani Bahaushe, wanda ya zo daga Nijer, an sa ya fara aikin gidan rediyo, yana aikin gidan rediyo, kuma yana koyarwa, jami'armu ta zabi dalibai biyu wadanda ke koyon Faransanci, su je gidan rediyon Beijing, domin su fara koyon Hausa da wancan Bahaushe. Bayan sun gama karatunsu na Hausa, wato wadanda suka je Ghana da wadanda suka je gidan rediyo, sai sun dawo nan jami'a, an kafa sashen Hausa, kuma an fara daukar dalibai masu koyon Hausa. Ni ina daya daga cikinsu.
Lubabatu:Dalibai nawa ne suka koyi wannan harshe tare da kai?
Yusuf:Mu tara kawai, maza 7 da mata biyu.
Lubabatu:Daga bayanku, shin an rika koyar da Hausa a nan jami'ar? Ya zuwa yanzu, dalibai nawa ne suka gama karatun Hausa kuma suka sami digiri daga nan jami'ar?
Yusuf:Tun bayan da aka kafa sashen Hausa a nan jami'ar, kusan ko wadanne shekaru 4, a kan dauki sababbin dalibai masu koyon Hausa. Har zuwa yanzu, yawansu ya kai wajen 100.
To, masu sauraro, ko kun ji dadin amsa da muka ba ku. Daga nan, tilas ne mu dasa aya. Tare da fatan za ku ci gaba da kasancewa tare da shirinmu na 'amsoshin wasikunku' a mako mai zuwa, ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, sai mako mai zuwa, ku huta lafiya.(Lubabatu Lei)
|