Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-10 21:55:01    
Kasar Sin za ta kara tabbatar wa 'yan kwadago ikonsu da kuma moriyarsu

cri
Ran 10 ga wata, babbar jam'iyyar 'yan kwadago ta kasar Sin wadda ke wakiltar ikon 'yan kwadago na kasar Sin da moriyarsu ta bayyana cewa, yawan ra'ayoyi da shawarwari da 'yan kwadago na yau da kullum suka gabatar a kan doka kan kwangilar daukar 'yan kwadago wadda ake shiryawa ya wuce dubu 100. Wannan ne karo na farko da aka samu ra'ayoyi da shawarwari masu yawa kamar haka, yayin da ake kafa wata doka a kasar Sin har cikin sama da shekaru 50 da suka wuce.

Bisa kidayar da gwamantin kasar Sin ta bayar, an ce, tun daga shekarar 1995 zuwa ta 2004, yawan 'yan kwadago na birane da garuruwa na kasar Sin ya karu daga miliyan 190 zuwa miliyan 265, haka nan kuma yawan manoma da suka samu aikin yi a birane da garuruwa ma ya kai miliyan 100. A sa'i daya kuma yawan kara da wadannan yan kwadago da manoma suka gabatar dangane da aiki shi ma ya karu sosai. A cikin shekarun nan 10 da suka wuce, yawan ire-iren kararrrakin nan ya kai miliyan 1 da dubu 300 a kasar Sin, kuma ya shafi 'yan kwadago da yawansu ya wuce miliyan 4 da dubu 400.

A karshen shekarar bara ne, aka gabatar da shirin doka kan kwangilar daukar 'yan kwadago ga hukumar dokoki ta kasar Sin don dudduba shi. Malam Rui Lixin, mataimakin shugaban ofishin dokoki na ma'aikatar kwadago da tabbatar da zaman jama'a ta kasar Sin ya bayyana cewa, "makasudin kafa doka kan kwangilar daukar 'yan kwadago shi ne tabbatar wa 'yan kwadago iko da moriya, kuma da sa kaimi ga samar da jituwa tsakanin 'yan kwadago da masu daukar su, ta yadda za a ba da taimako wajen bunkasa harkokin zaman jama'a da na tattalin arziki."

Don cim ma wannan makasudi, hukumar dokoki ta kasar Sin ta tsai da kuduri a kan sauraron ra'ayoyi sosai daga wajen jama'a. Madam Xin Chunying, mataimakiyar shugaban hukumar kula da harkokin dokoki da kwadago ta zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta ce, "muna fatan za mu iya sauraron ra'ayoyi daga bangarori daban daban a kan shirin doka kan kwangilar daukar 'yan kwadago, musamman ma 'yan kwadago na yau da kullum. Za mu yi la'akari da wadannan ra'ayoyi sosai, yayin da muke yin kwaskwarima kan shirin dokar nan."

A cikin wata daya da yake saurarar ra'ayoyi a kan shirin doka kan kwangilar daukar 'yan kwadago, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasa ta Sin ya sami ra'ayoyi da shawarwari da yawansu ya kai kimanin dubu 200 daga bangarori daban daban. Daga cikinsu, kashi 2 cikin kashi 3 na yawan nan an same su ne daga 'yan kwadago na yau da kullum. An gabatar da wadannan ra'ayoyi ne musamman a kan yadda za a daidaita batun kulla kwangilar daukar 'yan kwadago cikin gajeren lokaci, da yadda za a biya diyyar kudi ga marasa aikin yi, da kuma yadda za a tsai da tsawon lokacin daukar 'yan kwadago bisa gwaji da yawan 'yan kwadago da za a sallame su da dai sauransu. Duk irin wadanan ra'ayoyi sun dace da makasudin kafa dokar nan.

Malam Li Yuan, shugaban sashen kula da doka kan gudanar da harkokin mulki na kwamitin dokoki na majalisar wakilan jama'ar kasa ta Sin ya bayyana cewa, " bisa halin da ake ciki yanzu a kasar Sin, 'yan kwadago masu neman aikin yi sun fi yawan da ake bukata. Sabo da haka wajibi ne, mu tanadi abubuwa a cikin dokar don daidaita matsaloli da ake gamuwa da su wajen tauye moriyar 'yan kwadago sosai, kuma mu ba da taimako ga 'yan kwadago don kare iko da moriyarsu." (Halilu)