Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-10 16:06:33    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(04/05-10/05)

cri
Ran 7 ga wata, an rufe gasannin cin kofunan Thomas da Uber na wasan kwallon badminton tsakanin kungiyoyi na shekarar 2006 a birnin Tokyo na kasar Japan, kungiyoyin maza da mata na kasar Sin sun kwashe dukan kofunan Thomas da na Uber. A cikin karon karshe na gasar tsakanin kungiyoyin maza, kungiyar kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Denmark da ci 3 ba ko daya, ta ci kofin Thomas ne a karo na 5. Kungiyar mata ta kasar Sin kuma ta lashe kungiyar kasar Holland da ci 3 ba ko daya, ta yadda ta ci kofin Uber a karo na 10.

Akwai wani labari daban game da wasan kwallon badminton da aka bayar daga Tokyo. Ran 6 ga wata, Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kwallon Badminton ta Duniya ta kira taron shekara-shekara, inda ta tsai da kudurin fara aiwatar da tsarin samun maki 21 a hukunce a cikin gasannin da za a yi a nan gaba, don rage lokacin gasar wasan kwallon badminton, ta haka za a jawo hankulan 'yan kallo da raya kasuwa da kuma taimakawa watsa shirye-shirye kan telibijin kai tsaye.

Ban da wannan kuma, a gun wannan taron, darektan kula da gasar wasan kwallon badminton na kwamitin shirya wasannin Olympic na Beijing Mr. Ren Chunhui ya gabatar da cewa, za a yi kwanaki 9 ana yin gasar wasan kwallon badminton a cikin wasannin Olympic na Beijing, kuma za a yi takara don neman samun lambobin zinare 5 a cikin kwanaki 3 na karshe.

An kammala gasar fid da gwani ta wasan kwallon tebur tsakanin kungiyoyi ta duniya ta karo na 48 a birnin Bremen na kasar Jamus a ran 1 ga wata, kungiyoyin maza da mata na kasar Sin dukansu sun zama zakaru. A cikin karon karshe na gasar tsakanin kungoyoyin maza, kungiyar maza ta kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Korea ta Kudu da ci 3 ba ko daya, kungiyar mata ta kasar Sin kuma ta lashe kungiyar Hong Kong ta kasar Sin da ci 3 da 1.

A cikin gasar ba da babbar kyauta da Hadaddiyar Kungiyar Wasan Tsalle-tsalle da Guje-guje ta Duniya ta shirya a birnin Osaka na kasar Japan a ran 6 ga wata, dan wasan kasar Sin Liu Xiang ya zama zakara a cikin gasar gudun ketare shinge mai tsawon mita 110 da dakikoki 13 da 22, wannan ne karo na 3 da ya sami lambar zinare a cikin wannan gasar da aka shirya a Osaka.

An kawo karshen budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta Estoril ta karo na 17 a birnin Lisbon na kasar Portugal a ran 7 ga wata, 'yan wasan kasar Sin mata sun zama zakaru a cikin gasannin tsakanin mace da mace da kuma tsakanin mata biyu biyu. A cikin karon karshe na gasar tsakanin mace da mace, 'yar wasan kasar Sin Li Na ta janye jikinta saboda ciwon kafarta ta dama, ta haka 'yar takararta kuma abokiyarta Zheng Jie ta zama zakara. A cikin karon karshe na gasar tsakanin mata biyu biyu, 'yan wasan kasar Sin Li Ting da Sun Tiantian sun lashe 'yar wasan kasar Argentina Gisela Dulko da 'yar wasan kasar Spain Sanchez Lorenzo da cin 2 ba ko daya, don haka sun sake zaman zakaru.(Tasallah)