Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-08 17:44:24    
Kasar Sin ta dora muhimmanci kan ba da ilmin jima'i tsakanin matasa

cri

Yanzu ga wani bayanin da muka shirya muku da ke da lakabi haka 'Kasar Sin ta dora muhimmanci kan ba da ilmin jima'i tsakanin matasa', wakilin gidan rediyon kasar Sin ya aiko mana wannan bayani ne bayan da ya kai ziyara a wata makarantar midil ta Beijing.

'malam: zan gaya muku wani labari game da wata budurwa, sunanta Yueyue, shekarunta ya kai 16, wata rana, a cikin makaranta, ta gamu da wani namiji, wai shi Li Qiang, wanda ke da 18 da haihuwa. Yana da kyakkyawa. Sannu a hankali, sun fara zuwa makaranta da kuma koma gida tare. Amma Yueyue ba ta kwantar da hankalinta sosai ba, shi ya sa, ta je wajen malami mai ilmin halin dan Adam, ta yi tambaya ta ce, a ganinka, ko ina sonsa?

'yan makaranta sun yi murmushi.

Malamin ya ci gaba da cewa, Yueyue ta kara da cewa, a ganinka, ko za mu yi zaman tare har abada? To, ko kuna tsamani Yueyue da Li Qiang za su yi zaman tare har abada?

'yan makaranta ba su ce kome ba.'

Abubuwan da kuka ji a dazun nan hira ce da ke tsakanin malami da 'yan makarantar midil ta 171 ta Beijing a kan ilmin kiwon lafiya a lokacin kuruciya. An tafiyar da wannan kos a makarantu masu yawa a Beijing da sauran birane fiye da 10 da kuma wasu yankunan kauyuka. Wannan kos yana daya daga cikin manyan abubuwan da aka tanadi cikin 'aikin kiwon lafiya a lokacin kuruciya' da hadadiyyar kungiyar harkokin yin haihuwa bisa shiri ta kasar Sin ta aiwatar da shi don ba da ilmin jima'i tsakanin matasa.

Wannan kungiya ta kyautata hanyoyin da aka bi wajen tafiyar da kos na kiwon lafiya a lokacin kuruciya, ta ba da wannan kos ta hanyar kimiyya yadda ya kamata, matasa sun kara amincewa da shi.

Ga misali, dazun nan kun ji hira tsakanin malami da 'yan makarantar midil mai lambar 171 ta Beijing. An koyar da matasa yadda matasa maza da mata suka yi cudanya da juna. 'Yan makarantar sun fi sa hannu cikin kos din da aka koya musu. Su Min, wata budurwa, mai shekaru 16 da haihuwa, ta nuna sha'awa kan wannan kos sosai. Ta ce,

'malaminmu ya koya mana yadda mata da maza suka yi cudanya da juna yadda ya kamata. Mun ji dadin koyon irin wannan kos, saboda mun iya yin mu'amalar ra'ayoyinmu sosai.'

Yin cudanya tsakanin maza da mata wani kashi ne na kos na kiwon lafiya a lokacin kuruciya, ya kuma hada da ilmi na yin haihuwa da hana haihuwa da yin rigakafin cutar AIDS da yin jima'i. Don tafiyar da wannan aiki lami lafiya, hadadiyyar kungiyar harkokin yin haihuwa bisa shiri ta kasar ta tsara littattafai da yawa, ta kuma zaba da horar da malamai. Don tabbatar da ingancin malamai, ta zabi malaman da suka ba da kos na kiwon lafiya a lokacin kuruciya daga masu sa kai na musamman, kamarsu malamai da likitoci da masu ba da shawara kan hankalin dan Adam da dai sauransu.

Kos na kiwon lafiya a lokacin kuruciya ya sami maraba. Yanzu an tafiyar da shi a makarantu misalin 300 a duk fadin kasar Sin. Ga misali, ana tafiyar da kos na kiwon lafiya a lokacin kuruciya a makarantar midil mai lambar 54 ta Beijing. Ana koyar da 'yan makarantar sakatare na aji na 1 da na 2 cikin mintoci 45 a ko wane mako. 'Yan makarantar sun kuma bude shafin Internet da kansu, inda suka gabatar da ilmin kiwon lafiya a lokacin kuruciya, sa'an nan kuma, 'yan makarantar suka iya yin mu'amalar abubuwan da suka koya. Da zarar budewar wannan shafi, sai 'yan makarantar suna maraba da shi sosai. Malamai kuma suna nuna goyon baya. Madam Chen Hong, malama mai ilmin hankalin dan Adam ta musamman a makarantar midil mai lambar 54, wadda ta koyar da kos na kiwon lafiya a lokacin kuruciya, ta yi bayanin cewa, shafin da 'yan makarantar suka bude ya bayyana ra'ayoyin da 'yan makarantar suke tsayawa a kai, hukumar makarantar ta goyon bayan ci gaba da bude wannan shafi. Ta ce,

'bayan da 'yan makaranta na wannan zagaye suka gama karatu, sabbin makaranta za su ci gaba da wannan aiki. Sa'an nan kuma, muna da hadaddiyar kungiyar 'yan makaranta, muna son za ta sa hannu cikin sabunta da kuma kyautata wannan shafi.'

Ban da kos kuma, aikin kiwon lafiya a lokacin kuruciya yana kunshe da ayyukan sa kaimi kan lafiyar matasa a jere. Sakatariyar hadaddiyar kungiyar harkokin yin haihuwa bisa shiri ta kasar madam Li Yanqiu ta bayyana cewa, an sami babbar nasara bayan da aka aiwatar da aikin kiwon lafiya a lokacin kuruciya a shekaru 5 da suke wuce. Ta kuma kara da cewa, kungiyarta za ta ci gaba da ba da ilmin lokacin kuruciya tsakanin matasa, sun yi shirin kara tafiyar da aikin kiwon lafiya a lokacin kuruciya a makarantun da yawansu zai ninka har sau daya a cikin shekaru 5 masu zuwa.(Tasallah)