Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-08 17:13:40    
A kwana a tashi ana kara karfin hadin guiwar aikin gona tsakanin bangarori biyu na Zirin tekun Taiwan

cri
Tun daga ran 1 ga wannan wata, yawan irin 'ya'yan itatuwa da babban yankin kasar Sin ya amince da shigowa da su daga Taiwan ya karu zuwa 22. Mutane da abin ya shafa sun bayyana cewa, wannan karin manufar da babban yankin kasar Sin ya tsaida don kawo fa'ida ga manoman Taiwan a cikin 'yan shekarun nan biyu da suka wuce, kuma ya shaida cewa, hadin guiwar aikin gona da ake yi tsakanin bangarorin biyu na zirin tekun Taiwan kullum sai kara karfi yake yi.

A gun taron dandalin tattaunawa kan tattalin arziki da ciniki tsakanin bangarorin nan biyu da aka yi  kwanakin baya a nan birnin Beijing, babban yankin kasar Sin ya bayar da manufofi da matakai guda 15 da ya dauka wajen sa kaimi ga kara musanya da hadin guiwa a tsakanin bangarori biyu don kawo fa'ida ga jama'ar Taiwan. Daya daga cikinsu shi ne karin ire-iren amfanin gona da Taiwan ke fitarwa zuwa babban yankin kasar Sin. Bisa sabuwar amincewa da aka samu, tun daga ran 1 ga wata, an fara sayar da wani irin lemo na Taiwan da lemo mai tsami da sauran 'ya'yan itatuwa na Taiwan a birnin Xiamen na lardin Fujian da ke a kudancin kasar Sin. Malam Huang Chengqing, babban direktan kungiyar manoma ta kauye mai suna Yuejing na Taiwan ya bayyana cewa, a da, manoman Taiwan sun gamu da wahala wajen sayar da lemo, yanzu, manufar da babban yankin kasar Sin ke tafiyar dangane da kara shigo da amfanin gona daga Taiwan ta ba mu babban taimako. Ya ce, "yanzu, mun sami damar sayar da lemonmu a kasuwannin babban yankin kasar, a ganina, ta haka ne za mu iya daidaita matsalarmu game da wasu rarar amfanin gona da ba mu iya sayarwa a Taiwan ba. Na hakake, wannan zai ba da babban taimako ga raya aikin gona a Taiwan. "

An ruwaito cewa, tun daga ran 1 ga wata, ban da 'ya'yan itatuwa da babban yankin kasar Sin ke kara shigowa da su daga Taiwan, haka nan kuma ya amince da shigowa da manyan ire-iren ganyayen lambu 11 daga Taiwan ba tare da buga harjin kwastan ko kwabo daya ba. Kungiyoyin sana'o'i da abin ya shafa za su aika da tawagarsu zuwa Taiwan don yin odar 'ya'yan itatuwa da ganyayen lambu.

A hakika dai, a shekarar bara, babban yankin kasar Sin ya riga ya kara yawan ire-iren 'ya'yan itatuwa da yake shigowa da su daga Taiwan, kuma ba ya buga harajin kwastan ko na kobo daya a kan wasu daga cikin wadannan 'ya'yan itatuwa don ba da taimako ga manoman Taiwan wajen daidaita matsalar rarar amfanin gona da ba su iya sayarwa ba, da kuma sa kaimi ga yin musanya da hadin guiwa tsakanin bangarori biyu na zirin tekun Taiwan a fannin aikin gona. Jimlar 'ya'yan itatuwa da Taiwan ta fitar zuwa babban yankin kasar Sin ta kai ton 3,400 a shekarar bara, wato ke nan ya karu da kashi 35 cikin dari bisa na shekarar bariya.

Ban da wannan kuma, masana'antun aikin gona da yawa na Taiwan sun kafa rassansu a babban yankin kasar Sin. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa karshen shekarar bara, yawan ire-iren wadannan masana'antu da suka zuba jari a babban yankin kasar ya wuce 5,000. Haka zalika an sami kyakkyawan sakamako wajen kafa yankunan gwajin aikin gona a babban yankin kasar Sin cikin hadin guiwar bangarori biyu na zirin tekun Taiwan.

Malam He Ziyang, mataimakin shugaban ofishin ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin ya bayyana cewa, "a ganinmu, ya kamata, mu yi kokari wajen kafa tsare-tsaren hadin guiwar tsakanin bangarori biyu na zirin tekun Taiwan cikin dogon lokaci. Daga cikinsu, akwai tsarin kara amincewa da amfanin gona da za a sayar a kasuwannin bangarorin biyu da na 'yancin zuba jari, da tsarin daidaita matsalolin tattalin arziki da ciniki ta hanyar shawarwari, da tsarin rage yawan harajin kwastan da bangarorin nan biyu ke bugawa da makamantansu."

Mutane da abin ya shafa sun nuna cewa, ya kamata, bangarorin biyu na zirin tekun Taiwan su kara kokari wajen karfafa hadin guiwarsu a fannin cinikin amfanin gona da musanyan fasahohi da zuba wa aikin gona jari da sauransu don moriyar jama'arsu. (Halilu)