Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-04 21:50:56    
Kungiyar CBA ta shirya budadiyyar gasa a kauyuka

cri

Hadadiyyar kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin wato CBA ta shirya gasar CBO domin al'ummar kasar tun daga shekarar da ta gabata, masu shiga wannan gasa matasan 'yan wasa ne masu kishin wasan kwallon kwando, idan wani yana son irin wannan wasa, to, zai iya shiga. Saboda haka, da zarar budewar wannan gasa, sai masu kishin wasan kwallon kwando da ke birane daban daban na kasar Sin sun yi maraba da ita. Gasar wasan kwallon kwando da aka yi a Fengyang ta fi jawo hankulan mutane saboda karo na farko ne kungiyar CBA ta yi gasar CBO a kauyuka, kuma masu shiga gasar dukansu manoma ne.

Mataimakin shugaban kungiyar CBA Mr. Li Yuanwei ya bayyana cewa, mutanen kasar Sin suna maraba da wasan kwallon kwando sosai, yanzu kungiyar CBA ta shirya gasar CBO don ya da wasan kwallon kwando a wurare daban daban, musamman na a kauyuka, ta yadda wasan kwallon kwando zai zama wani kashi ne na zaman rayuwar mutane. Ya kuma jaddada cewa, bisa binciken da babbar hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta yi, an ce, manoman kasar sun fi son wasan kwallon kwando da na tebur. Sa'an nan kuma, ba a bukatar kudi da yawa wajen kafa filin wasan kwallon kwando, shi ya sa, yin gasar CBO a kauyuka ya ba da taimako wajen kyautata wa manoma zamantakewar al'adu.

Lokacin da yake ziyarar Fengyang, wakilinmu ya ji cewa, manoman wurin suna kishin wasan kwallon kwando sosai. Ran 17 ga watan Afril, mutane kimanin dubu 10 sun yi kallon bikin bude gasar CBO a wani fili na Fengyang, ban da wannan kuma, manoma fiye da dubu sun yi kallon wata gasar da aka yi a kauyen Xiaogang na gundumar Fengyang, bayan gasar, manoma sun yi wasan ja-in-ja da igiya da yin basukur sannu-sannu da dai sauransu da kansu. Sakataren kwamitin gundumar Fengyang na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Mr. Ma Zhanwen ya yi bayanin cewa,

'Ana yin wasannin motsa jiki tsakanin al'ummar Fengyang sosai, halin da ake ciki a wasu kauyuka yana da kyau, amma a wasu kuma ba ya da kyau, a sakamakon haka, muna son yin amfani da zarafin kafa sabbin kauyuka na gurguzu, da kuma gasar CBO, mu ya da irin wannan wasa mai farin jini, za mu kara zuba kudi kan yin kwaskwarima kan manyan ayyuka, ta yadda za a share fage ga wannan wasa.'

A garin Daying na gundumar Laian da ke kusa da Fengyang, manoma su kan yi wasan kwallon kwando kullun. Mr. Zhang Silin, mai kula da harkokin al'adu na garin Daying ya gabatar da cewa, manoma ba su bukatar kashe kudi da yawa wajen yin wasan kwallon kwando, 'yan kallo sun yi alla-allar shiga, wasan kwallaon kwando yana daya daga cikin wasannin motsa jiki da suka dace da kauyuka. Ya ce,

'muna da karfi a fannin wasan kwallon kwando, dukan kauyuka suna da kuniyoyinsu, mutane 40 zuwa 50 na ko wane kauye su kan yi wannan wasa kullun, su kan yi gasa, a sa'i daya kuma, masu kishin kallon gasar wasan kwallon kwando suna da yawa, idan akwai gasa, to, maza da mata, yara da tsoffi sun je kallon gasa, a maimakon yin ciniki, ban da wannan kuma, akwai mutanen da suka san ilmin wannan wasa sosai, idan alkalin wasa ya yi kuskure, to, za su bayyana ra'ayoyinsu. Saboda haka, wasan kwallon kwando ya aza harsahi mai kyau tsakanin mutanen garinmu.'

A lokacin da ake shirya gasar wasan kwallon kwando bisa gayyata a Fengyang, a sa'i daya kuma, an kusan kawo karshen hadadiyyar gasar wasan kwallon kwando ta kasar Sin, Mr. Li Yuanwei ya tsaya tsayin daka kan kallon gasar da aka yi a Fengyang. Mr. Li ya bayyana cewa, nan gaba, kungiyar CBA za ta kara shirya wa manoma irin wannan gasar wasan kwallon kwando, ta yadda za a shimfida wasan kwallon kwando lami lafiya a kauyuka.