Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-04 20:05:13    
Kasuwannin nuna wasannin fasaha suna ci sosai a Beijing a duk tsawon lokacin bikin ma'aikatan duniya

cri

Tare da zuwan dogon hutu na kwanaki 7 na bikin ma'aikatan duniya na ran daya ga watan Mayu, kasuwannin nuna wasannin fasaha su ma suna ci sosai, inda ake nuna wasannin fasaha iri daban daban masu ban sha'awa da kuma yin nune-nune masu ma'ana. Lallai wannan ya kara kawo annashuwa ga masu yawon shakatawa na gida da na waje da kuma jama'ar birnin Beijing dake bisa matsayin cibiyar al'adun kasar kasar Sin.
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ana nan ana nuna wasannin fasaha iri daban daban samar da 100 domin cimma bukatun mutane masu shan bambancin matsayin al'adu.
Harkar yin nishadi na ' Haduwa a Beijing' wanda akan yi sau daya a kowace shekaara ta rigaya ta zama tamkar ginshikin kasuwannin nuna wasannin fasaha na bikin ma'aikatan duniya na ran daya ga Mayu a nan Beijing tun daga shekarar 2000. Harkar nan, wani irin gaggarumin bikin fasaha ne na matakin kasa, wanda 'yan wasannin fasaha daga kasasheda jihohi fiye da l0 sukan halarta a kowace shekara.
A ran 28 ga watan jiya da dare, kungiyar wake-wake da raye-raye ta lardin Guizhou ta rera wakoki tare da yin raye-rayen kabilu irin na babban salo da ake kira ' Sigogi masu launi iri daban daban na Guizhou'. Yin haka kuma ya bude bikin harkar nishadi ta 6 ta ' Haduwa a Beijing'. Lardin Guizhou yana kudu maso yammacin kasar Sin, inda kananan kabilu fiye da l0 suke zaune a cunkushe a can.
Ban da wannan kuma, wasannin fasaha na wake-wake da raye-raye da ake kira ' Daren nishadi a Mexico' na kungiyar wake-wake da raye-raye da kasar Mexico, da wasannin Ballet da ake kira ' Carmen' da ' Budurwa daga garin Arles' da kuma ' Raymonda' na hadin gwiwar kasashen Sin da Fransa ,da " Taron rera wakoki masu karbuwa ko ina" na kungiyar makada ta kasar Rasha da kuma ' Taron rera wakoki na taruwar muryar kananan yara na kasashen Fransa da Sin, duk wadannan za su shere mutane a dakalin nuna wasannin fasaha na Beijing a duk tsawon lokacin bikin ma'aikata.
Mr. Zhang Yu,babban manajan kamfanin yin musanye-musanyen al'adu tsakanin kasa da kasa na kasar Sin ya furta, cewa: 'Yawan ayyukan wasannin fasaha da ake nunawa a wannan gami ya wuce 50 ; 'yan wasannin fasaha kuma ya zarce 1,500 ; kazalika, nune-nunen da ake yi sun kai guda 5 ; Kasashe 21 daga kwatinant 5 sun shiga harkar ' Haduwa a Beijing' da ake gudanar da ita a wannan gami.'
Ban da wasannin fasaha da ake nunawa a dakunan wasannin tiyata, ana kuma yin shagulgulan nishadi iri daban daban masu ban sha'awa a manyan lambunan shan iska da kuma filaye. Shugaban hukumar al'adu ta birnin Beijing Mr. Xiang Gongmin ya furta, cewa:'A duk dogon lokacin hutu na bikin ma'aikata na ran daya ga Mayu, ana daukar lambun shan iska na Chao Yang kan matsayin muhimmin wurin gudanar da harkar ' Haduwa a Beijing', wato a nan ana ci gaba da shirya harkar ' Makon wakoki masu karbuwa ko ina a duniya', inda kungiyoyin wasannin fasaha fiye da l0 daga kasashen Amurka, da Italiya da kuma Pahama da dai sauransu suke nuna wasannin fasaha.
Ban da wadannan kuma, babban dakin tiyata na fadar kabilu ta Beijing da kuma hadaddiyar kungiyar wallafa da fasaha ta kasar Sin sun hada kansu wajen shirya wata harkar ' Makon wake-wake da raye-raye' a lokacin hutu na bikin ma'aikata na wannan shekara. Mashahuran ' yan wasannin fasaha fiye da 60 daga bangaren al'adu za su nuna kyawawan wasannin fasaha. Wani jami'in hadaddiyar kungiyar wallafa da fasaha ta kasar Sin mai suna Qin Zhigang ya buga babban take ga wannan harkar ' Makon wake-wake da raye-raye' da ake gudanar da ita.( Sani Wang )