Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-03 18:49:02    
An yi yawon shakatawa a kasar Nijeriya

cri

Kasar Nijeriya tana kudu maso gabashin Afirka ta yamma, a kudunta shi ne tekun gulf na Guinea na Atlantic, duk fadin kasar ya kai muraba'in kilomita fiye da dubu 920, tsawon gabar tekunta ya kai kilomita dari 8, babban birninta shi ne Abuja, wanda ba ya dab da gabar teku.

Kasar Nijeriya ta fi samu yawan mutane a nahiyar Afirka, yawan mutanen da take da shi ya kai miliyan 133. Kasar Nijeriya tana da kabilu da yawansu ya zarce 250, amma manyan kabilu 3 daga cikinsu su ne kabilar Hausa-Fulani da ke arewacin kasar, da kabilar Yoruba da ke kudu maso yammacin kasar da kuma kabilar Igbo da ke gabashin kasar Nijeriya. Harsunan Hausa da Yoruba da Igbo sun zama manyan harsuna 3 a kasar, amma harshen Turanci ya zama harshen gwamnatin kasar Nijeriya.

Kasar Nijeriya tana da dogon tarihi da dadaddun al'adu, har kafin shekaru fiye da dubu 2 ya kasance da al'adu a kasar. Daga karni na 15 zuwa na 16, bi da bi ne 'yan mulkin mallaka na kasashen Portugal da Britaniya suka kai hari a kasar Nijeriya, a shekarar 1914, kasar ta zama wata kasa da kasar Britaniya ta yi mulkin mallaka a kai. A ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1960, kasar Nijeriya ta sami 'yancin kai, a ran 1 ga watan Oktoba na shekarar 1963, an kafa jamhuriyyar tarayyar kasar Nijeriya.

Nijeriya ta zama kasa ta farko da ta fi samar da man fetur a Afirka kuma ta zama ta goma a duk duniya, haka kuma tana kasancewa wata mambar kungiyar OPEC wato kungiyar kasashe masu fitar da man fetur. Yawan man fetur da aka gani a kasar Nijeriya ya kai ganga biliyan 35 da miliyan 200, a ko wace rana ta samar da man fetur da yawansu ya kai ganga miliyan 2 da dubu 500.

Nijeriya kasa ce mai arzikin gas da kwal da dai sauran ma'adinai. Yawan gas da take da shi ya kai cubic mita biliyan 5000, yawan kwal da take da shi ya kai ton biliyan 2 da miliyan 750, ta haka ta zama kasar kawai da take samar da kwal a yammacin Afirka.

Bayan shekarar 1971 da kasashen Sin da Afirka suka kulla dangantakar diplomasiyya, dangantakarsu tana samu bunkasuwa cikin sauri. Bangarorin biyu suna hadin kai a fannonin tattalin arziki da cinikayya da samar da gas da manyan ayyuka da aikin gona da kimiyya da fasaha masu zamani da dai sauransu, kuma sun riga sun sami nasarori da yawa. A shekarar 2005, yawan kudaden da bangarorin biyu suka samu wajen yin cinikayya ya kai dala biliyan 2 da miliyan 830, wanda ya faru da kashi 29.6 daga cikin dari. Kasar Nijeriya ta riga ta zama muhimmiyar abokiyar cinikayya da a nahiyar Afirka.(Danladi)