Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-03 18:29:52    
Hirar da muka da Malam Abudullahi Garba Baji

cri

Idan ba ku manta ba, da ma mun taba sanar da muku a kan wadanda suka sami nasarori a cikin gasar kacici kacici da muka shirya muku a bara dangane da tsibirin Taiwan na kasar Sin, kuma daga cikinsu, akwai wani mai sauraronmu da ya zo na farko, sabo da haka ya sami kyautar zuwa nan kasar Sin ziyara. To, masu sauraro, yanzu, muna farin ciki matuka da shaida muku cewa, wannan mai sauraronmu ya riga ya zo nan kasar Sin, kuma ga shi yanzu yana tare da ni a cikin dakin daukan murya namu.

Lubabatu:To, malam Abudullahi, maraba da zuwa kasar Sin, kuma maraba da zuwa gidan rediyon kasar Sin.

Baji:To, madalla, malama Lubabatu, na gode.

Lubabatu:Da farko, ko za ka gabatar da kanka zuwa ga masu sauraronmu, mene ne sunanka, kuma daga ina ne ka fito.

Baji:To, ni dai sunana Abudullahi Garba Baji, kuma na zo daga jihar Kano ta Nijeriya. Ina aiki a gidan rediyon Freedom wanda ke jihar Kano. Kuma ni shugaban kungiyar masu sauraron gidan rediyon kasar Sin ne wadda ake kira Mobaji Radio Club, kuma ni ne shugabanta, kuma tana da 'yan kungiya da yawa wadanda suke sauraron gidan rediyon kasar Sin.

Lubabatu:To, watakila masu sauraronmu suna sha'awar me ya kawo ka nan kasar Sin a halin yanzu, ko za ka gaya musu abin da ya kawo ka?

Baji:Gaskiya shi ne sakamakon wata gasar kacici kacici da aka yi, to, na samu nasara, na zo na daya, kuma sashen Hausa na rediyon kasar Sin suka ga ya dace su gayyace ni, domin in kawo ziyara a nan kasar Sin, tare da sauran abokaina wadanda suka zo daga fanni daban daban, mu kusan 11 ne, muka zo aka tara mu a nan akwai mutumin Poland, akwai mutumin Jamus, akwai mutumin kasar Vietnam, da dai sauransu,

Lubabatu:Me ka ji lokacin da aka sanar da kai cewa ka sami wannan kyautar zuwa nan kasar Sin ziyara?

Baji:Da farko da na samu labari, na sha mamaki, na yi mamaki kwarai da gaske, kuma ni na dauka ma ko ba gaskiya ba ne, amma daya baya dai, da na ga wasika ta inji mai kwakwalwa, Jamila ta aiko mana cewa, lalle, na ci wannan kyauta, kuma har na kawo ziyara a nan kasar Sin. Shi ya sa na ji dadi, na yi murna, na gaya iyayena, sun yi mana addu'a, na gaya matata, ta yi murna, sauran 'yan kungiya na tara su ga gaya musu, gaba daya mutane abokaina suna zuwa har gida suna cewa, muna yi maka murna, za ka tafi kasar Sin, ka je ka gani, abin da ka gani abin da ka ci, ka zo ka gaya mana.

Lubabatu:Watakila wannan shi ne ba karo na farko ba a gare ka wajen shiga irin wannan gasar kacici kacici da muka shirya?

Baji:Gaskiya, ni na kai shekaru 30 ina sauraron rediyon kasar Sin. Ina ta shiga ina ta shiga, na taba yin nasara ta biyu, na taba yin nasara ta uku, to, har ma lokacin da na zo na daya, har Allah ya sa na sake samun wannan nasara, gaskiya wannan kyauta ba karama ba ce, kuma a nan ma ina so in gaya miki, jiya shugaban rediyon kasar Sin ya ba ni wani babban kopi, ya ce, wannan kopi na girmamawa ne, sabo da kokarin da na yi, na zo na daya a wannan gasa ta kacici kacici, sabo da haka, na ji dadi.

Lubabatu:Tun farkon fari, me ya sa ka ce, to, bari in ma in shiga wannan gasar?

Baji:Abin da ya sa da ma, sauraron rediyo abin sha'awata ne, kin san kowa akwai abin da Bature kira 'hobby', kowa da hobby dinsa, wani kwallon kafa, wani sukuwa, ni hobby dina sauraron rediyo, tun ina sakandare. Wannan hobby shi ya sa har ma na kama aiki da rediyo. Sabo da haka, ko na ci, ko ban ci ba, in an aiko mana, to, zan rubuta.

Lubabatu:To, a nan abin da nake sha'awa shi ne shin yaushe ne ka fara sauraron shirye-shiryen sashen Hausa na rediyon kasar Sin?

Baji:Na fara sauraron shirye-shiryenku tun shekaru 30 baya, domin tun ina sakandare, wata rana, ina laluman tasha, sai kawai na ji sashenku, na tsaya na ce, wannan kamar Hausa ake yi, wato ba zato ba tsamani sai na ji an yi Hausa, na ce, bari in dai in tsaya in ji, shi ke nan, sai na ji Hausa ake yi, daga karshe sai aka ce, daga nan rediyon kasar Sin kuke sauraron wannan labari, sai na maki din tasha, shi ke nan, sai na ga lokacin da suke yi, sai na ce, shi ke nan, in Allah ya yarda, ko da yaushe, ni ma zan dinga sauraron wannan tasha.

Lubabatu:Wadanne shirye-shiryenmu ne ka fi so?

Baji:Shirye-shiryenku da na fi so, kin ga dai da farko, labari, sabo da yana kawo mana labari na nan kasar Sin, wanda ba a ko wane gidan rediyo za a ji ba. Sa'an nan kuma, akwai zabi sonka, daga labarai sai zabi sonka, bayan wannan kuma, sai tatsuniyoyi, sabo da suna ba mu dariya, muna jin dadinsa, sa'an nan kuma bangaren wasikun masu sauraro. Sabo da in an karanto wasikana, zan ji dadi, wani abokina zai yi mana waya ya ce, na ji an karanto, ina jin dadi.

Lubabatu:Da ma ka saurari shirye-shiryenmu ne a can nisa Nijeriya, amma ga shi yanzu ka zo har nan gidan rediyonmu, ko akwai da ya burge ka?

Baji:Abin da ya burge ni, da na zo sashen Hausa, yaro da babba, mace da namiji, kowa Hausa yake yi, wannan ba karamin abu ba ne, yanzu ga shi ke yarinya karama, kin fito daga university, amma abin sha'awa, ke kina kasar Sin, amma kin tafi university, kin karanta Hausa, wannan abu ya ba ni sha'awa.

Lubabatu:To, a matsayinka na shugaban wannan kulob na masu sauraro, ina so ka sanar da mu ra'ayoyin masu sauraronmu a kan shirye-shiyenmu.

Baji:Yawwa, su masu sauraro, suna son rediyon kasar Sin ta bude kofa wajen gabatar da shirye-shirye, ta bude Hausawa su shigo ciki, zai yi kyau domin idan ke Lubabatu kin yi naki labarai, Amina za ta zo ta yi nata, misali Baji zai zo ya yi nashi, idan kuke yi haka, kun ba wa masu sauraro dama su saurari murya kala kala, su saurari muryar Bahaushe, su saurari muryar Basine, wani idan bai fahimci maganar da basine ya yi ba, ga dan garinku ya yi, za ka fahimta. Sabo da haka, muke so ku bude. Lubabatu:To, daga karshe, me kake so ka fada wa masu sauraronmu?

Baji:Abin da nake so in ce wa masu sauraron sashen Hausa na rediyon kasar wadanda suke ko ina a Afirka, ina so in tabbatar musu da cewa, gidan rediyon kasar Sin ya riga ta ci gaba, kuma akwai alhirai tattare da ita wannan rediyo. A ci gaba da sauraron gidan rediyon kasar Sin, a ci gaba da rubuto musu wasiku, a ci gaba da rubuto musu shawarwari, a ci gaba da rubuto musu gyare-gyare, za ku gyara, na sani.

Lubabatu:A madadin dukan ma'aikatan sashen Hausa na rediyon kasar Sin, mun yi maka godiya kwarai da gaske, sabo da shawarwari da ra'ayoyi masu matukar kyau da ka ba mu a kan shirye-shiryenmu, ta yadda za mu kara kyautata su.

Baji:Na gode na gode.

Lubabatu:To, daga karshe, maraba da zuwa kasar Sin, kuma maraba da zuwa nan gidan rediyon kasar Sin.

Baji:Na gode malama Lubabatu, ke ma na yi miki fatan wata rana, za ki je Kano Nijeriya, domin bunkasa aikin gidan reidyon kasar Sin.

Lubabatu:To, Allah ya sa.

Baji:Allah ya sa, Allah ya taimaka.