Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-03 17:55:27    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (27/04-03/05)

cri

Ran 28 ga watan jiya, kwamitin wasannin motsa jiki na Olympics na duniya ya bayar da wata sanarwa, cewa an rigaya an tabbatar da dukkan ayyukan wasanni na taron wasannin motsa jiki na Olympics na Bejing a shekarar 2008, ciki har da manyan ayyukan wasanni 28 da kuma kananan ayyukan wasanni 302, wadanda kuma suka hada da ayyukan wasanni 165 na maza, da 127 na mata da kuma l0 na gauraya tsakanin mace da namiji.
Ban da wannan kuma ,sanarwar ta ce, sa kaimi ga mata wajen shiga wasannin motsa jiki na Olympics, ya zama daya daga cikin ayyukan kwamitin wasannin motsa jiki na Olympics na duniya yake yi a ' yan shekarun baya. Daidai saboda wannan dalili ne, kwamitin ya dan gyara ayyukan wasannin motsa jiki na Olympics na shekarar 2008, wato ke nan za a kara ayyukan wasa guda 2 na mata da kuma 'yan wasa mata da yawansu zai kai 130 a gun taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing idan an kwatanta su da na Aden ;
An soma aikin horo na tsaron kwanciyar hankali na taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing da gaske a ran 27 ga watan jiya. An yi irin wannan horo ne har zuwa watan Yuli na shekarar 2008.
A gun gasar fid da gwani ta karshe ta 48 ta cin kofin duniya ta wasan kwallon tebur da aka yi tsakanin kungiya-kungiya na mata jiya Lahadi a birnin Bremen na kasar Jamus, kungiyar kasar Sin ta lashe ta yankin Hongkong da ci 3 da 1, wato ta zama zakara har sau 7 a jere.


Ran 30 ga watan jiya, a birnin Sendai na kasar Japan, an kawo karshen gasa bisa matakin rukuni-rukuni ta gasar cin kofin duniya ta 2006 ta wasan Badaminton tsakanin kungiyoyin maza da na mata. Kungiyoyin waza da na mata na kasar Sin dukansu sun riga sun shiga jerin kungiyoyi 8 masu kasaita bisa matsayin lambawan a gun gasa tsakanin rukuni-rukuni. An bude wannan gasa ne a ran 27 ga watan jiya, kuma za a kammala gasar a ran 7 ga wannan wata.
An kawo gasar kusa da karshe ta hadaddiyar gasar wasan kwallon kafa ta Turai a ran 26 ga watan jiya. Kungiyar Barcelona ta Spain ta lashe ta AC Milan ta kasar Italiya da ci daya da sifiri; kuma kungiyar Arsenal ta England ta lashe ta Villarreal ta Spain da ci daya da sifiri, wato dukkansu za su shiga gasar karshe da za a yi a ran 17 ga wannan wata a kasar Fransa. ( Sani Wang )