Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-03 17:55:07    
Mahahuran mutane biyu na kasar Sin na zamanin da wato gimbiya Wenchen na daular Tang da sarkin kabilar Tufan Songzanganbu

cri

 

Birnin Lhasa , hedkwatar jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin, wani birni ne da ke da halayen musamman a kan fadaddun tsaunuka a kasar Sin, kuma tsarkakken wuri ne da ke da mashahurin suna wajen addinin Buddah. A birnin, ba ma kawai da akwai fadar Budala da ke da shahararren suna a duniya ba, hatta ma da akwai shahararrun wuraren tarihi da ke bayyana yadda jihar Tibet da babban yankin kasar Sin suke yin cudancya a tsakaninsu, wadanda suke kunshe da babban dutsen tunawa da yadda aka kulla kawance a tsakanin daular Tang da kabilar Tufan da babban dutsen tunawa da sarkin Kang Xi na daular Qing da dai sauransu. Daga cikinsu, da akwai wani shahararren labari dangane da yadda gimbiyar daular Tang Wanenchen ta shiga cikin jihar Tibet don aure da Songzanganbu, sarkin kabilar Tufan.

Daular Tang ta wanzu cikin karni na 7 zuwa karni na 10 tana daya daga cikin daulolin sarakunan da ke da tasiri sosai a tarihin kasar Sin, tana da karfi sosai, kuma ta yi tasiri sosai ga duk shiyyar gabashin Asiya. A farkon kafuwar daular Tang, wani sarki na kabilun da ke kudancin kasar Sin Songzanganbu ya cika burinsa na dinkuwar kasar da ke kan fadaddun tsaunuka na Tibet gu daya, ya kafa daular Tufan. A lokacin da Songzanganbu yake rike da mulkin daular, ya tsara tsare-tsaren mulki da yawa, ya yi kokarin raya tattalin arziki da kuma raya sha'anin al'adu cikin himma da kwazo, sa'anan kuma ya kago kalmomi da shigar da addinin Buddah da kuma fassara littattafan addinin Buddah. Ya yi kokarinsa ga raya ayyukan daular Tufan, sa'anan kuma ya nemi a kulla huldar da ke tskanin daularsa da daular Tang, cikin himma da kwazo ne ya shigar da fasahohin ci gaba na daular Tang tare da al'adunta da siyasarta, sau biyu yana aikawa da manzaninsa na musamman don neman aure daga daular Tang.

A shekarar 640, sarkin daular Tang Li Shimin ya yarda da rokonsa na neman aure, wato ya yarda da ba da auren gimbiya Wencheng gare shi. A kan hanyar zuwa wurin kabilar Tufan, gimbiya Wencheng ta bar labarai masu ban sha'awa sosai da sosai. Wani mashahurin labari daga cikinsu shi ne, asalin samun tafkin Qinghai. A cikin tatsuniyar da 'yan kabilar Tibet suke yadawa, an bayyana cewa, sarkin Tang ya bai wa gimbiyar wata sadaka, wato wani madubi don kawar da begenta ga inda aka haife ta, a duk wurin da ta sa kafa, to za ta iya ganin abubuwan da ke faruwa a birnin Chang'an na daular Tang, har ma ya kera rana da wata ta hanyar yin amfani a zinariya don raka ta. Lokacin da gimbiya Wencheng ta sauka iyakar da ke tsakanin daular Tang da daular Tufan, ta ga abubuwan da ke faruwa a garinta, sa'anan kuma ta bar madubin nan a wurin don mai da hankali ga makomarta ta nan gaba. Kai, nan da nan madubin ya zama taskin Qinghai mai kyaun gani sosai, rana da wata da aika kera da zinariya sun zama duwatsu masu sifofin rana da wata.

Bayan da Songzanganbu ya sami labarin zuwan gimbiya Wencheng a Tufan, ya yi farin ciki sosai, shi kansa ya fita waje ya yi maraba da gimbiya Wencheng, kuma bisa matsayin mijin gimbiyar daular Tang ne ya gana da manzon musamman na daular Tang, lokacin da gimbiyar ta sauka birnin Lhasa, jama'ar wurin sun yi matukar maraba da ita.

Shigar da gimbiya Wencheng a Tufan ya sa kaimi ga raya tattalin arzikin wurin, kuma gimbiyar ta yadadda al'adun addinin Buddah da kuma kara dankon huldar da ke tsakanin daular Tang da daular Tufan. Ta tafi Tufan tare da abubuwa da yawa daga daular Tang, kamar su irin hatsi da irin ganyayen lambu da dabarun nomansu da sauran fasahohin yin abubuwa, kamar su na yin giya da daka garin hatsi da sauransu, hr ma ta tafi da dawaki da kekuna da rakumai da littattafan addinin Buddah da sauransu, har ma gimbiyar ita kanta ta dasa wata bishiya, yar wa yau dai bishiyar tana kamawa.

Gimbiya Wencheng ta fid da tsoron wahalar tafiya zuwa wuri mai nisa, kuma ta auri wani sarkin kabilar Tufan, wannan ya sa kaimi ga yin ma'amalar tattalin arziki da al'adu a tsakanin daular Tang da daular Tufan, kuma ya kara dankon huldar da ke tsakanin jama'ar kabilun biyu, shi ya sa ta sami girmamawa da kauna daga wajen wadanda suke bayanta. A shekarar 710, dan Songzanganbu shi ma ya yi koyi da mahaifinsa, ya auri gimbiya mai suna Jincheng, wannan ya bayyna burin jama'ar kabilar Han da kabilar Tibet wajen kulla zumunci daga zuri'a zuwa zuri'a (Halima)