Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-02 21:10:51    
Shahararren tafki mai suna Xihu na birnin Hangzhou na Sin a watan Maris

cri

Tafki mai suna Xihu wani shahararren wurin yawon shakatawa ne a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang da ke a gabashin kasar Sin. Dukkan fadin wannan wuri ya kai kimanin muraba'in kilomita 50, daga cikinsu, haddin ruwa ya kai muraba'in kilomita 5.6. Idan an sami damar sa kafa a bakin tafkin Xihu a watan Maris, to, za a more ido da bishiyoyi masu furanni iri daban daban.

Malam Gao Quan, dan yawon shakatawa wanda ya taba zuwa tafkin Xihu har sau uku ya bayyana cewa, "na kan zo tafkin Xihu ne a watan Maris. Dalilin da ya haka shi ne domin tafkin Xihu ya kan zama wuri ne mai matukar kayatarwa a wannan lokaci. Ba ma kawai ganyayen bishiyoyi sun yi kore shar ba, har ma iskar da ake shaka ta yi kyau kwarai. Musammam ma ina sha'awar kyawawan gadoji 6 masu sigogi iri daban daban da aka gina a kan tafkin Xihu."

A gabar kudu maso gabashin tafkin Xihu, akwai wani wuri da ake kiwon tsuntsaye. Da ma a nan lambun shan iska ne na sarkin kasar Sin. Tsuntsaye su kan yi kuka sosai a kan bishiyoyi. Idan masu yawon shakatawa sun ji kukan tsuntsaye, to, za su ji dadi ainun.

Shahararrun mutane da yawa na gida da waje suna sha'awar wannan ni'imataccen wurin yawon shakatawa ainun. Alal misali, marigayi shugaba Mao Zedong na kasar Sin ya taba zuwa birnin Hangzhou har sau 40 a duk lokacin rayuwarsa, lokaci mafi tsawo da ya zauna a can ya kai watanni 7. Haka kuma tsohon shugaban kasar Amurka Richard Milhous Nixon shi ma ya yi yawon shakatawa a tafkin Xihu har sau biyu, ya yaba cewa, birnin Beijing hedkwatar kasar Sin ne, birnin Hangzhou kuwa "cibiyar" kasar nan ne.

Ba ma kawai tafkin Xihu mai matukar kayatarwa yana jawo hankulan masu yawon shakatawa na wurare daban daban na kasar Sin ba, har ma aminanmu da yawa na kasashen waje suna sha'awar zuwa. Malam John Lee wanda ya fito daga kasar Amurka ya shafe shekaru 4 ko fiye yana zama a birnin Hangzhou. Ya yi matukar farin ciki da bayyana cewa, "lokacin bazara lokaci ne da duk abubuwa masu rai ke farfadowa. Watan Maris kuma lokaci ne da tafkin Xihu ya fi kyaun gani a ko wace shekara. A nan ga bishiyoyi masu launin kore shar, ga kuma furanni masu launuka iri daban daban. Lalle, tafkin Xihu ya cancanci wuri da za a yi yawon shakatawa. Ban da wadannan kuma a nan akwai tsoffafin shahararrun wurare masu ni'ima da yawa, ina sha'awarsu ainun. "

Yanzu, masu yawon shakatawa suna shiga cikin lambun shan iska na tafkin Xihu ba tare da biyan ko anini daya ba. Da Malam Wang Guoping, sakataren reshen Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a birnin Hangzhou ya tabo magana a kan tafkin Xihu, sai ya ce, "kullum muna ganin cewa, ba ma kawai tafkin Xihu tafki na mazaunan birnin Hangzhou da na lardin Zhejiang ne ba, har ma na duk jama'ar kasar Si da ta duk duniya ne. Yanzu, masu yawon shakatawa suna shiga cikin manyan lambunan shan iska guda 7 da ke gabobin tafkin Xihu ba tare da biyan ko anini daya ba, mun hakkake cewa, tabas ne, masu yawon shakatawa za su ji matukar farin ciki da ganin sabon hali mai kyau da ake ciki a tafkin Xihu da birnin Hangzhou musamman su yi yawon shakatawa a wadannan wurare biyu a watan Maris na ko wace shekara."

Wasu mutane sun mayar da tafkin Xihu na birnin Hangzhou da tafkin Geneve na kasar Switzerland bisa matsayin lu'ulu'ai masu kayatarwa guda biyu a duniya. A cikin littafinsa na yawon shakatawa, dalilin da ya sa marigayi Marco Polo, shahararren matafiya na kasar Italiya ya dauki birnin Hangzhou bisa matsayinsa na birni mafi kayatarwa da daraja a duniya, shi ne duk domin tafkin Xihu. (Halilu)