Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-05-02 20:12:02    
Yawon shakatawa da ake yi ta hanyar tuka motocinsu da kansu ya zama wani sabon tashe a ranaikun hutu na kasar Sin

cri

Daga ran 1 zuwa ran 7 ga watan Mayu na kowace shekara, ranaikun hutu ne na duk kasar Sin baki daya, mutane da yawa sukan yi yawon shakatawa cikin wadannan ranaikun hutu guda 7. A da, idan Sinawa sun yi yawon shakatawa zuwa sauran wurare, yawancinsu sukan zabi kayayyakin tafiye-tafiye na jama'a ciki har da jiragen kasa da na sama. Amma bisa karuwar yawan motocin da mutanen kasar Sin suka saya da kansu, a lokicin hutu na "Ran 1 ga Mayu" na wannan shekara, Sinawa sai kara yawa suke suna ta yin yawon shakatawa ta hanyar tuka motoci da kansu.

Mr. Guo Jian, edita mai shirya labarun wasannin motsa jiki na wata jaridar birnin Beijing, yana son wasannin motsa jiki kuma yana sha'awar yawon shakatawa. A karshen shekarar da ta wuce, Mr. Guo ya sayi wata karamar mota. A ran 29 ga watan Afrilu da yamma, ya yi farin ciki ya dudduba motarsa domin shirin yawon shakatawa ta karo na farko ta hanyar tuka motarsa da kansa. Ya ce, "A da idan ana son yin yawon shakatawa zuwa sauran wurare, ba yadda za a yi sai ta hanyar jiragen kasa ko jiragen sama, amma a ranaikun hutu na "ran 1 ga Mayu" na wannan shekara, a shirye nake zan tuka motata zuwa birnin Qingdao domin yawon shakatawa tare da aminiyata, ina tsammani cewa wannan wani sabon aiki ne sosai gare ni."

Mr. Tang Min, wani ma'aikaci ne na kulob din yawon shakatawa na masu tuka motocinsu da kansu na babbar hukumar yawon shakatawa ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Da kyar za a lisafta yawan mutanen da za su yi yawon shakatawa a lokacin hutu na "Ran 1 ga Mayu" ta hanyar tuka motoci da kansu, amma ana iya tabbatar da cewa, wannan adadi zai fi na shekarun baya yawa sosai. Ina tsammani cewa, da akwai abubuwa guda 2 wadanda suke iya bayyana babban tashen da za a yi wajen yawon shakatawa ta hanyar tuka motoci na masu zaman kansu. Na farko shi ne, yawan kungiyoyin da hukumomin yawon shakatawa suka kafa a lokacin hutu na "Ran 1 ga Mayu" na wannan shekara, dukkansu sun ragu a bayyane, amma wannan bai bayyana cewa halin da ake ciki a kasuwannin kasar Sin wajen yawon shakatawa bai yi kyau ba, amma dalilin da ya sa haka shi ne sabo da mutane da yawa sun zabi hanyar tuka motoci da kansu domin yawon shakatawa. Na 2 kuma shi ne sabo da kwanan baya hukumar yawon shakatawa tamu ta kaddamar da shirin yawon shakatawa na kwanaki 4 a lokacin hutu na "Ran 1 ga Mayu" daga birnin Beijing zuwa birnin Shenyang ta hanyar tuka motoci na masu zaman kansu, cikin kwanaki 3 na bayan da aka kaddamar da wannan shiri kawai kuma da akwai mutane kusan 100 wadanda suka yi rajista ko kuma yin tambayoyi kan wannan batu."

Bari mu ji maganar da wata mai sha'awar yawon shakatawa ta hanyar tuka motarta da kanta ta fada, madam Wang da ke zaune a nan birnin Beijing tana shirin yawon shakatawa zuwa birnin Shenyang da ke arewa maso gabashin kasar Sin ta hanya tuka motarta da kanta, kafin tashinta ta gaya wa wakilinmu cewa, "Ina sha'awar yawon shakatawa ta hanyar tuka motata da kaina sosai, dalilin da ya sa na yi haka shi ne sabo da a da sayen motoci na masu zama kansu ya zama mafarki ne ga Sinawa, amma yin yawon shakatawa zuwa wurare masu ni'ima ta hanyar tuka motoci na kansu ya zama abu mafi kyau daga cikin wannan mafarki. Sabo da haka ina tsammani cewa Sinawa da yawa da suka yi irin wannan yawon shakatawa na karo na farko ne domin tabbatar da mafarkinsu." (Umaru)